Isra'ila na da 'yanci ta yi maganin Hamas - Ministan Tsaron Birtaniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtar Adamu Bawa and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawo wa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Sojojin Isra'ila sun fara kutsawa wasu unguwannin Gaza

    e

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun ce sun fara kai samame wasu unguwannin Zirin Gaza yayin da dakarunsu ke shirin kai gagarumin farmaki ta ƙasa.

    Mai magana da yawun sojin Isra'ilar ya ce manufar yin hakan shi ne domin kawar da 'ƴan ta'adda' da kuma kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Sanarwar na zuwa daidai lokacin da Falasɗinawa ke barin arewacin Gaza a ƙoƙarinsu na cika umarnin da Isra'ila ta basu na barin yankin.

    Daruruwan mashina da manyan motoci ɗauke da katifu da sauran kayan amfanin yau-da-kullum ke ficewa daga Arewacin Gazar, yayin da wasu da dama suke tafiya a ƙasa.

  3. Halin da Falasɗinawa ke ciki a asibiti ya girgiza ma'aikatan BBC

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Ma'aikatan BBC sun kaɗu, har sai da suka dakatar da aikin da suke yi na ɗaukan rahoto saboda kaɗuwa da abin da suka gani a wani asibiti na Falasɗinawa.

    Sun ga wasu daga cikin dangi da maƙwaftansu cikin mawuyacin hali.

  4. 'Ina alfahari da wannan rana kamar kowane ango'

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Ɗaya daga cikin angwayen da suka sha ƙamshi a auren zawarawa da ƴan mata na gwamnatin jihar Kano ya bayyana wa BBC yadda ya ji.

    Gwamnatin ta ce kimanin zawarawa da 'yan mata 1,800 ne ta ɗauki nauyin aurar da su a ranar juma'a.

  5. Tinubu ya cire Abuja daga tsarin Asusun Ajiya na Bai-ɗaya

    s

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya cire birnin tarayyar ƙasar Abuja daga tsarin Asusun Ajiya na Bai-ɗaya (TSA)

    An ɗauki matakin ne da nufin bayar da dama wajen bunƙasa ci gaban birnin ƙarƙashin jagorancin ministan Abuja Nyesom Wike, domin ba shi ƙarin iko kan kuɗaɗen da birnin ke tarawa.

    Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudanar ranar Juma'a a Abuja.

    Asusun Ajiya na Bai-ɗaya (TSA) Tsari ne da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi a 2015, da nufin sanya duka kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu a cikinsa, domin tabbatar da gaskiya da bin diddigin kuɗaɗen gwamnati.

  6. Isra'ila ta kashe masu zanga-zanga a Gaɓar Yamma da kogin Jordan

    w

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Lafiya na Yankin Falasdinu sun ce a ƙalla mutane tara ne dakarun Isra'ila suka kashe a lokacin da suke tsaka da zanga-zanga a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Lamarin na zuwa ne yayain da rikici ya ɓalle a garuruwan Ramallah da Nablus da Hebron da kuma Tulkarm.

    Rahotanni na cewa sama da masu zanga-zanga ɗari suka jikkata.

  7. Amurka ta fara kwashe 'yan ƙasarta daga Isra'ila

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar gwamnatin Amurka ta ce jirgin farko ɗauke da Amurkawa daga Isra'ila ya sauka a birnin Athens na jihar Georgia.

    Ana sa ran wasu ƙarin jiragen da za su tashi daga birnin Tel Aviv zuwa Athens nan da 19 ga watan Oktoba, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Fiye da Amurkawa 400 ne suka nuna sha'awar shiga jirgin farkon da ya tashi a ranar Juma'a.

    Mai magana da yawun fadar White House, John Kirby, ya ce gwamnatin Amurka na duba yiyuwar kwashe 'yan ƙasarta ta teku.

  8. Isra'ila na da 'yanci ta yi maganin Hamas - Ministan Tsaron Birtaniya

    Grant Shapps

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila na da 'yanci ta yi “maganin kungiyar Hamas” a cewar sakataren tsaron Birtaniya.

    Da aka tambaye shi, ko gwamnatin Birtaniya tana goyon bayan gargadin Isra'ila na cewa mutum miliyan 1.1 su fice daga arewacin Gaza cikin sa'a 24, Grant Shapps ya fada wa shirin BBC's Today cewa, abu ne mai muhimmanci ga Isra'ila ta yi bayani kafin ta dauki mataki.

    “Abu ne mai kyau ganin cewa sun samar da bayanai kafin (su fara kai hari), tabbas Hamas ba ta yi haka ba, kafin ta kutsa ta halaka mutane,” Shapps ya ce.

    Ya kara da cewa babu cikakkun bayanai game da shirin Isra'ila, kuma Shugaba Biden ya bayyana karara cewa akwai bukatar Isra'ila ta tabbatar da yin aiki sau da kafa da dokokin kasashen duniya.

    Ya kuma ce ya ba da umarnin tura jiragen ruwa da helikwaftoci da jiragen sama don samar da ayyukan bin diddigi da tattara bayanai kan shirin abokan gaba.

    “Birtaniya na kokarin ba da gudunmawarta wajen tabbatar da ganin, abin bai kara bazuwa ba,” Shapps ya ce

  9. Hare-haren Isra'ila sun ritsa da 'yan jarida a Lebanon

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Shaidun gani da ido sun ce Isra'ila ta yi luguden wuta a gabashin Lebanon, lamarin da ya kashe ɗan jarida guda.

    Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya tabbatar da mutuwar ma'aikacinta mai aukar hoton bidiyo, Issam Abdallah, tare da jikkata wasu abokanan aikinsa biyu.

    Ma'aikacin kamfanin dillacin labarai na AFP da gidan talabijin na Aljazeera na cikin mutanen da suka jikkata a harin da Isra'ilar ta kai a kusa da Alma Al-shaaab dake kusa da iyakar Isra'ila.

    'Yan jaridar sun je wajen ne domin ɗaukar rahoto kan rikicin Isra'ila da Ƙungiyar Hizbullah.

    Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai ba game da lamarin.

  10. An gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Iraƙi

    Dubbun mutane Bagadaza babban birnin Iraƙi, sun gudanar da zanga-zangar nuna ƙin jinin abin da Isra'ila ke aikatawa a Gaaza.

    Masu Zanga-zangar sun riƙa jan tutar ƙasar Isra'ila a ƙasa.

    Jagoran mabiya shi'a ,Moqtada al-Sadr ne ya shirya zanga-zangar tare da goyon bayan gwamnatin Iraƙi.

    Ana yin irin wannan zangar-zangar ta nuna goyon baya a Jordan inda sama da mutum 10,000 suka fito.

  11. Najeriya za ta raba wa matan karkara nau'in irin shinkafa

    r

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin mata ta Najeriya za ta raba tan 26,000 na nau'ikan irin shinkafa ga matan yankunan karkara domin rage tsadar shinkafar tare da bunƙasa nomanta da wadatar ta ƙasar da abincin.

    Ministar al'amuran mata ta ƙasar Mrs Uju Kennedy-Ohanenye ce ta bayyana haka a lokacin da take jawabi a taron manema labarai gabanin bikin ranar matan karkara ta duniya da za a gudanar ranar 15 ga watan Oktoba.

    Ta ce ” Wani kamfain ƙasar China ne ya bayar da tan 26,000 na irin shinkafar ga ma'aikatar".

    Misis Kennedy-Ohanenye ta yi kira ga matan da su tallafa wa manoman da kayan aiki domin rage wa matan karkara wahalhalu ta yadda za su samu amfanin gomna mai yawa.

    Ta ƙara da cewa uwar gidan shugaban ƙasar Misis Remi Tinubu za ta raba wa matan karkarar kayayyakin aikin noma miliyan 151.

  12. Matsayar hukumar FA kan Isra'ila da Gaza ya janyo ce-ce-ku-ce

  13. Hezbollah ta ce za ta shiga yaƙin Isra'ila don taimaka wa Falasɗinawa

    d

    Asalin hoton, Hezbollah

    Mataimakin shugaban ƙungiyar Hezbollah ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake masu na kada su shiga rikicin Gaza da Isra'ila.

    Na'im Qassem ya ce ƙungiyarsu a shirye ta ke domin yaƙar Isra'ila idan lokacin hakan ya yi.

    Ko satin da ya gabata ƙungiyar Hezbollah ta gwabza rikici da dakarun Isra'ila a kan iyakar Labanon.

    Kalaman na ƙungiyar sun zo daidai lokacin da ministan harkokin wajen Iran ya kai ziyara a birnin Beirut.

    Tehran na ba da tallafin kuɗi da na soji ga Hizbullah.

  14. Ambaliyar ruwa ta raba fiye da mutum 4000 da muhallansu a Ghana

    Fiye da mutum 4000 aka tilasta wa barin gidajensu a kudu maso gabashin Ghana sakamakon mummunar ambaliya ruwa da ta auku sakamakon fashewar madatsun ruwan Akosombo da Kpong.

    Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gidajen da gonaki suka lalace.

    An samu katsewar wutar lantarki da ruwan sha a wasu garuruwan.

    Hukumomin Ghana sun ce garuruwa tara da lamarin ya shafa na cikin tsananin buƙatar tallafi.

    Hukumar kula da kogin Volta, wadda ke lura da madatsun ruwan biyu, ta gargaɗi mutane da su fice daga gidajensu kafin ɓallewar madatsun biyu.

    Madatsun biyu su ke samar da kashi ɗaya bisa uku na wutar lantarkin ƙasar.

    An samu ƙaruwar ruwa amadatsun sakamakon mamakon ruwan sama a lokacin damina.

  15. An naɗa Jorge Vilda kocin tawagar matan Morocco

  16. Cikin hotuna: An yi tarukan nuna alhini ga Isra'ila a fadin duniya

    Mutane a fadin duniya na gudanar da gangami da tarukan nuna juyayi don nuna goyon baya ga Isra'ila bayan mummunan harin da kungiyar Hamas ta kai ranar Asabar da ta wuce.

    Israel Vigil

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, 'Yan majalisar wakilan Amurka sun gudanar da taron nuna juyayi ga Isra'ila ta hanyar kunna kyandira a wajen ginin Capitol da ke birnin Washington
    Israel Vigil

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Daliban Jami'ar Columbia a New York City sun shiga wani gangami da taron nuna alhini ga wadanda aka kashe a Isra'ila, da nufin mayar da martani ga wani gangamin dalibai a kusa, wanda aka shirya don nuna goyon bayan Falasdinawa
    Israel Vigil

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Bayanan hoto, Mutane suna karkada tutocin Isra'ila a lokacin taron nuna alhini a Montevideo, babban birnin Uruguay
  17. An ɗaura auren zawarawa da ƴan mata a Kano

    Dangi da ƴan'uwa gami da abokan arziƙi ne suka halarci Babban Masallacin Juma'a na Kano inda suka shaida auren zawarawa da ƴan mata da gwamnatin jihar Kano ta ɗauki nauyi gudanarwa.

    Gwamnatin jihar Kano ta ce ta nauyin auren zawarawa da 'yan mata kimanin 1,800 don tallafa musu wajen gina tushen rayuwar iyali da kyautata harkokin zamantakewa.

    An daura auren ne a Babban Masallacin Juma'a na Kano da kuma a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

    Shugaban hukumar na HISBA Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yace sun kafa wani kwamiti da zai rika bibiyar amaren don tabbatar da cewa sun zauna lafiya kuma babu saki ko cin mutunci.

    Sannan ya ce za su samar da kotun tafi-da-gidanka don gurfanar da duk angon da ya ci zarafin amaryarsa.

    Ga wasu daga cikin hotunan angwayen a lokacin da suka halarci wurin daurin aure na Babban Masallacin Juma'ar.

    ...
    ...
    ...
    ...
  18. Yadda ƙasashe za su yi gwawarmaya a gasar cin kofin Afirka ta 2024

  19. An buɗe bincike kan 'yan wasan Italiya Sandro Tonali da Nicolo Zaniolo

  20. Ambaliyar madatsar ruwan Ghana ta shafi ɗaruruwa

    ...

    Asalin hoton, @EFO DELA/TWITTER

    Sama da mazauna kudu-maso-gabashin Ghana 4,000 sun tsere daga gidajensu saboda ambaliyar ruwa.

    Sakamakon ambaliya da madatsar ruwa ta Akosombo ta yi, gidaje da gonaki sun lalace.

    An dai kawo cikas ga muhimman ayyuka, inda aka katse ruwa da wutar lantarki a wasu yankunan.

    A ranar Juma'a, gwamnatin Ghana ta ce dubban mutane, "a aƙalla gundumomi tara", sun rasa matsugunansu.

    A wani wuri kuma, Hukumar Kula da Bala'i da Haɗin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi rijistar raunuka bakwai.

    Hukumar kogin Volta ta Ghana a baya dai ta bukaci mazauna yankin da su matsa zuwa wani wuri mai tudu yayin da ruwan dam din ke ci gaba da hauhawa sakamakon ruwan sama mai karfin gaske.