Yanzu muka fara - Netanyahu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Buhari Muhammad Fagge

  1. An kashe 'yan kasar Thailand 12 tare da yin garkuwa da 11

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Thailand ta ce an kashe 'yan kasarta 12 tun bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare a safiyar Asabar.

    An kuma yi garkuwa da wasu 11, sannan takwas sun jikkata.

    Wani ma'aikaci ɗan kasar ya shaida wa BBC cewa an kusa kashe shi ranar Asabar.

    "Ina cikin rarrafe a karkashin wata babbar mota kawai sai mutanen Hamas suka jawo ni suka nuna min bindiga," in ji shi.

    Akwai dai kusan 'yan ƙasar Thailand 30,000 a Isra'ila, kuma kusan 5,000 a Zirin Gaza.

    • Israel ta kai wa Gaza hari bayan martanin Hamas da balan-balan
    • An harbe sojan da ya kashe mutum 26 a Thailand
  2. Isra'ila ta kai hari sansanin 'yan gudun hijira a Gaza

    Hare-haren Isra'ila zuwa Gaza sun samu wasu sansanonin 'yan cirani biyu, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Falasdinawa ta bayyana.

    Rahotanni sun ce daga sansanin Al-Shati har na Jabalia an kai musu hari, kuma gwamman mutane sun mutu wasu sun jikkata.

    Akwai sansanin 'yan cirani takwas da aka amince da zamansu a yankin Zirin Gaza mai cikowar al'umma.

    • Isra'ila ta kai hari sansanin 'yan gudun hijira a Gaza
    • Abin da ya sa ba ma so mu koma gida — ‘Yan gudun hijira
  3. Poland ta fara kwashe mutanenta daga Isra'ila

    Ƙasar Poland ta fara kwashe mutanenta daga Isra'ila, yayin da jirgin farko da ya kwashe mutum 120 ya sauka a Warsaw a safiyar Litinin.

    "Mutanen farko da aka ɗebe daga Isra'ila sun sauka a Polad.

    "Ina so na miƙa godiyata ga sojojinmu saboda da yin aikin yadda ya dace. Sun yi abin da ya kamata," in ji ministan harkokin tsaron Poland Mariusz Blaszczak

    Akwai jirage biyu da ake sa ran za su sauka a ƙasar a yau.

    A ranar Lahadi ministan ya ce a kwai kimanin 'yan Poland 200 da ke yawon buɗe ido a Isra'ila, ciki har da yara da suka je ziyara daga makaranta. kuma suna tsammanin su bar ƙasar a ko da yaushe.

    Akalla sojojin Poland 200 ne suka shiga aikin taimakon.

    • Hankalin kasashen duniya ya karkata kan harin Poland
    • Yadda yaƙi tsakanin ƙasashe zai kasance nan gaba a duniya
  4. Ƙasashe na rige-rigen kwashe mutanen su daga Isra'ila da Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Gaza da Isra'ila, kasashe na ƙoƙarin fitar da 'yan kasarsu.

    A yau ne wani jirgin sama daga Tel Aviv zuwa Serbia ya sauka, kuma ofishin jakadancin Serbia ya ce an shirya wani jirgi.

    Ministan harkokin wajen Romania ya ce an mayar da mutane kusan 800 gida daga Isra'ila, da sa ran maido da sauran.

    Gwamnatin Thailand ta ce tana shirya tawagogin gaggawa da jiragen sama don ceto 'yan kasar daga Isra'ila.

    Ana kuma shirye-shiryen jiragen sama daga Kazakhstan, a cewar ma'aikatar harkokin wajen ƙasar.

    A safiyar yau kasar Poland ta tabbatar da cewa jirgi na farko ya koma ƙasar daga Isra'ila tare da farar hula a cikinsa.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Burtaniya ta yi gargadi game da tafiye-tafiye zuwa Isra'ila

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Sojojin Israila sun fara janye farmaki kan Falasdinawa a Jenin
  5. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta ba da umarnin a datse Gaza gaba ɗaya

    g

    Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya yi umarnin a "yi wa Zirin Gaza ƙawanya, babu shigar abinci, babu wuta sannan ba man fetur".

    A wani mataki na matashiya - Isra'ila ce ke da iko da sararin samaniyar Gaza da kuma hanyoyin ruwansa, sannan ta sanya takunkumai a kan wane ne da kuma me za a iya shiga da shi ta kan iyakar yankin.

    Haka kuma a ɗaya bangaren, inda Masar ke iko da iyakar Gazan, ita ma tana lura da wane ne zai shiga ko kuma ya fita daga yankin.

  6. Labarai da dumi-dumi, Ana ta jin ƙarar jiniyar hare-haren a Ƙudus da faɗin Isra'ila- IDF

    Ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce ana ta jin ƙarar jiniyar hare-hare da ta cika birnin Ƙudus da faɗin Isra'ila sakamakon makaman roka da ake harbawa daga Gaza.

    An ji aƙalla ƙarar fashewar abubuwa uku a birnin Ƙudus.

    Babu wanda ya sani ko waɗannan rokoki sun dira ko kuma sojojin Isra'ila sun iya kakkaɓo su.

  7. Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya kusa 500

    Adadin mutanen da da suka mutu a hare-haren da Isra'ila takai Gaza ya ƙaru zuwa 493, in ji ma'aikatar lafiya ta ƙasar.

    Adadin waɗanda suka jikkata kuma cikin Falasɗinawa ya kai 2,751.

  8. Kimanin mutum 30 suka mutu a zaftarewar ƙasa a Kamaru

    Cameroon landslide

    Asalin hoton, REUTERS

    Bayanan hoto, Zaftarewar lakar ta janyo rugujewar gidaje 25

    Adadin mutanen da suka mutu sanadin zaftawar kasa ranar Lahadi a Yaounde babban birnin kasar Kamaru ya karu zuwa mutum 30, yayin da karin 17 suka ji raunuka.

    Ministan cikin gidan Kamaru wanda ya je wurin da abin ya faru ne don ganin irin barnar da aka yi ya sanar da haka.

    Gidaje da dama a Mbankolo, wata unguwar masu karamin karfi, sun ruguje sun zama baraguzai, bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya. Haka kuma akwai fargabar cewa karin mutane ne gine-gine suka rufta da su kuma har yanzu ba a kai ga gano su ba.

    “Mun sanya ayarin jami'ai da zai ci gaba da aiki tsawon rana don gano mutane," kamar yadda ministar gidaje da raya birane, Celestine Ketcha Courtès ta fada wa BBC.

    Daga cikin wadanda aka kubutar, har da jariri dan wata uku.

    Hukumomi sun bukaci mazauna unguwar wadda ake dauka a matsayin yanki mai hatsari, su fice daga cikinta saboda fargabar sake aukuwar zaftarewar kasar.

    Mazauna unguwar sun fada wa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da ruwan sama ya tumbatsa a wani kogin yanki. Mutanen da suka yi asarar komai nasu, sun ce ba su da wani wuri da za su iya zuwa.

    Wani gidan rediyon yankin ya ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 40. Ambaliyar ruwa na ci gaba da kawo cikas ga ayyukan ceto, abin da ya tilasta wa mutane yin amfani da hannuwansu wajen zakulo gawawwaki daga cikin laka.

    Iftila'in ya zo ne kusan shekara daya bayan akalla mutum 14 sun mutu a wata zaftarewar lakar da ta faru a birnin.

    Unguwar talakawa ta Mbankolo ce iftila'in ya fi muni a lamarin na baya-bayan nan, inda gidajen da aka gina a gangare, suka ruguje, ambaliya ta jijjige bishiyoyin ayaba.

    An ga gawawwakin kananan yara "kwakkwance a kan tabo@, wani mazaunin unguwar ya shaida wa kafar yada labarai ta Cameroon Voice.

    • Zabtarewar kasa: Mutum 40 sun mutu ana neman 13 a Kamaru
    • Mutum 50 sun mutu sakamakon zaftarewar kasa a Dimukradiyyar Kongo
    f
  9. Iran ta musanta hannu a harin da Hamas ta kai Isra'ila

    g

    Iran "ba ta da hannu" cikin harin da Hamas ta kai kudancin Isra'ila, in ji ofishin jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya.

    "Muna jaddada goyon bayanmu ga Falasɗinawa; amma duk da haka ba mu da hannu a matakin da Falasɗinawa suka ɗauka, saboda su ne suka ɗauki matakinsu da kansu,"kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wata sanarwa da suka fitar ta fada.

    Tun da fari Hamas ta ce ta kai harin ne da taimakon Iran a cikin ƙarshen makon.

    Iran dai ta jima tana goyon bayan Hamas na tsawon shekaru kuma tana bai wa mayakanta makamai da horo.

    Sai dai sakataren harkoki wajen Amurka Antony Blinken ya shaida wa CNN a ranar Lahadi cewa Gwamnatin Amurka "ya zuwa yanzu ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa Iran na da hannu cikin wannan rikin".

    • Amurka ta fara matsar da jiragen yaki kusa da Isra'ila bayan harin Hamas
    • Isra'ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne
  10. Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a wajen shagalin Isra'ilawa ya kai 260

    Adadin Isra'ilawan da suka mutu a wajen wani bikin kiɗa ya kai 260, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Isra'ila ke rawaitowa.

    Kimanin mutum 3,000 ne suka halarci shagalin wanda Hamas ta ɗana wa tarko da mummunan hari.

    An yi shagalin ne a hamadar Negev, kusa da Kibbutz Re'im wanda ba shi da nisa da Zirin Gaza.

  11. An rufe ofishin jam'iyyar adawa a Uganda

    g

    Asalin hoton, Google

    'Yan sanda a Uganda da sojoji sun rufe hedikwatar ofishin jam'iyar adawa ta NUP, jam'iyyar da Bobby Wine yake jagoranta.

    "An jibge jami'an tsaro dauke da makamai a sakateriyarmu da ke Kamoukia, kuma ba su da adadi," kamar yadda kakakin jam'iyyar ya wallafa a shafinsa a ranar Litinin.

    Bobby Wine ya ce jami'ai sun kai hari hedikwatar jam'iyyar sun hana mutane shiga ko kuma fita daga gnin jam'iyyar.

    Mawaƙin wanda ya zama ɗan siyasa ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa wannan ƙawanyar da jami'an suka yi wani mataki ne na dakatar da shirin addu'ar da jam'iyyar ta tsara a ofishinta da ke Kampala a a ranar Litinin.

    • Yoweri Museveni: Shin shugaban Uganda yana son yin mulki har abada?
    • Ali Bongo da shugabannin Afirka da suka kafe a kan mulki
  12. Hotunan abubuwan da ke faruwa daga Gaza da Isra'ila

    g

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hayaƙi kawai ake gani tsakanin gine-gine a Gaza bayan hare-haren Isra'ila
    f

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Falasɗinawa na kallon wasu ƙonannun motoci bayan harin sama da Isra'ila ta kai cikin dare
    f

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A Ashkelon wani mutum na leƙe ta tagar gidansa domin ganin ɓarnr da rikicin ya haifar ya zuwa yanzu
    g

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani sojan Isra'ila da ke aiki a kan iyaka na zaune a kan akwatun harsashi yana duba wayarsa
  13. Wannan hari daidai yake da na 9/11 da aka kai wa Amurka - Isra'ila

    A ɗazu ne wanus manyan jami'an Isra'ila biyu suka kwatanta hare-haren da aka kai musu ranar Asabar daga Gaza a matsayin waɗanda suka yi daidai da na 9/11 da aka kai Amurka.

    "Wannan shi ne harinmu na 9/11," in ji kakakin Manjo Nir Dinar "Sun same mu kwarai".

    Laftanar Kanar Jonathan Conricus shi ma ya kwatanta harin na Hamas da manyan hare-haren da aka kai wa Amurka.

    "Wannan zai iya zama harin 9/11 da kuma na Pearl Harbor idan aka haɗe baki ɗaya," in ji shi.

    "Wannan ita ce mummunar rana a tarihin Isra'ila.

    "Babu wani abu guda da ya taba kashe Isra'ilawa da yawa kamar haka, har da hare-haren makiya."

  14. Abin da muka sani ya zuwa yanzu daga Isra'ila da Gaza

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da gari ke shirin wayewa a Isra'ila, ana ci gaba da gwabaza faɗa tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas.

    Wataƙila yanzu ka fara bin labarin, to idan haka ne ga wasu daga cikin abubuwan da muka sani ya zuwa yanzu.

    • An kashe sama da mutum 1,100 tsakanin ɓangarorin biyu a mumunan faɗan da ya kaure wanda Hamas ta fara kai hari a safiyar ranar Asabar
    • Kimanin sa'o'i 37 da fara wannan rikici an raba makaman roka masu yawa daga Gaza zuwa kudancin Isra'ila.
    • Hare-hare ramuwar da Isra'ila ta kai na sama ya janyo raba Falasɗinawa 123,000 daga muhallansu a Gaza yayin da kusan 74,000 suka fake a makarantu, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana
    • Asibitoci a Gaza sun yi cikar kwari kuma suna ta fama da katsewar wuta. MDD ta ce zai ɗauki lokacin kan wuta ta dawo a gaza.
    • Ƙasashen duniya da dama sun yi koken an kashe mutanensu wasu kuma sun ce an sace 'yan ƙasarsu da yawa
    • Amurka ta aike da wani ƙaton jirgin ruwanta mai ɗauke da jiragen ruwa masu yawa kusa da Isra'ila inda ta yi alƙawarin sake aikewa da makamai - a wani mataki da ta yi tir da shi na takalar faɗa daga Hamas.
    • Jami'an Isra'ila na sa ran Isra'ila ta ƙaddamar da wasu hare-hare zuwa Gaza nan da kwanaki biyu
    • Farashin mai ya yi tashin gwaron zabi saboda wanan rikici da zai iya janyo tsaiko a safararsa zuwa Gabas ta Tsakiya
    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Hotunan tashin hankali da fargabar da mutane ke ciki
    • Israel-Gaza: Abin da doka ta ce a kan rikicin Isra’ila da Falasdinawa
    d

    Asalin hoton, EPA

  15. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye tare da ni Aisha Babangida da Buhari Fagge

    Ku kasance da mu tsawon yinin yau, domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya daban-daban har ma da Najeriya.