Atiku ya ɗaukaka ƙara kan zaɓen Tinubu zuwa Kotun Ƙoli

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. An gurfanar da masu son kafa ƙungiyar Wagner a Ghana kotu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Hukumomi a Ghana sun gurfanar da mutum biyar a gaban kotu bisa zargin kafa ƙungiyar sojojin haya ta Wagner a ƙasar.

    An kama waɗanda ake zargin ne a watan jiya a garin Takoradi da ke kudancin Ghana.

    Wata 'yar majalisa daga yankin, Ramatu Ibrahim ta shaida wa BBC cewa waɗanda ake zargin sun shirya wani abin da suka bayyana a matsayin zanga-zangar ƴanci ta Wagner.

    Rundunar ƴan sanda a Ghana har yanzu ba ta bayar da cikakken bayani game da kama mutanen a hukumance ba.

    Ƙasar Rasha na ƙara faɗaɗa tasirinta a nahiyar Afirka, ta hanyar sojojin haya na Wagner, inda ta jibge dakaru a ƙasar Mali da ke yankin Sahel na yammacin Afirka da kuma Libya da Sudan har ma da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

  2. Atiku ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli don ta soke nasarar Tinubu

    A

    Asalin hoton, Atiku P

    'Yan takarar na manyan jam'iyyun adawar Najeriya, Atiku Abubakar na PDP da takwaransa Peter Obi na Labour Party sun garzaya gaban Kotun Ƙolin ƙasar don ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wadda ta kori ƙararrakin da suka shigar a kan nasarar zaɓen Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.

    Ayarin alƙalai guda biyar ne a ranar 6 ga watan Satumba, suka yanke hukuncin bai ɗaya na cewa duk 'yan takarar jam'iyyun adawa sun gaza tabbatar da hujjar cewa zaɓen yana cike da kura-kurai.

    Sun ayyana cewa masu ƙorafin ba su iya tabbatar da zarge-zargen aringizon ƙuri'u ba, da take 'yancin masu zaɓe, kuma sun gaza kawo isassun shaidu da za su tabbatar da ƙararrakinsu.

    Da yake ƙalubalantar hukuncin, ɗan takarar PDP Atiku Abubakar ya nemi Kotun Ƙoli ta soke hukuncin kotun zaɓen shugaban ƙasa, inda ya nunar cewa hukuncin da ya tabbatar da nasarar zaɓen Tinubu "cike yake da manyan kura-kurai da kuma rashin adalci".

    Babban ɗan adawar na Najeriya ta hannun lauyansa, ya kuma soki yadda kotun ta yi amfani da "kalaman aibatawa" waɗanda ya ce, "sun nuna fifita wani ɓangare".

    A wani mataki makamancin wannan, Peter Obi na jam'iyyar Labour ya nunar cewa kotun zaɓen shugaban ƙasa ta kawar da kai ga gaskiyar al'amuran da ya gabatar a shari'arsa, kuma ta gaza yin la'akari da girman shaidun da ya gabatar, abin da ya sa ta kai ga hukunci mai cike da kure.

    Lauyoyin masu ƙorafin a ranar Talata sun shigar da sanarwar ɗaukaka ƙararrakinsu a kan dalilai masu yawa, ciki har da batun cewa kamata ya yi Kotun Ƙoli ta jingine hukuncin ƙaramar kotu, wanda ya tabbatar da nasarar Bola Tinubu, kuma ta ayyana cewa bai cancanci tsayawa takarar shugaban ƙasa a Najeriya ba a lokacin da ya yi hakan.

    A cewarsu, bisa hujjar an taɓa kama shi da laifi kan zargin safarar ƙwaya a Amurka.

    Ba a dai sanya wata rana don sauraron shari'o'in ba.

    Kuma har yanzu jam'iyyar APC mai mulki ba ta ce uffan kan wannan sabon mataki ba, mako biyu bayan murnar samun nasara kan hukuncin da ya tabbatar da zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

    • Dalili biyar na korar ƙararrakin Atiku da Obi
  3. Dattijo ɗaya cikin huɗu a duniya na fama da cutar hawan jini - WHO

    ..

    Asalin hoton, SOPA IMAGES

    Rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ranar Talatar kan illar cutar hawan jini a duniya ya nuna cewa kusan hudu daga cikin mutane biyar masu fama da cutar hawan jini a duniya ba su samun isasshen magani.

    Rahoton ya jaddada cewa, idan kasashe za su iya fadada ayyukansu, zai iya magance mace-mace miliyan 76 tsakanin shekarun 2023 zuwa 2050.

    Hawan jini na shafar daya daga cikin dattijai uku a duniya, kuma yana da alaka da manyan matsalolin lafiya kamar shanyewar jiki da ciwon zuciya da gazawar zuciya da lalacewar koda, da dai sauransu.

    Rahoton ya kuma bayyana cewa adadin masu fama da hawan jini, ya nunka daga miliyan 650 a shekarar 1990 zuwa biliyan 1.3 a shekarar 2019.

    Abin mamaki, kusan rabin masu fama da cutar hawan jini a duk duniya ba su san halin da suke ciki ba, kuma sama da kashi uku cikin huɗu na manya masu fama da hawan jini suna rayuwa ne a ƙasashe marasa ƙarfin tattalin arziƙi.

    • Hawan jini a shekarun kuruciya ka iya janyo dimaucewa
    • Ko kun san abubuwan da ke janyo matsalar bugun jini?
  4. Farashin ɗanyen man fetur ya yi tashin da bai taɓa yi ba cikin wata goma

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin man fetur a duniya ya yi tashin da bai taɓa yi ba a cikin watanni goma.

    Farashin gangar ɗanyen mai na Brent ya tashi zuwa sama da dalar Amurka 95 a ranar Talata.

    Tashin farashin ya zo ne bayan rage yawan ɗanyen man fetur da ƙasashe biyu mafiya fitar da man fetur ɗin suka yi, wato Saudiya da kuma Rasha.

    Hukumar kula da makamashi ta duniya ta yi gargadin cewa ɗanyen man zai yi ƙaranci nan da ƙarshen shekara.

    Farashin man fetur ya tashi zuwa dalar Amurka 120 kan kowace ganga bayan mamayen da Rasha ta ƙaddamar kan Ukraine a shekarar da ta wuce, sai dai ya sauko zuwa dalar Amurka 70 a cikin watan Mayu.

    • Kalaman 'yan Najeriya bayan sake ƙara kuɗin man fetur
    • Farashin man fetur ya tashi a duniya bayan rage adadin da Saudiyya ke fitarwa
  5. Ƴan sanda ba su daki Mahsa Amini da sanda ba - Ra'isi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sugaban Iran, Ebrahim Ra'isi ya yi magana a kan mutuwar Mehsa Amini, budurwar da ake zargin ƴan hisba da sanadin rasuwarta a bara.

    Ya ce: "Game da batun yarinyar nan ta shekarar da ta wuce, binciken masana lafiya ya nuna cewa ƴan sanda ba su buge ta ba, to amma ko kafafen yaɗa labaru na ƙasashen yamma sun faɗi hakan?"

    Mr.Ra'isi ya kuma bayyana batun sanya hijabi, da ƴancin ɗan'adam da kuma batun nukiliya a matsayin wata dabara kawai ta kai wa ƙasa mai ƴanci kamar Iran farmaki."

    Ya kuma bayyana Amurka a matsayin "kurkuku mafi girma ga mata" tare da bayyana cewa akwai mata masu yara da dama a cikin kurkuku na Amurka.

    Shugaban na faɗin hakan ne bayan da matashiya Mehsa Amini ta rasu a wurin tsare mutane na jami'an tsaron Iran.

    Masu bincike a Iran sun sanar da cewa ba bugu a kai ba ne ya haddasa mutuwar tata ba.

    Sai dai mahaifin Mehsa ya yi watsi da sakamakon binciken.

    • Iran ta rushe hukumar Hisbah bayan zanga-zanga a kasar
    • Romina Ashrafi: 'Yan sanda sun kama mutumin da ya kashe 'yarsa a Iran
  6. An fara artabu tsakanin sojoji da mayaƙan RSF a birnin Port Sudan

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Faɗa tsakanin bangarori biyu da ke gaba da juna na sojojin Sudan ya bazu zuwa birnin Port Sudan da ke gabar tekun Bahar Rum a karon farko cikin watanni biyar da ak kwashe ana gwabza faɗa.

    Sojojin Sudan sun yi musayar wuta da 'yan kungiyar 'yan tawayen kabilar da ke kiran kanta da dakarun kawancen jam'iyyu da ƙungiyoyin gabashin Sudan.

    Sojojin sun yi ƙokarin kawar da shingayen binciken ababen hawa da kungiyar ta kafa a ranar Litinin a tsakiyar birnin.

    Port Sudan ne ke ƙunshe da filin jirgin sama daya tilo da ke aiki a kasar.

    Birnin kuma shi ne inda wasu jami'an gwamnati da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka koma sakamakon fadan da ake yi a babban birnin kasar, Khartoum, da sauran yankunan kasar.

    Artabu tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tun bayan barkewar rikicin a babban birnin kasar, Khartoum, a cikin watan Afrilu.

    • 'Ba mu da tabbacin abin da zai faru da mu idan muka isa Port Sudan'
    • 'Mu na cikin mawuyacin hali a Sudan'
  7. Yunwa da ƙyanda sun kashe yara 1,200 a Sudan - MDD

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta ce aƙalla yara 1,200 a sansanonin ‘yan gudun hijira a Sudan sun mutu tun a watan Mayu sakamakon ƴunwa da kuma kamuwa da cutar ƙyanda.

    Ta ce wasu dubbai da dama, ciki har da jarirai, na cikin hatsarin mutuwa kafin karshen shekara.

    UNICEF ta ce sama da yara dubu hamsin ne ke bukatar maganin matsalar rashin abinci mai gina jiki mafi muni a kowane wata a Sudan.

    Kuma ta ce yaƙi ya tilastawa wasu cibiyoyin ciyar da abinci rufewa.

    Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce da yawa daga cikin yaran da ke mutuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira sun tsere ne daga yaƙin Sudan ta Kudu da Habasha.

    • Yaron da ke yaƙin ceto 'yan uwansa daga mutuwa saboda tsananin yunwa
    • Tamowa ka iya kashe yara kusan 300,000 a Najeriya a 2021 - UNICEF
  8. Shugabar Peru ta ayyana dokar ta-ɓaci a ƙasar saboda rikicin ƴan daba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar Peru, Dina Boluarte, ta ayyana dokar ta baci a gundumomi biyu a babban birnin kasar Lima da arewacin jihar Piura.

    Wannan na zuwa bayan mummunan tashin hankalin da kungiyoyin 'yan daba suka haddasa.

    Boluarte ta ce gwamnati ta ƙaddamar da bincike kan karuwar hare-hare a Peru, an kuma dauki matakai na musamman da za su bai wa 'yan sanda damar shiga gidajen mutane ba tare da wata shaidar hukuma ba.

    Su ma wasu gundumomi da ke wajen Limada da suka hada da San Huwan-de Luriganko da San Martín de Pores, masu al'umma miliyan 2, an dauki irin wannan matakin.

    A 'yan makwannin nan ana yawan samun hatsaniya da taho mu gama tsakanin kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna.

    Ko a makon jiya an jefa gurneti wani gidan rawa, inda mutum 15 suka mutu.

    • An ayyana dokar ta baci kan mummunar gobarar daji a Koriya Ta Kudu
    • Somalia: An ayyana dokar ta-baci kan farin dango
  9. Tinubu na son ƙarfafa dangantakar Najeriya da Afrika ta kudu

    ...

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tattauna da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, inda ya yi maraba da masana'antun hakar ma'adinai na kasar da su zuba jari a fannin bunkasa ma'adanai na Najeriya.

    An gudanar da tattaunawar ce a ranar Litinin a birnin New York, gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya.

    A cewar wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya ci gaba da yunkurinsa na bunkasa tattalin arziki na diflomasiyya don jawo hankalin masu zuba jari a yayin ganawar.

    "Kamfanonin hakar ma'adinai na Afirka ta Kudu suna da rawar da za su taka a fannin bunkasa ma'adanai a Najeriya," in ji shugaban Najeriyar.

    “Yan kasuwar ku sun kyautata sosai a harkar sadarwa ta Najeriya."

    "Muna da arzikin ma'adinai mai yawa a fadin kasarmu, kuma kuna da kwarewa sosai a wannan fannin."

    "Saboda haka, muna sa ran samar da ayyukan yi da kuma sakamako mai amfani a wannan fanni a matsayinmu na ‘yan’uwan juna.”

    Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu da ta haɗa kai da Najeriya wajen yin kira ga yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin taimaka wa Afirka wajen yaƙar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.

    • 'Za mu kawo wa Najeriya ɗaukin dala biliyan 2.5 don yaƙi yunwa'
    • Shin talauci na raguwa a duniya?
  10. Za a ware wa mata kujeru a majalisar dokokin Indiya

    Narendra Modi

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Indiya ta kai wani kudurin doka gaban majalisar dokokin ƙasar domin ware wasu kujeru a majalisar ga mata.

    Dokar, wadda aka gabatar da ita shekaru 27 da suka wuce, an amince da ita ne a wani zama na musamman a ranar Litinin.

    Firaminista, Narendra Modi ya bayyana kudurin a matsayin wani buri da har yanzu ba a cika ba.

    Ya kuma ce tattaunawa kawai kan cigaban mata bai isa ba.

    Batun ware kujeru ga mata na cikin alƙawurran da jam'iyyar BJP ta yi a zaɓukan shekarun 2014 da 2019.

    • Matan Indiya da ke alfahari da kasancewarsu 'marasa aure'
    • Ko ya dace India ta soke gwamnonin jihohi?
  11. Ko kun san me ake tattaunawa a taron MDD?

  12. Indiya ta kori jami'in diflomasiyyar Canada

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Indiya ta kori wani babban jami'in diflomasiyyar Canada.

    Ma'aikatar harkokin wajen kasar a birnin Delhi ta ce matakin da ta dauka na nuni da abin da ta kira kara nuna damuwa game da tsoma bakin jami'an diflomasiyyar Canada a cikin harkokin cikin gidan Indiya.

    Sanarwar ta zo ne sa'o'i bayan ministan harkokin wajen Canada ya sanar da cewa an kori wani jami'in diflomasiyyar Indiya.

    Rikicin diflomasiyyar da ke kara ta'azzara ya ta'allaka ne kan ikirarin Canada na cewa watakila jami'an gwamnatin Indiya na da hannu a kisan ɗan gwagwarmayar Sikh dan kasar Canada, Hardeep Singh Nijjar, a yankin British Columbia a watan Yunin wannan shekarar.

    Sai dai Indiya ta kira wannan zargin a matsayin wauta.

    Amurka ta nuna matukar damuwa a kan zargin da Canada ke yi wa Indiya kuma ta ce yana da matukar muhimmanci a gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu.

  13. Akwai yiwuwar masu amfani da shafin X (twitter) su fara biyan kuɗi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Mai kamfanin sada zumunta na dandalin X wanda a baya ake kira da Twitter, Elon Musk, ya ce masu amfani da shafin ka iya fara biyan kudi domin amfani da shi.

    Attajirin mai kudin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci wani zauren tattaunawa da firaministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu a jihar California.

    Wakiliyar BBC ta ce Musk ya ce a halin yanzu masu amfani da shafin X za su ci gaba da cin bagas, amma nan gaba batun biya zai ɓullo.

    Tun bayan da ya karbi ikon da kamfanin dai ya ke ta kokarin fito da sabbin matakai da ba ya yi wa ma'aikata da masu amfani da shafin dadi.

    Matakin biyan kudin da alama zai rage wa X mabiya da kuma samun raguwar masu tallace-tallace a ciki.

    • Elon Musk ya sayi Twitter: Wanne sauyi za a samu a kamfanin?
    • Mutum miliyan goma sun yi rijista da dandalin Threads kishiyar Twitter
  14. An koma makarantu a yankunan da girgizar kasa ta afku a Maroko

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Yara sun koma makaranta a garuruwa da ƙauyuka da dama a Moroko bayan mummunar girgizar kasar da ta afku a kasar, kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.

    A wurare kamar Amizmiz da Asni da Taroudant, an ci gaba da ɗaukan darussa tare a cikin tantuna 150 waɗanda aka samu tallafi daga hukumomin yankin na musamman da aka tanadar don koyarwa, a cewar shafin intanet na Lakome mai zaman kansa.

    Kamfanin dillancin labaran kasar MAP ya bayar da rahoton kyakkyawan fata da jajircewa a tsakanin malaman da daliban.

    Bugu da kari, ana jigilar dalibai 6,000 daga yankunan da lamarin ya shafa a El Haouz zuwa makarantu a birnin Marrakesh, kamar yadda gidan talabijin na 2M ya ruwaito.

    • Ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi a Morocco cikin hotuna
    • Malamar da girgizar ƙasa ta halaka dukkanin ɗalibanta a Moroko
  15. Hedikwatar tsaron Najeriya za ta yi bincike kan 'bidiyon ƴan bindiga a Katsina'

    ...

    Asalin hoton, X/@DefenceInfoNG

    Hedikwatar tsaron Najeirya ta ce ta kaddamar da bincike kan wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu da ake zargin sojoji ne suna magana da wasu mutane a kan babura ɗauke da makamai, waɗanda ake tunanin ƴan fashin daji ne.

    Ana zargin cewa, an ɗauki bidiyon ne a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    A cikin bidiyon an ji wani da ba a san ko wane ne ba, na bayyana cewa "an yi sulhu da mutanen kuma za a bar su, su wuce ba tare da an taɓa su ba."

    Wata sanarwa da mai magana da yawun hedikwatar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, hedikwatar ta ce maƙasudin gudanar da binciken shi ne a tabbatar da sahihancin bidiyon da kuma gano sojojin.

    Sanarwar ta ƙara da cewa cibiyar na sane da cewa wasu ‘yan bindigan sun yanke shawarar tuba, kuma suna maraba da su.

    Katsina na cikin jihohin da matsalar ƴan fashin daji ta yi wa katutu.

    Ƴan bindigar kan sace mutane tare da garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, haka kuma sukan tarwatsa ƙauyuka da satar kayan masarufi da dabbobi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin sojoji suna ƙokarin murƙushe masu aikata laifuka a yankuna daban-daban na ƙasar.

    • 'Sai hukumomin tsaro sun haɗa kai a ga bayan matsalar tsaron Najeriya'
    • Mun raba Najeriya da ƴan ta'adda fiye da 800 a wata uku - Sojoji
  16. Canada na zargin Indiya da hannu a kisan wani jagoran Sikh

    ...

    Asalin hoton, SIKH PA

    Bayanan hoto, ...

    Indiya ta mayar da kakkausan martani kan zargin da Canada ke yi mata na yiwuwar hannu a kisan Hardeep Singh Nijjar, wani mai fafutuka dan Canada, mabiyin addinin Sikh.

    A watan Yuni da ya wuce ne aka harbe shi har lahira a wajen wurin bauta a yankin British Columbia.

    Tun da farko, firaministan Canada Justine Trudeau ya yi kira ga India da ta bai wa Canada hadin kai a binciken da take yi na gano musabbabin kisan.

    Trudeau ya kuma ce ya tabo batun a lokacin ganawarsa da takwaransa na India Narendra Modi a taron kasashen G20 da aka yi a baya-bayan nan.

    • Miji da mata da 'yayansu da tsananin sanyi ya kashe a Canada
  17. Masu zanga-zanga na zargin hukumomi kan mummunar ambaliya a Libya

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Daruruwan mazauna birnin Derna da ke gabashin Libya a ranar Litinin sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da hukumomin yankin, fiye da mako guda bayan ambaliyar ruwa ta kashe dubban mutane a birnin.

    Masu zanga-zangar sun soki shugaban majalisar dokokin gabashin ƙasar, Aguila Saleh, da hukumomin, inda suka dora alhakin ambaliyar da ta kashe kusan mutum 4,000, a cewar alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya.

    A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, masu zanga-zangar sun ce suna son a gaggauta gudanar da bincike kan ambaliyar ruwan da kuma daukar matakin shari'a kan shugabannin da ke da hannu.

    Sun kuma buƙaci a biya su diyya da sake gina Derna.

    Masana sun kuma bayyana cewa rashin kula da madatsun ruwa na birnin da hukumomi suka yi ne ya sa suka fashe tare da fitar da ruwa.

    Masu zanga-zangar sun kuma kona gidan magajin garin Derna, Abdulmenam al-Ghaithi.

    Tuni dai Firaministan Libiya Osama Hammad ya dakatar da Mista Ghaithi tare da wasu jami'an karamar hukumar Derna.

    • Ambaliyar Libya: Gawawwakin da ba a iya gane su ba saboda bala'i
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'
  18. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar Talata.

    Aisha Babangida da Zulaiha Abubakar ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.