Majalisar Dattijai za ta tantance shugaban CBN da Tinubu ya naɗa

Asalin hoton, CITIBANK
A yau ne Majalisar Dattawa za ta gudanar da aikin tantance Olayemi Cardoso, tsohon Shugaban Bankin Citi a Najeriya a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN.
Bugu da kari kuma, za a tantance wasu mutane hudu da aka zaɓa a matsayin mataimakan gwamnonin Babban Bankin Najierya, domin su hada karfi da karfe da Cardoso don tafiyar da harkokin bankin a cikin shekaru biyar masu zuwa.
A cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na shugaban majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele ya fitar, majalisar za ta tantance duk waɗanda aka miƙa sunan su bayan ta dawo daga hutun ta na shekara.
Sanarwar ta kara da cewa, “Majalisar dattawan tarayyar Najeriya za ta koma zaman ta a ranar Talata 26 ga watan Satumba. Za mu yi nazari kan tantance Dr. Cardoso a kwamitin baki daya.“
"Za a kuma tantance mataimakan gwamnoni hudu da suka hada da Emem Nnana Usoro da Muhammad Sani Abdullahi Dattijo da Philip Ikeazor da kuma Dakta Bala M. Bello.“
A ranar 15 ga watan Satumba ne shugaba Tinubu ya amince da nadin Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Ya kuma amince da nadin mataimakan gwamnoni hudu na tsawon shekaru biyar kowanne a matakin farko, har zuwa lokacin da majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta amince da su.
- Wane ne sabon Gwamnan CBN Olayemi Cardoso?
- Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele








