Isra'ila na da 'yanci ta yi maganin Hamas - Ministan Tsaron Birtaniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Cikin hotuna: 'Yan Isra'ila na makokin rasuwar 'yan'uwansu ana ci gaba da harba rokoki

    Israeli women

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mata suna makokin rasuwar Daniella Dana Petrenko daga yankin Haifa wadda aka kashe lokacin da 'yan bindigan Hamas suka auka wa masu halartar bikin Supernova kuma suka bude wuta a kan masu shagali. Ta halarci bikin ne tare da saurayinta
    Israeli soldier

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani sojan Isra'ila yana taka kayayyaki a kusa da wani gida cikin kauyen Kibbutz Be'eri na kudancin Isra'ila, inda Hamas ta yi wa mutane fiye da 100 kisan gilla, cikinsu har da kananan yara
    Rockets firing from Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ana ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ila daga Gaza; yayin da ita ma Isra'ila tana ta kai manyan hare-hare a cikin yankin
  2. Ana zanga-zangar nuna goyon bayan Gaza a Jordan

    Yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ke ganawa da Sarki Abdallah na Jordan da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas a birnin Amman, ana gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al'ummar Gaza bayan sallar Juma'a.

    Masu zanga-zangar suna yaɗa bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda sojojin Jordan ke amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa zanga-zangar da suke yi, kusa da kan iyakar Jordan da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ke karkashin mamaya.

    An rufe mashigar Allenby ko mashigar Sarki Hussein wadda Isra'ila ke iko da ita a bangaren Falasɗinu

    Ba a iya jin ta bakin jami'an tsaron Jordan ba.

    Yawancin 'yan kasar Jordan, Falasdinawa 'yan gudun hijira ne ko kuma suna da tushe da al'ummar Falasɗinawa ciki har da Sarauniya Rania.

  3. Tinubu ya yi sabbin nade-nade a bangaren kula da masana'antu

    ...

    Asalin hoton, TINUBU FACEBOOK

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade ga hukumomi da cibiyoyin da ke bangaren harkokin zuba jari da kasuwanci da masana'antu na kasar.

    Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya kan yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar ta ce nade-naden sun fara aiki ne nan take.

    Sanarwar ta ce Tinubu ya yi nade-naden ne bisa kudurinsa na dora kokarin farfado da tattalin arzikin Najeriya a kan tushen bunkasa kasuwanci ta hanyar saukaka harkokin gudanar da kanana da matsakaita har ma da manyan masana'antu a kasar.

    Ga sunayen shugabannin hukumomin da Tinubu ya nade da kuma wuraren da za su yi aiki:

    Hussaini Ishaq Magaji (SAN) — Hukumar yi wa kamfanonin rijista (CAC)

    Afiz Ogun Oluwatoyin — Asusun ba da horon masana'antu (ITF)

    Kamar Bakrin — Majalisar bunkasa harkokin samar da sukari ta kasa

    Olufemi Ogunyemi — Hukumar bunkasa harkokin fitar da kayayyaki zuwa ketare ta Najeriya (NEPZA) —

    Nonye Ayeni — Majalisar bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta Najeriya (NEPC)

    Aisha Rimi — Hukumar bunkasa harkokin zuba jari ta Najeriya

    Bamanga Usman Jada — Hukumar kula da yankunan harkokin man fetur da gas maras haraji (OGFZA)

    Charles Odi — Hukumar bunkasa harkokin kanana da matsakaitan masana'antu ta Najeriya (SMEDAN)

    Ifeanyi Chukwunonso Okeke — Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya (SON)

    Rabiu Olowo — Majalisar daidaita rahotannin harkokin kudi ta Najeriya (FRCN)

    Anthony Atuche, CFA — Hukumar kula da kasuwannin zuba jari ta Najeriya (NCE)

    Veronica Safiya Ndanusa — Cibiyar shirya baje-koli ta duniya da ke Lagos (LITFCMB)

    Lucia Shittu — Hukumar kula da dandalin Tafawa Balewa

    Oluwemimo Joseph Osanipin — Majalisar bunkasawa da tsara fasalin motoci ta kasa (NADDC).

    • Ministocin a Najeriya: Su wane ne ƙusoshin gwamnatin Tinubu?
    • Mun zaɓo ministoci ne bisa cancanta - Tinubu
  4. Sojoji sun ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su a Kebbi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar Alhamis, sun ce sun yi nasarar ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su tare da karɓe babura daga hannun ƴan bindiga a yayin wani aikin ceto a jihar Kebbi.

    Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Kyaftin Yahaya Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

    Ya ce an samu nasarar hakan ne a lokacin da sojojin da aka jibge a Malekachi suka gudanar da aikin ceto sakamakon sahihan bayanai da ke nuna cewa ‘yan bindaga sun yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a kauyen Kanya da ke karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi inda suke ƙoƙarin tsallakawa da su zuwa Nijar.

    Sanarwar ya ce “Sojoji sun yi kwanton bauna a kan hanyoyin da ake zargin ‘yan ta’addan ne za su yi amfani da su a kauyen Karenbana..

    Bayan haka, karfin wuta na sojojin ya tilastawa 'yan ta'addan suka tsere da raunukan harbin bindiga tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su wanda ya kai ga ceton su.

    “Wadanda aka ceto sun hada da mata 6 da maza 11 da suka hada da ‘yan sanda da aka yi garkuwa da su a Danko-Wasagu."

    "An mika waɗanda aka ceto ga jami’an ‘yan sanda na yankin Bena domin sada su da iyalansu. Haka kuma, sojojin sun kwato Babura 5 da suka kone,” in ji sanarwar.

    Ya kuma ƙara da cewa kwamandan rundunar hadin gwiwa, Manjo Janar Godwin Mutkut, ya yabawa matakin da sojojin suka mayar a kan lokaci, inda ya buƙace su da su ƙara kaimi tare da ci gaba da hana ‘yan ta’addan ‘yancin kai dauki.

    • Mun raba Najeriya da ƴan ta'adda fiye da 800 a wata uku - Sojoji
    • Al'ummomi a Sokoto na fargaba kan ɗauki ɗai-ɗai da ƴan bindiga ke musu
  5. A cikin hotuna: Mutanen Gaza suna tserewa daga gidajensu

    Muna ganin hotuna suna fitowa na mutane a birnin Gaza suna daukan kayayyaki suna ficewa daga gidajensu, bayan gargadin da Isra'ila ta bayar na cewa su tashi, su koma kudu.

    Daga cikin wadanda ke kokarin kai wa ga tudun-mun-tsira kananan yara ne. Kusan rabin al'ummar Gaza, yara ne 'yan kasa da shekara 18.

    Gazans

    Asalin hoton, Reuters

    Gazans

    Asalin hoton, Getty Images

    Gazans

    Asalin hoton, Reuters

  6. Ana tsammanin yin zanga-zanga a fadin kasashen Larabawa bayan Sallar Juma'a

    Palestinian solidarity protest in Baghdad

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Zanga-zangar nuna goyon bayan al'ummar Falasdinawa a Gaza, cikin birnin Bagadaza

    Dubban mutane ne suka taru a birnin Bagadaza don nuna goyon baya ga Falasdinawan Gaza.

    "Wannan gangamin na da nufin yin alla-wadai ne da abin da ke faruwa a yankin Falasdin da ke karkashin mamaya, irin zubar da jinin da ake yi da keta hakkokin dan'adam," Abu Kayan, daya daga cikin masu shirya zanga-zangar ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Wannan daya ce kawai a cikin zanga-zanga da dama da aka shirya gudanarwa yau a fadin Gabas ta Tsakiya, bayan shugabannin Hamas da na Hezbollah sun yi kira ga jama'a su gudanar da zanga-zanga bayan Sallar Juma'a.

    Tsohon jagoran Hamas, Khaled Meshaal a jiya ya bukaci mutane su “fita zuwa dandali da filayen Allah a fadin kasashen Larabawa da na Musulmi” don gudanar da gangami.

    Ana tsammanin irin wadannan taruka da yawa za su gudana a Lebanon da Tunisia da kuma Jordan a yau.

    Dakarun tsaro sun kuma shirya don tunkarar yamutsi a Masallacin al-Aqsa da ke cikin yankin mamaya a Gabashin Kudus.

    • Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa
    • Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
  7. An harba rokoki kan birnin Ashkelon na kudancin Isra'ila

    Ashkelon

    A halin yanzu ana harba makaman roka daga Gaza zuwa kudancin Isra'ila, inda aka nufi Ashkelon.

    Tawagar BBC da take wajen ta ga tashin bam ɗaya .

    Bangaren sojan Hamas, na al-Qassam Brigades, na ikirarin harba rokoki 150.

    • Sahihan bidiyon harin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila
    • Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
  8. Blinken ya gana da shugaban Falasɗinawa a Jordan

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gana da shugaban Falasɗinu Mahmoud Abbas a kasar Jordan.

    Abbas, wanda ke zama a gaɓar yamma da Kogin Jordan, abokin hamayyar siyasa ne ga Hamas da ke mulkin Zirin Gaza.

    Blinken yana kuma ganawa da Sarkin Jordan Abdullah a Amman bayan ya isa can a safiyar yau, Juma'a.

    A ranar Laraban da ta gabata ne dai Bliken ya je Isra'ila don tattaunawa da firaministan ƙasar, Benjamin Netanyhu inda aka nuna masa hotunan matattun yaran da Hamas ta kashe.

    • Blinken zai gana da shugaban Falasdinawa ranar Juma'a
  9. Sabbin bayanai game da rikicin Isra'ila da Gaza

    Ga bayanan sabbin abubuwan da suka faru a rikicin Gaza

    • Umurnin Isra'ila - Isra'ila ta umarci Falasɗinawa miliyan 1.1 a arewacin Gaza su fice zuwa yankin kudu a cikin sa'a 24 mai zuwa don tsira da rayukansu kafin farmakin da ake sa ran kai wa.
    • Amma wani jami'in Hamas ya bayyana umarnin da Isra'ila ta bayar a matsayin "farfagandar karya", ya kuma bukaci mazaunan yankin su yi watsi da ita.
    • Majalisar Dinkin Duniya ta ce umarnin ba abu ne mai yiwuwa ba, inda ta buƙaci Isra’ila ta janye wannan abu da take nufi.
    • Karin 'yan siyasa sun kai ziyara Isra'ila - shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin na ziyara a Isra'ila a yau. Tuni dai, sakataren wajen Amurka Antony Blinken shi ma ya je yankin don tattaunawa da shugabannin.
    • Nan gaba a yau - za mu sa ido ga duk wata zanga-zanga bayan Hamas da Hizbullah sun yi kiran a gudanar da zanga-zangar kin jinin Isra'ila yau "a duk fadin kasashen Larabawa da na Musulmi". A halin da ake ciki kuma, ƙarin jiragen saman fasinja suna ci gaba da barin Isra'ila - inda Amurka ta aika jirgin farko da zai kwashe mutanenta.
  10. Hamas ta ce hare-hare a kan Gaza sun kashe 'yan Isra'ila 13 da take garkuwa da su

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Hamas ta yi ikirarin cewa an kashe ƴan Isra'ila 13 da wasu 'yan kasashen waje da take garkuwa da su a Zirin Gaza a hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai cikin sa'a 24,

    Sanarwar da rundunar Izzedine al-Qassam ta fitar na cewa "an kashe fursunonin 13 ciki har da 'yan kasashen waje a wurare guda biyar da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai wa hari."

    Hamas ta kama tare da yin garkuwa da mutane kusan 150 a lokacin da ta kai harin ba-zata a ranar 7 ga Oktoba.

    Ta yi barazanar kashe mutanen da take garkuwa da su, matukar Isra'ila ta jefa bama-bamai a gidajen fararen hula ba tare da gargadi ba.

    Kamar yadda rahotanni suka shigo, Sakataren Tsaron Burtaniya Grant Shapps ya shaida wa ITV cewa zai so a yi taka-tsantsan kan wannan iƙirarin amma akwai "tsananin damuwa".

    • Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
    • Dalilai huɗu da suka sa Hamas ta kai wa Isra'ila hari
  11. Nadin sabon shugaban hukumar EFCC ya haifar da ce-ce-ku-ce

    Nadin sabon shugaban hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeirya ya haifar da ce-ce-ku-ce inda wasu ke cewa bai cika sharuddan tanadin dokar hukumar ba.

    A ranar Alhamis shugaban kasar Bola Tinubu ya sanar da naɗin Ola Olukoyede a matsayin sabon shugaban EFCC, amma sai majalisar dattawa ta tabbatar da shi.

    Yayin da wasu ke cewa bai cika sharudda hukumar ba na zama shugaban EFCC, fadar shugaban ƙasar kuma na cewa babu inda aka saɓa doka kafin sanar da naɗinsa kasancewarsa toshon shugaban ma’ikata na hukumar EFCC kuma sakataren hukumar tare da aiki a hukumar tabbatar da doka.

    Dangane da tanadin dokar, BBC ta tattaunawa da Dr Zakiyu Muhammad, masanin shari’a a Najeriya

    • Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar EFCC
    • Ya kamata a binciki shugaban EFCC — Matawalle
    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron tattaunawar
  12. Kimanin Falasɗinawa sama da 400,000 sun tserewa gidajensu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kimanin Falasɗinawa sama da dubu dari hudu ne suka tserewa gidajensu, sakamakon hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa Zirin Gaza.

    Bakin hayaki ne ya turnuke sararin samaniyar birnin da aka shafe kwanaki biyu cir, cikin duhu sakamakon yanke musu wuta, da ruwa, da abinci, da man fetur da Isra'ilar ta yi.

    Jami'an kiwon lafiya na Falasɗinawa sun ce akalla mutane arba'in da biyar ne suka mutu a lokacin da wani hari ta sama ya rutsa da wani rukunin gidaje a gundumar Jabaliya.

    Ministan makamashi na Isra'ila ya ce ba za a bai wa Gaza wuta ba, har sai mayakan Hamas sun saki 'yan Isra'ilar da suka kama.

    Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Amnesty International sun bayyana matakin na Isra'ila a matsayin laifin yaki.

    • Fargaba na ƙaruwa yayin da Isra'ila ke jibge dakarunta a kan iyakar Gaza
    • Gaza 'nan gaba kaɗan za ta kasance babu man fetur, magunguna da abinci'
  13. Burkina Faso za ta ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya da Rasha

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Burkina Faso da Rasha za su rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta gina tashar makamashin nukiliya a yammacin Afirka, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AIB ya bayyana.

    Yarjejeniyar za ta kasance karshen tattaunawar da shugaban mulkin sojan Burkina Faso, Kaftin Ibrahim Traore ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin a watan Yuli, yayin taron Rasha da Afirka a Moscow.

    "Za a rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Rosatom, hukumar makamashin nukiliya ta tarayya ta Rasha, da ma'aikatar makamashi ta Burkina Faso, a makon makamashi na Rasha na 2023," in ji AIB.

    Al'ummar Burkina Faso kimanin kashi 20 cikin 100 ne ke samun wutar lantarki daya daga cikin mafi ƙarancin farashi a duniya, a cewar hukumar makamashin nukiliya ta duniya IEA.

    Bayan da aka samu saɓani da galibin kawayenta na yammacin Turai, ciki har da Faransa da ta yi mulkin mallaka, Burkina Faso ta koma kasar Rasha domin samun tallafin tattalin arziki da na soji.

    • Abin da ya sa Rasha ke murna da juyin mulkin Burkina Faso
    • Me sojojin mulkin Nijar ke nema daga ƙawayensu?
  14. An dakatar da yarjejeniyar dala biliyan shida tsakanin Amurka da Iran

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labaran Amurka sun rawaito cewa an dakatar da wata yarjejeniyar dala biliyan shida tsakanin Amurka da Iran, yayin da ake ci gaba da bincike kan irin goyon bayan da kasar ke ba wa kungiyar Hamas.

    Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta ce cin amana ne gwamnatin Amurka ta yin watsi da yarjejeniyar da aka kulla a Qatar, wadda ta kai ga yin musayar fursononi a baya-bayan nan.

    An bankaɗo labarin ne daga wani taron masu ruwa da tsaki na baitul malin Amurka.

    Gwamnatin Biden ba ta tabbatar ko musanta rahotannin ba.

    Gwamnatin Amurka tana kokarin hana Iran da ƙungiyoyin yan gwagwarmayar kasashen Larabawa shiga rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

    • Yadda dangantaka tsakanin Amurka da Saudiyya ta rika sauyawa
    • Burtaniya da Amurka sun ce Iran za ta yaba wa aya zaki kan harin jirgin ruwan Isra'ila
  15. Isra'ila ta umarci Falasɗiwa sama da miliyan 1 su fice daga arewacin Zirin Gaza

    ...

    Isra'ila ta shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa jazamun ne dukkanin al'ummar Falasɗinawa sama da miliyan daya da dubu dari da ke rayuwa a arewacin Zirin Gaza, su fice daga yankin cikin awanni 24 masu zuwa.

    Mai magana da yawun Majalisar Stephane Dujarric, ya ce kungiyar ta yi kakkausan suka ga wanan mataki, da ka iya bude kofar bala'in da ba a san iyakarsa ba.

    Wakilin Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan, ya soki kalaman na MDD, yana cewa kamata ya yi ta maida hankali wajen ceto mutanen da Hamas ke garkuwa da su maimakon yi wa Isra'ila wa'azi.

    Wani jami'in Hamas ya bayyana wannan umarni na Isra'ila a matsayin 'farfaganda', yana kira ga Falasɗinawa su yi watsi da kiran.

    Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya a Gaza sun ce jami'an haɗin gwiwa na sojojin Isra'ila ne suka kai musu saƙon gargadin cikin daren da ya gabata, kuma ya shafi kowa da kowa ne.

    Ana kyautata zaton Isra'ilar na shirin ƙaddamar da mamaya ta kasa a Zirin na Gaza.

    • Rayuwa a Gaza: 'Babu wurin fakewa a ruwan makamai masu linzami'
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
  16. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkanmu da safiyar Juma'a.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Aisha Babangida.

    Ku kasance da mu tsawon yinin yau, domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban har ma da Najeriya.