Abin da ya sa nake bincike kan takardun karatun Tinubu - Atiku

Asalin hoton, ATIKU ABUBAKAR
Lauyan ɗan takarar shugaban ƙasa na jami’iyyar PDP ya ce “Takardar shaidar kammala karatu da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa hukumar zaɓe ta INEC na bogi ne.”
Lauyan ya faɗi haka ne jim kaɗan bayan ɗan takarar, Atiku Abubakar ya kammala ganawa da manema labaru yau Alhamis a Abuja.
Lauya Kalu Kalu ya ce takardar kammala karatun digiri da Tinubu ya miƙa wa Inec ba na gaskiya ba ne.
Fadar shugaban ƙasa dai ta sha musanta wannan zargi.
Taƙaddama ta ɓarke a Najeriya tsakanin Atiku Abubakar wanda ke ƙalubalantar zaɓen shugaba Tinubu, da kuma ɓangaren na shugaban ƙasa ne tun bayan da Atiku ya nace kan samun takardun karatun shugaba Tinubu daga jami’ar jihar Chicago da ke Amurka.
Sai dai a cikin makon nan ne jami’ar ta fitar da takardun, inda ta tabbatar da cewa Bola Tinibu ya yi karatu a jami’ar.
Sai dai bayan yin nazari kan takardun an ci gaba da samun ƙorafe-ƙorafe daga ɓangaren Atiku da jam’iyyar PDP, inda suka nuna shakku kan bayanan da ke ƙunshe a cikin takardun.
Lauya Kalu ya ce takardun da jami’ar ta fitar sun nuna cewa “Bola Ahmed Tinubu ya haɗa takardar kammala karatu ta bogi tare da miƙa wa Inec.
“Na biyu, sunan da ke jikin takardar karatun da aka yi amfani da ita domin shiga jami’ar jihar Chicago na ƙunshe ne da sunan mace, wanda ke nuna cewa ba na Bola Ahmed Tinubu ba ne.
“Na uku, Takardar da aka yi amfani da ita wajen shiga jami’ar Chicago ta nuna cewa Bola Ahmed Tinubu ya yi karatunsa na sakandare ne a kwalejin gwamnati da ke Legas, inda ya kammala a 1970, to amma a zahiri an kafa kwalejin ce a 1974.
“Takardun sun nuna cewa wanda ya mallaki takardar baƙar fata ne ɗan Amurka, amma takardun da Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa Inec ya bayyana cewa ƙasa ɗaya ce kawai yake amsawa, wanda hakan ke nufin cewa ba takardunsa ba ne.















