Labarai da dumi-dumi, Yawan 'yan Isra'ila da suka mutu ya kai 1,000, in ji ofishin jakdanci
Akalla 'yan Isra'ila 1,008 aka kashe tun ranar Asabar, a cewar ofishin jakadancin Isra'ila a Amurka.
A wani sako da suka wallafa a shafin sada zumunta, ofishin jakadancin ya ce mutane fiye da 3,418 ne kuma aka jikkata.
Yarima Salman ya jaddada goyon bayan Saudiyya ga al'ummar Falasɗinawa
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mohammed Bin Salman, pictured last month
Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bin Salman ya tattauna da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta wayar tarho.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya ba da rahoton cewa, Yarima Bin Salman ya ce kasarsa za ta ci gaba da "taimaka wa al'ummar Falasɗin don cimma halastaccen 'yancinsu na rayuwa mai kyau, da cimma buri da fatansu da kuma samun zaman lafiya mai dorewa."
Ya kuma shaida wa Shugaba Abbas cewa yana aiki tare da dukkan bangarorin ƙasashe da na shiyya-shiyya don hana "kazancewar" rikicin.
Ya kamata a tuna cewa Abbas da Hamas mai iko da Zirin Gaza, abokan hamayya ne na siyasa.
Abbas ne ke jagorantar kungiyar Fatah mai iko da Gabar Yamma da Kogin Jordan. Shi ne kuma shugaban kungiyar tabbatar da 'yancin Falasdinu (PLO).
Sai dai goyon bayan Saudiyya ga Falasɗinawa na da matuƙar muhimmanci, domin ya sabawa koma-bayan tattaunawar bangarori guda uku da aka yi tsakanin Isra'ila da Saudiyya, da kuma Amurka da nufin daidaita alaƙa tsakanin gwamnatin Riyadh da ta Tel Aviv.
Manazarta na ganin cewa rikicin da ya ɓarke ya haifar da mummunar illa ga tattaunawar daidaita tsakanin manyan kasashen biyu na Gabas ta Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar bayan harin Hamas, Saudiyya ta dorawa Isra'ila alhakin tabarbarewar lamarin.
Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
Saudiyya ta yi gum a kan matakin Bahrain na farfado da alaka da Isra'ila
An tattara gawawwakin ƴan Isra'ila bayan kisan gillar kibbutz
Asalin hoton, AFP
Kafin safiyar yau, an ci gaba da gwabza fada a Kibbutz Kfar Azza, daya daga cikin garuruwan Isra'ila da ke kan iyaka da Gaza.
Hakan ce ta sa sai yanzu ne suke tattara gawawwakin 'yan Isra'ilan da aka kashe lokacin da Hamas ta keta shingen wayar karfe daga Gaza.
Yayin da muka nufi Kfar Azza, har a lokacin ana tura sojoji mayakan Isra'ila zuwa filayen da ke kewaye da kibbutz.
Ana jin amon makamai masu sarrafa kansu da suka kalli cikin iyakar Gaza. Sun ce suna ruguje wani gini bayan hango kai-kawo a hawa na biyu na gini.
Sojojin akasari sun fito ne daga rundunonin wucin gadi. Wani jami'i wanda ya ce shi mahaifin 'ya'ya shida ne ya amsa cewa al'ummar Isra'ila na tsananin rarrabuwar kai ta fuskar siyasa - amma ya dage a kan cewa yanzu sun hada kai saboda an kawo musu hari.
Mummunan harin ba-zata da Hamas ta kaddamar a kan Isra'ila
Isra’ila ta umarci Falasɗinawa su fice daga gidajensu
Bidiyo: Yadda al'amura suke a Birnin Gaza
Wakilin BBC Rushdi Abualouf ya dauki wannan bidiyo lokacin da yake zagayawa birnin Gaza a cikin mota bayan hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai
Bayanan bidiyo, Birnin Gaza: Zagaye cikin gine-ginen da aka rusa
Labarai da dumi-dumi, Sawun farko na dakarun Faransa ya bar Nijar - Rahoto
Asalin hoton, AFP
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ba da rahoton cewa Faransa ta fara janye sojojinta daga Nijar, bisa umarnin gwamnatin mulkin soja.
An ambato kakakin babban hafsan hafsoshin Faransa na cewa "dakaru na farko sun fice." daga kasar.
Tun da farko, shugabannin mulkin sojan Nijar sun ce dakarun Faransa za su fara fita daga kasar ranar Talatar nan cikin rakiyar sojojin Nijar.
Tun a watan Yuli ne aka fara zaman dar-dar tsakanin kasashen biyu, bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum.
Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne ke taimakawa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Sahel.
Faransa ta gama kwashe mutanenta daga Nijar
Shin wane tasiri janyewar dakarun Faransa za ta yi ga Nijar?
Abin da muka sani game da mutanen da aka yi garkuwa da su
Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan, ya ce akwai mutanen kasar tsakanin 100 zuwa 150 da ake garkuwa da su a Gaza, bayan sace su daga Isra'ila ranar Asabar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta yi magana da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kamar 50, kuma za ta tuntubi karin wasu, yayin da sojoji ke tantance bayanai.
A daren jiya, Hamas ta ce za ta kashe mutanen da take garkuwa da su, idan Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama ba tare da gargadi ba.
BBC ta zanta da wasu mutane da aka sace makusantansu a Isra'ila.
Bayanan hoto, Yoni Asher ya ce ya shaida matarsa Doron (a tsakiya) da 'ya'yansa Aviv (hagu) da Raz (dama) 'yan ta-da-kayar-baya na tura su bayan wata babbar mota
Wata uwa ta bayyana mugun ganin da ta yi a Gaza bayan luguden bama-bamai
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Gidaje da gine-gine sun lalace a harin sama da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza
Wata mahaifiya a Birnin Gaza ta bayyana yadda ta tsallake rijiya da baya tare da 'ya'yanta cikin tsakiyar dare lokacin da jiragen yakin Isra'ila suka yi wa unguwarsu luguden bama-bamai.
Najla Shawa, wadda take aiki ga kungiyar ba da agaji ta Oxfam, ta fada wa BBC cewa ta dauka tana wani bangare 'mai aminci' a birnin.
“Mutane sun tsere zuwa gidanmu, inda muke da mutum 18 da ke zaune tare da mu tun daga yammacin jiya,” in ji ta.
Sai dai ihun mutane ya sa ta farka daga barci da misalin karfe 1 na dare, yayin da mutane suke gudu.
"Za ku iya kaddara irin faduwar gaban da mutane suka shiga – a inda ake da kananan yara guda shida a gidan, da jimillar mutum 20 daga iyalai daban-daban, inda suka nufi wurin motocinmu suna kokarin shiga su tsere.”
Bayan sun yi kokarin samun mafaka a wani gidan abinci cikin tsakar dare, Najla ta ce ta koma gida inda ta ga ginin da ke kallon nasu “an yi masa rugu-rugu” yayin tagogin gidanta suka tarwatse.
"Tashin ['ya'yana] daga barci a irin wannan hali na fargaba - Ba na jin zan taba mancewa da wadannan lokuta a rayuwata."
Wace ce Hamas, mene ne ke faruwa a Isra'ila, da sauran tambayoyi
Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
Faransa za ta fara janye sojojinta daga Jamhuriyar Nijar a Talatar nan
Asalin hoton, AFP
Shugabannin mulkin sojan Nijar sun ce dakarun sojin Faransa za su fara janyewa daga kasar a yau Talata.
Ana takun-saka tsakanin kasashen biyu tun bayan juyin mulkin sojoji a watan Yuli da ya hambarar da zababben shugaban kasar kuma babban aminin kasar Faransa Mohamed Bazoum.
Rundunar sojin Nijar ta ce za ta yi wa kwambar motocin farko na sojojin Faransa rakiya zuwa wajen kasar. Ba a fayyace yadda tafiyar za ta kasance ba.
Har yanzu bakin iyakokin Nijar da makwabciyarta Benin da Najeriya a kudu na rufe.
Amma sauran iyakoki da kasashen Mali da Burkina Faso da Chadi waɗanda kuma ke karkashin mulkin soja, suna na nan a bude.
Kimanin sojojin Faransa 1,500 ne ke taimakawa Nijar wajen yaƙar 'yan ta-da-kayar-baya masu alaka da al-Qaeda da kungiyar IS.
A watan Agusta ne, gwamnatin mulkin sojan ƙasar ta buƙaci Faransa ta fice daga Nijar, inda ta zarge su da yunkurin mayar da Shugaba Bazoum kan mulki da karfi.
An shafe makonni ana zanga-zanga a wajen wani sansanin sojojin Faransa na Yamai babban birnin kasar.
Da farko dai, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ƙi amincewa da janye sojojin, amma daga bisani ya amince da bukatar haka a watan jiya, yana mai cewa za su bar ƙasar a karshen shekara.
A baya dai, ana kallon Nijar a matsayin daya daga cikin manyan aminan Kasashen Yamma a yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci.
Tasirin Faransa yana raguwa a can bayan juyin mulkin da aka yi cikin wasu kasashe da ta yi wa mulkin mallaka.
Shin wane tasiri janyewar dakarun Faransa za ta yi ga Nijar?
Me ya sa har yanzu wasu ƙasashen Afirka ke maraba da sojojin Faransa?
Algeria ta dakatar da shiga tsakani a rikicin juyin mulkin Nijar
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, The Niger military took power in a coup in July
Algeria ta bayyana dakatar da yunkurinta na shiga tsakani a rikicin siyasar Nijar bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta sanar a cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa, sanarwar da hukumomin Nijar suka fitar ta haifar da "halastattun tambayoyi game da ainihin aniyarsu ta amincewa da shiga tsakanin Aljeriya".
A yanzu dai, an dakatar da wannan mataki har sai sun samu tabbataciyar magana daga shugabannin mulkin sojan Nijar a kan ci gaba da shiga tsakanin.
A watan jiya, Nijar ta amince da tayin Aljeriya na shiga tsakani a rikicin siyasarta, da nufin mayar da kasar kan tafarkin dimokradiyya.
A watan Agusta, Aljeriya ta bai wa mahukuntan Nijar shawarar mika mulki a cikin wata shida zuwa hannun gwamnatin farar hula.
Sai dai shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar, Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya karbe iko a watan Yuli, ya bukaci mika mulki a cikin shekara uku.
Aljeriya ta kuma nuna rashin amincewa da matakin soji a matsayin hanyar warware rikicin Nijar bayan barazanar da kungiyar Ecowas ta yi na yiwuwar tura dakarun sojoji su mayar da mulkin dimokradiyya.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ya yi maraba da matakin shiga tsakanin, amma wannan sabon lamari zai kara kawo cikas ga ƙoƙarin warware rikicin siyasar Nijar.
Masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar Nijar
Shiga tsakanin da zai iya hana Ecowas auka wa Nijar da yaƙi
Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a Gaza yanzu ya kai 770
Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce adadin mutanen da suka mutu tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da harin ramuwar gayya a ranar Asabar kan Zirin Gaza sun kai 770
Ma'aikatar ta kuma ƙara da cewa Kusan mutum 4,100 ne suka jikkata.
Za a umarci kamfanonin jiragen saman Najeriya su biya fasinjoji diyya kan jinkirin tashi
Gwamnatin Najeriya ta ce nan ba da dadewa ba, za ta tilasta wa kamfanonin jiragen sama su fara biyan diyya ga fasinjoji saboda jinkiri ko soke tashi jirgi, matuƙar ba wani al'amari ne daga Allah ya haddasa matsala ba.
Gidan talbijin na Channels ya ambato ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo na bayyana haka lokacin da yake ganawa da kamfanonin jiragen sama a Abuja ranar Litinin.
“Dangane da jinkiri ko soke tashin jirgin sama, ina so na tabbatarwa al'ummar Najeriya da ke korafi a kullum game da irin wannan matsalar, za mu fara aiwatar da tanade-tanaden dokar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya’ wadanda 'yan Najeriya ba su san da su ba,"
"Wannan tanadi shi ne kamfanonin jiragen sama za su biya diyya a kan jinkiri ko soke tashin jirgi, matuƙar ba wata matsala ce ta faru sanadin wani al'amari daga Allah ba.
"Amma idan wani al'amari ne daga Allah, babu wata diyya da za su biya."
Sai dai Keyamo ya bukaci ma’aikatan kamfanonin jiragen sama su samar da hanyoyin sadarwa tabbatattu da ke bai wa fasinjoji damar samun bayanai a kan jinkiri ko sokewar tashin jiragen sama.
Rashin wuta ya sa dubban fasinjoji sun makale a filin jirgin Amurka
Yadda fasinja ya fitsare wata mata a jirgin sama
Muna yaba wa waɗanda suka shirya kai hari kan Isra'ila - Shugaban Iran
Asalin hoton, EPA
Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya musanta hannun ƙasarsa a munanan hare-haren da kungiyar Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila ranar Asabar.
Amma - a cewar fassarar da kamfanin dillancin labarai na Reuters - Khamenei ya ce: "Muna yaba wa waɗanda suka shirya kai hari a kan gwamnatin masu tsananin kishin Yahudanci".
A matsayin tunatarwa, an san Iran tana ba da kuɗade ga Hamas, da kuma ba da horo da makamai ga mayakan Hamas.
Mutum 187,000 sun rasa matsugunansu a Gaza - Majalisar Dinkin Duniya
Halin da ake ciki a Gaza yanzu in ji hukumar kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya
Sama da mutum 187,000 sun rasa matsugunansu a fadin Zirin Gaza - kuma ana tsammanin adadin zai karu.
Akwai mutum 137,500 da ke samun mafaka a makarantun Majalisar Dinkin Duniya guda 83.
Ofishin Hukumar ba da agaji ta MDD (UNRWA) a Gaza ya "lalace saboda hare-haren jiragen yaki."
Mutane KUSAN rabin miliyan a Gaza ba su samu damar karbar agajin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ba a wannan makon, yayin da aka rufe cibiyoyin raba kayan abinci.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya yi magana da Bazoum
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An hambarar da Mohamed Bazoum ne a juyn mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Yuli
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum domin jaddada goyon bayansa ga zababbiyar gwamnati.
Ya jaddada cewa "gwamnatin farar hula da aka zaba ita ce hanya mafi dacewa da za ta taimaka wa Nijar zama abokiyar tafiya a fannin tsaro da ci gaban yankin," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Matthew Miller.
Tun a ranar 26 ga watan Yuli, aka kifar da gwamnatin Bazoum, kuma sojoji na ci gaba da tsare shi tare da iyalansa.
Amurka "na kira a sako shi tare da duk wadanda aka kama ba bisa ka'ida ba, tun bayan da sojoji suka kwace mulki," in ji Miller.
Sojoji karkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, sun ce za su mika mulki hannun gwamnatin farar hula a cikin shekara uku, amma kungiyar Ecowas ta ki amincewa da wannan bukata.
Kungiyar Ecowas na kokarin sasantawa da shugabannin mulkin soja da suka yi juyin mulki kuma sun yi gargadin cewa idan diflomasiyya ta ki aiki, to za a iya tura dakaru zuwa Yamai.
Kullum sai na yi magana da Bazoum - Shugaban Faransa
Ci gaba da tsare Mohamed Bazoum na jawo ƙarin barazana
Manyen Kasashe Yamma sun yi Allah-wadai da harin Hamas kan isra'ila
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Shugabannin kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Italiya sun yi Allah-wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila, suna masu bayyana hakan a matsayin ta'addanci.
Ƙawayen na Isra'ila biyar sun ce za su ci gaba da jajircewa wajen bayyana goyon bayansu ga Isra'ila, na kare kanta.
Ko da yake sun amince da 'yancin Falasdinawa na neman cin gashin kansu, sun ce abun da Hamas ta yi, ba shi bane mafita.
A wajen Turai, China, ta bukaci a yayyafa wa zukata ruwa, yayin da itama Rasha ta ce dakatar da bude wuta shine abun da ya fi komi muhimmanci a yanzu.
A halin da ake ciki, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya buƘaci bangarorin biyu da su tsagaita wuta.
Yarima mai jiran gado na Saudiyya Muhamad Bin Salman ya yi waya da shugaban Faladinawa Mahmoud Abbas, inda ya shaida masa cewa Saudiyya na tare da su.
Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza
Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
Ƴan Laberiya na zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki
Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Laberiya na kada ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki.
'Yan takara 19 ne ke fatan maye gurbin tsohon gwarzon ƙwallon ƙafar na duniya George Weah, wanda ke neman wa'adi na biyu.
Manyan masu ƙalubalantar dai su ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Joseph Boakai da dan kasuwa Alexander Cummings.
Dukkansu sun kasance cikin ƙawancen jam'iyyun adawa amma ƙawancen ya tarwatse bayan samun saɓani a kan wanda zai shige musu gaba don takarar shugaban ƙasa.
Duk da samun ci gaba ta fuskar ilimi da samar da wutar lantarki, masu suka sun ce cin hanci da rashawa sun ƙara samun wurin zama a zamanin mulkin Weah.
Ya yi alƙawarin gina sabbin hanyoyi, batun da ya zo daidai kan gaɓa a lokacin zaɓe, inda aka katse manyan hanyoyin sadarwa na Laberiya daga Monrovia, babban birnin kasar.
Weah dai ya hau mulki ne a shekarar 2017, da goyon bayan jama'ar Laberiya, bayan yunƙuri guda biyu ba tare da nasara ba a baya.
George Weah ya kai zagaye na biyu a zaben Liberia
'Yan Liberia na zaben shugaban kasa
Hotunan bayan harin da sojojin Isra'ila suka kai cikin dare a Gaza
Rundunar sojin saman Isra'ila dai ta ce ta kai hari kan wasu 'yan bindiga 200 cikin dare.
Kusan mutum 700 ne suka mutu a Gaza a hare-haren da aka kai ta sama tun ranar Asabar, in ji hukumomin yankin.
Ga hotunan barnar da hare-haren da sojojin Isra'ila suka yi cikin dare.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Getty Images
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Isra'ila ta shafe dare na uku tana luguden wuta a Zirin Gaza
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, ...
Isra'ila ta kwashe tsawon dare tana luguden wuta a zirin Gaza, kwanaki uku bayan harin da mayakan Hamas suka kai mata, tare da halLaka sama da mutum 900.
Tuni kasar ta hana shiga ko fita a zirin Gaza, kana ta yanke, ruwa da wuta da kuma shiga da kayan abinci da na agaji.
Lamarin dai ya janyo suka daga sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce akwai buƙatar bayar da damar kai taimakon gaggawa.
Mazauna Gaza da suka firgita na kokarin tserewa gidajensu yayin da bama-bamai ke fado musu.
Isra’ila ta umarci Falasɗinawa su fice daga gidajensu
Isra'ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne
Assalamu alaikum
Masu bibiyar mu barkanmu da safiyar Talata
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa tare da ni Aisha Babangida.
Ku kasance da mu tsawon yinin yau, domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban har ma da Najeriya.