Atiku ya nemi haɗin kan Kwankwaso da Obi wajen binciken Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida, Rabiatu Kabir Runka and Haruna Kakangi

  1. Gwamnatin Biden ta ci gaba da gina katanga tsakanin Amurka da Mexico

    ...

    Gwamnatin Shugaba Biden ta yi amfani da ikonta na zartarwa wajen tsallake wasu dokoki 26 na tarayya, don ci gaba da aikin gina katanga a iyakar kasar da Mexico, da zummar rage kwararar bakin haure.

    Biden dai ya yi ta sukar manufar tsohon shugaban kasar Donald Trump ta gina katanga lokacin da yake takara da shi a shekarar 2015.

    Ɗaya daga cikin matakan da ya fara dauka a matsayinsa na shugaban ƙasa shi ne dakatar da gina katangar inda yayi alkawarin cewa a zamaninsa, babu sake yin almubazzaranci da sunan gina katanga.

    Abun da ya sa a yanzu masu suka ke ganin ya yi amai ya lashe.

    Umurnin zartarwa da ya bayar da nufin gina katangar a yanzu, na nufin hukumomi ba za su yi doguwar shari'ar kalubalantar keta dokokin muhalli ba.

    • Dalilan da suka sa miliyoyin Amurkawa ke zuwa Mexico neman lafiya
    • Poland za ta gina katanga kan iyakarta da Belarus saboda ƴan gudun hijira
  2. Mahaukaciyar guguwar Koinu ta yi barna a Taiwan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gawurtacciyar guguwar Koinu mai tafe da ruwan sama, ta isa kudancin Taiwan, da karfin tafiyar kilomita 250 cikin sa'a daya.

    An soke tashin jiragen sama fiye da 100, tare da rufe makarantu tun ana dakon isarta.

    An rufe ofisoshi da dama, sannan ruwan sama da iska sun mamaye yankin.

    Wakiliyar BBC da ke yankin ta ce lamarin ya haifar da faduwar bishiyoyi da dama, kuma ta ga kayan karafa da rufin gidaje na yawo a cikin iska, wasu a warwatse, akwai kuma motocin agajin gaggawa da ke kokarin ceton mutane.

    Bayan ta ratsa yankin Taiwan, ana hasashen guguwar za ta nufi lardunan Guang-dong da Fujian da ke kudancin China, sannan za ta nufi yankin Hong Kong, inda a can ne ake hasashen karfinta zai dan ragu.

    • Mahaukaciyar guguwa da ta shafe fiye da wata ɗaya tana ɓarna
    • Yadda mummunar guguwa ta afku a Iraki sau takwas a wata ɗaya
  3. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa barkan mu da safiyar Alhamis

    Ku kasance da mu a wannan shafi na kai-tsaye domin kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku a wannan lokaci.