Atiku ya ɗaukaka ƙara kan zaɓen Tinubu zuwa Kotun Ƙoli

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Cutar mashaƙo ta kashe mutum 487 a jihar Kano

    Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun ce akalla mutum 487 ne suka mutu sakamakon cutar mashaƙo da ta ɓarke a jihar.

    Kwamishinan lafiya na jihar Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.

    Ya ce "an fara samun wannan cuta ne tun a watan Disamban 2022, kimanin wata 10 kenan.

    "An yi ta samun mace-mace a nan da can cikin waɗannan watanni, kuma shi ne ya kai adadin waɗanda suka mutu zuwa 487 cikin watanni. Sai dai an samu raguwar mace-mace a 'yan kwanakin nan," in ji Kwamishinan.

    Mutanen da ake da su a yanzu a asibiti da ke kwance sanadin wannan cuta, ba su fi ɗari da goma ba, wani abu da ke nuni da raguwar cutar in ji shi.

    Ƙungiyar ba da agaji ta likitocin ta MSF ta wallafa wata sanarwa a shafinta na intanet, inda ta ce a birnin Maiduguri na jihar Borno, sai da ta ƙara gadajen kwanciya ashirin a ƙaramin asibitin yara na Gwande 111, inda yara 110 ke samun kulawa daga kungiyar tun daga watan Janairun wannan shekarar.

    A jihar Bauchi kuwa MSF ta ce tana kula da yara 21.

    A shekarar 2021 kadai yara miliyan 25 ‘ne ba a yi wa rigakafin ba sam sam ko kuma ba a kai ga kammala musu ba a kasar.

  2. Sai da safe!

    A nan muka kawo ƙarshen rahotanni da labaran da muka kawo muku tsawon wannan wuni. Sai kuma gobe Laraba, idan Allah ya kai mu, za mu dawo don ci gaba daga inda muka sa aya.

    Amma, kuna iya shiga shafin don ci gaba da karanta labaran da muka sanya muku. Mukhtari Adamu Bawa ke cewa sai da safe!

  3. Barca ta caskara Royal Antwerp a Champions League

  4. Ba za mu lamunci tada zaune-tsaye kan shari'ar zaɓen Kano ba - 'Yan sanda

    Police

    Asalin hoton, Kano Police

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gudanar da wani sintirin a sassan birnin Kano don nuna ƙarfin da take da shi wajen tunkarar abin da ta kira "kowacce irin barazana".

    An ga kwambar motocin haɗin gwiwar jami'an tsaro da suka haɗar da 'yan sanda da sojoji da kuma sauran jami'ai masu kayan sarki yayin wannan sintiri da suka zagaya sassan birnin kasuwancin.

    Jami'an dai na wannan shiri ne da kuma jan kunne a ranar jajiberen hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano, za ta yanke a ranar Laraba.

    Kwamishinan 'yan sandan jihar Hussain Muhammad Gumel ya shaida wa BBC cewa sun yi tsare-tsare don tabbatar da ganin ba a samu asarar rai ko dukiya ko kuma cin zarafin wani mutum ba, bayan sanar da hukuncin kotun.

    "Dangane da bayyana wannan hukunci, ko da ta yi daɗi gare shi, ko ba ta yi daɗi gare shi ba".

    Ya ce jami'an tsaro za su tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a ciki da wajen harabar kotun da za ta yi wannan hukunci. CP Hussain Gumel ya ce duk mutumin da zai shiga kotun, sai 'yan sanda sun tantance shi, sannan an caje shi lokacin da ya je domin halartar zaman yanke hukuncin.

    Police

    Asalin hoton, Kano Police

    Police

    Asalin hoton, Kano Police

    Police

    Asalin hoton, Kano Police

    Rundunar ta ce tuni ta tura isassun jami'an tsaro da kayan aiki zuwa wuraren da ta shaida a matsayin muhimmai a Kano don tabbatar da tsaron rayuka da na dukiya, a ƙoƙarin wargaza duk wani yunƙuri na kawo hargitsi da karya doka da oda.

    'Yan sandan sun kuma fitar da jerin shawarwari ga mazaunan jihar ciki har da:

    - Gujewa taro ko shiga duk wani taron masu haddasa tarzoma ko jerin gwano ko zanga-zanga da murnar da za ta iya haddasa rikici.

    - Sai mutanen da ke da cikakken katin shaida ne za a bai wa damar shiga harabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Kano.

    - Kyamarori da wayoyi da duk wata na'urar aika bayanai game da hukuncin na iya zama raina kotu, kuma za a hukunta waɗanda suka take wannan umarni, in ji 'yan sanda

    - Furta kalamai ba tare da linzami ba na iya haddasa tunzurin babu gaira babu dalili, ko kuma yin zagon ƙasa ga harkokin tsaro da kuma mutuncin kotu.

  5. An kashe 'yan sanda biyar a wani harin 'yan bindiga cikin jihar Imo

    Nigerian Police

    Asalin hoton, Nigerian Police/Facebook

    'Yan sanda a Najeriya sun ce an kashe jami'ansu guda biyar a wani hari da aka kai cikin jihar Imo a kudu maso gabashin ƙasar.

    'Yan a-ware a yankin suna kai hare-hare lokaci-lokaci inda suke far wa gine-ginen 'yan sanda da na gwamnati.

    Hukumomi dai na ɗora alhakin akasarin hare-haren da ake kai wa kan ƙungiyar IPOB da aka haramta. Amma dai ƙungiyar ba ta ce uffan ba.

    Ƙungiyar IPOB na fafutukar ganin al'ummar Igbo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun samu ƙasa mai 'yancin cin gashin kanta.

    Rahotanni sun ce aƙalla mutum takwas aka kashe a tarzomar baya-bayan nan da ta ɓarke ciki har da sojoji da jami'an sibil defes.

  6. 'Bai kamata a yarda da mugu ba - kuma ku tambayi Prigozhin' - Zelensky

    Yayin jawabinsa a gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Volodymir Zelensky ya yi bayani game da shirin zaman lafiya, wanda ya ce zai iya kawo ƙarshen yaƙin ƙasarsa da Rasha.

    Akwai wani taron ƙoli na zaman lafiya da ake shiryawa, in ji shi, kuma ya nemi masu sauraron jawabinsa su halarta da zarar an tabbatar da shi.

    Ya ce kamata ya yi a tattauna batun haɗin kai a fili, amma ba a asirce cikin ɗaki ba.

    "Bai kamata a yarda da mugu ba, kuma ku tambayi Prigozhin," Zelensky ya ce, yana buga misali ne da tsohon shugaban ƙungiyar sojojin haya ta Wagner, da ya ƙaddamar da bore sojoji a kan Shugaba Putin amma ya mutu daga bisani bayan wata biyu, a wani hatsarin jirgin sama.

    Zelensky ya kammala jawabinsa da fatan cewa yaƙin Rasha zai kasance na ƙarshe ga al'ummar duniya, yana cewa "Slava Ukraini" lokacin da yake barin kan mumbari.

  7. Kotu ta ba da belin 'yan Najeriyan da ake zargi da halartar auren 'yan luwaɗi

    court symbol

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Najeriya ta ba da belin mutum 69 waɗanda aka kama a cikin watan jiya bayan wani samame kan abin da 'yan sanda suka bayyana da bikin auren 'yan luwaɗi.

    Kamar sauran ƙasashen Afirka da dama, akasarin mutane a Najeriya na kallon luwaɗi da maɗigo a matsayin gurɓacewar tarbiyya.

    Ƙasar tana da tsauraran dokoki a kan auren jinsi.

    Wani lauyan mutanen da ake ƙra ya ce waɗanda yake karewa za a sake su a matsayin beli amma sai sun ajiye kuɗi kimanin N500,000 kowannensu.

    A watan jiya ne, 'yan sanda suka kama mutanen bayan wani samame a wani otel da ke birnin Warri sakamakon tsegunta musu rahoto game da wnai auren 'yan luwaɗi.

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Human Rights Watch ta soki lamirin 'yan sandan Najeriya saboda holin mutanen da ake zargi a bainar jama'a gaban 'yan jarida, tare da titsiye su kan zarge-zargen da ake yi musu.

    Najeriya ta kafa doka wadda ta haramta duk wata mu'amala ta 'yan luwaɗi, kuma ana iya ɗaure wanda aka kafa laifi tsawon sama da shekara 10 zuwa shekara 14 a gidan yari.

    • Yadda aka yi wa ɗan luwadi rukiyya don sauya daɓi’arsa
  8. Zelenski ya gabatar da jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

    Zelenski

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymir Zelensky ya gabatar da jawabinsa a yayin Babban Taron Babban Zauren majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya taɓo batutuwan da suka shafi yaƙin nukiliya.

    Ya ce ƙarni na 20 ya koya mana hankali cewa kada mu yi amfani da makaman ƙare dangi, kuma mu tabbatar da cikakken aiki da yarjejeniyar kwance ɗamarar makaman nukiliya.

    Sai dai Rasha har yanzu tana da kayan haɗa makaman nukiliya duk da yake "ba ta da iko" ta ci gaba da mallakar makaman nukiliya, in ji shi.

    Ya ce akwai yarjeniyoyin da suka hana mallakar irin waɗannan makamai, amma babu wani tarnaƙi na zahiri a kan mayar da kayayyaki kamar abinci makaman yaƙi.

    "Tun lokacin da aka fara yaƙin nan gadan-gadan, Rasha ta datse tashoshin ruwan Ukraine," in ji shi. "Tashoshin ruwanmu na Kogin Danube har yanzu suna fuskantar hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa."

    A cewar Zelensky Rasha na amfani da harkokin samar da abinci don matsa lamba ga sauran ƙasashe a kan su amince da yankunan Ukraine da ke ƙarƙashin mamaya a matsayin na Rasha, kuma ya yaba ƙasashen da ke sayen hatsin Ukraine don nuna bijirewa ga irin wannan ƙoƙari.

    Ya ce a baya, ƙungiyoyin 'yan ta'adda sun sace ƙananan yara amma a yaƙin Ukraine, sacewa da iza ƙeyar ƙananan yaran Ukraine zuwa Rasha, na cikin manufar gwamnatin Putin, abin da ba a taɓa gani ba a shekarun baya.

    "Akwai dubun dubatar ƙananan yara da muka sani Rasha ta sace," a cewar Zelensky kuma "muna ƙoƙarin ganin mun dawo da yaranmu gida, amma dai lokaci yana tafiya. Me zai faru da su?"

    "Waɗannan ƙananan yara da ke Rasha ana koya musu ƙiyayyar Ukraine, kuma ana tsinke duk wata igiyar alaƙa tsakaninsu da iyayensu. Wannan ƙarara, wani nau'in kisan ƙare dangi ne," ya ce.

  9. AC Milan da Newcastle sun tashi ba ci a Champions League

  10. Taliban ta naɗa malamin sunni a matsayin shugaba a yankin mabiya Shi'a

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban gwamnatin Taliban, Hebatullah Akhundzadeh, ya sanar da naɗa mambobin majalisar malamai a yankunan Bamyan da Daikundi da Sarpol da Maidan Wardak da Ghor da kuma Nuristan.

    A cewar wani mazaunin lardin Bamyan wanda mafiya yawan mazaunansa 'yan Shi'a ne, ba a sanya ko sunan malami guda ba daga malaman shi'ar da ke yankin.

    Mambobin mabiya Shi'a na da yawa a waɗan nan yankuna masu yawa.

    Ƙungiyar Malamai na daga cikin waɗanda ake tuntuba kuma suna taka rawa mai yawa sannan kuma akwai mazauninsu a tsarin gwamnatin Taliban.

    Cikin wata sanarwa da Zabihullah Mujahid, kakakin gwamnatin Taliban ya fitar ta ce ana shawartar al'umma su yi biyayya ga dukkan abin da ƙungiyar Malamai ta sharuɗanta.

    Wani da ya nemi a sakaya sunansa daga Bamyan ya shaida wa BBC cewa asalin jerin sunayen da aka aika daga Kandahar akwai sunayen malaman shi'a ciki, saboda yankunan cike cike da mabiya Shi'a da dama.

    Wata majiyar ta a lardin Daikundi ta shaida wa BBC cewa "kimanin wata huɗu baya, an raba wa malaman Shi'a 25 wani fom sannan aka bai wa na Sunni 15 suma su gudanar da zaɓe tsakaninsu sannan su aika sakamakon zuwa shugaban Taliban.

    "Cikin sunayen akwai malamai 25 na Shi'a. Amma cikin sanarwar da Hebatullah Akhundzadeh ya fitar sai muka ga babu na Shi'a ko ɗaya."

    h

    Asalin hoton, Authorities

  11. Ana nuna damuwa kan ƙarin 'yan matan da ke yin ciki a arewacin Mozambique

    Pregnancy

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da rabi na 'yan mata tsakanin shekara 15 zuwa 19 a yankin Cabo Delgado mai fama da rikici na ƙasar Mozambique sun samu juna biyu, a cewar wani nazari daga Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasar.

    Mazauna lardin na zaune ne cikin wani yanayi na taɓarɓarewar tsaro a yankin mai arziƙin man fetur da iskar gas da kuma dutsen ruby mai daraja.

    Yankin dai yana cikin shekararsa ta shida da rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya na masu iƙirarin jihadi.

    Rikicin ya tilasta wa mutane fiye da rabin miliyan tserewa daga gidajensu, wasu 4,000 sun riga mu gidan gaskiya, sannan an lalata makarantu kusan 200.

    A baya, daraktan ilmi na Cabo Delgado, Ivaldo Quincardete ya taɓa hana 'yan mata masu juna biyu zuwa makaranta amma ya ce daga baya an canza matakin yayain da ake nuna damuwa game da matsayin ilmin al'ummar yankin.

    Kimanin kashi 70 cikin 100 na matan lardin ba za su iya rubutu ko karatu ba.

    Ya ce alƙaluman baya-bayan nan, abin damuwa ne kuma "wata manuniya ce ta babban ƙalubalen da ke fuskantar lardin".

  12. Kotu ta yi wa masanin haɗa magunguna ɗaurin rai-da-rai bisa laifin fyaɗe a Abuja

    Hukumar yaƙi da fasa-ƙwaurin bil'adama ta Najeriya (NAPTIP), ta ce ta yi nasarar tabbatar da hukunci a kan wani masanin haɗa magunguna, Abubakar Danraka, wanda kotu ta yi wa ɗaurin rai-da-rai saboda laifin aikata fyaɗe.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta ranar Talata ta ce wata babbar kotun tarayya da ke unguwar Kubwa ce ta samu Abubakar Ɗanraka da laifi kuma ta yanke masa hukuncin rai-da-rai a gidan yari.

    Sanarwar ta ambato jami'in yaɗa labaran hukumar Mista Vincent Adekoye na cewa kotun Mai shari'a A. Akanbi-Yusuf ta yanke wa wanda aka yi ƙara hukuncin ne, bayan masu shigar da ƙara sun yi nasara tabbatar da hujjoji na yankan shakku.

    A ranar 9 ga watan Agustan 2021 ne aka tuhumi mai laifin a gaban kotu,bayan tun farko ya musanta zargin da aka yi masa.

    Sanarwar NAPTIP ta ce mai laifin, tsohon babban jami'in magunguna ne a Asibitin Ƙasa na Abuja, kuma an tuhume shi da laifin fyaɗe.

    Ta ce a ranar 27 ga watan Maris ne aka kama mai laifin, bisa zargin lalata wata ƙaramar yarinya.

    Hukumar ta zargi Abubakar Ɗanraka da yaudarar yarinyar zuwa ɗakinsa, inda ya neme ta, ta dubura bayan ya gauraya ƙwaya cikin abin shan da ya ba ta.

    Hukuncin, ya kawo ƙarshen shari'a mai cike da taƙaddama, da aka shafe tsawon shekara uku ana tafkawa.

    Sanarwar dai ta kuma ambato babbar daraktar hukumar NAPTIP, Farfesa Fatma Waziri-Azi, tana yaba wa hukuncin, wadda ta ce zai kasance izina ga masu yunƙurin aikata irin wannan laifi.

    • Ana kokarin gano wadanda suka yi wa yarinya fyade 'ta dubura' kuma suka kashe ta a Kaduna
  13. Ƙungiyar G7 ta nemi China ta matsawa Rasha ta fice daga Ukraine

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, Ƙungiyar G7 ta ƙasashe mafiya arziƙi a duniya ta nemi China ta matsawa Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine.

    Sanarwar ta ce tana fatan mambobin ƙungiyar za ci gaba da neman gwamnatin China ta matsawa Rasha da tasirin da ke tsakaninsu, domin ta gaggauta ficewa daga Ukraine ɗin ba tare da wasu sharuɗa ba.

    A gefe ɗaya kuma ana sa ran gwamnatin China za ta duba wannan roƙo kuma ta kalle shi da idon basira.

    Ministan harkokin wajen China Wang Yi ya tafi Rasha a wata ziyara ta kwanaki huɗu domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu.

    Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar sun fitar da sanarwar ne a ƙarshen wata tattaunawa da suka yi a gefen babban taron zauren MDD.

  14. Atiku ya ɗaukaka ƙara kan zaɓen Tinubu zuwa Kotun Ƙoli

  15. Ambaliyar Libya: Hukumomi a Derna sun ce duk 'ya jaridan su fice daga birnin

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Wani ministan a gwamnatin birnin Derna da ke gabashin Libya, ya ce duk 'yan jarida su fice daga birnin, wanda ambaliya ta ɗaiɗaita.

    Ministan sufurin jiragen sama na fasinja, Hisham Abu Shekiwat ya zargi kafafen yaɗa labarai da haifar da koma-baya ga aikin ceto da ake yi a birnin wanda ambaliya ta shafa a makon jiya.

    A ranar Litinin, masu zanga-zanga suka cinna wuta a gidan hamɓararren magajin garin.

    Wasu na cewa masifar da ta faru wadda manyan madatsun ruwa biyu suka fashe dalilin wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, abu ne da za a iya kaucewa.

    Jami'ai sun yarda da cewa masu gina madatsun ruwan ba su yi aikinsu na kula da shi ba.

  16. Maguire da Mount da Varane ba za su buga wasan Bayern ba

  17. An maka ƙarar iyayen wani riƙaƙƙen ɗan kirifto a kotu

    An kai ƙarar mahaifan mutumin da ya kafa kamfanin kirifto na FTX, Sam Bankman-Fried saboda asarar da karyewar kamfaninsa ta haddasa wa masu zuba jari.

    A cikin wata takardar ƙara, manajojin kamfanin da ya karye sun zargi dattijan da mallakar miliyoyin daloli "na kuɗi ta hanyar damfara" da kawar da kai ga abubuwan da aka riƙa aikatawa na ba daidai ba a kamfanin.

    An shigar da shari'ar ne a madadin miliyoyin abokan hulɗar kamfanin FTX, da suka yi asarar kuɗaɗensu lokacin da ya karye a bara.

    Karyewar kamfanin ta janyo kama Mista Sam Bankman-Fried.

    Masu shigar da ƙara na Amurka sun zargi tsohon biloniyan wanda a baya ake yi wa laƙabin "Sarkin Masu Kuɗin Kirifto", da aika miliyoyin kuɗi ta haramtacciyar hanya daga kamfanin musayar kuɗin don yin rufa-rufa kan asarar da yake tafkawa da bayar da gudunmawar kuɗi ga 'yan siyasa da kuma sayen kadarori.

    Ya dai musanta duk tuhume-tuhumen da ake yi masa, amma dai yana tsare a gidan yari, inda yake zaman jiran shari'a a watan gobe.

    Parents of a FTX crypto

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Barbara Fried da Joseph Bankman

    Lauyoyin mahaifansa sun ce iƙirarin da ake yi a kansu "gaba ɗaya ƙarairayi ne" kuma an tsara su ne don gurgunta damar da ɗansu ke da ita wajen samun nasara a shari'arsa.

    Ƙarar, wadda aka shigar a wani ɓangare na shari'ar karyewar arziƙin kamfanin, ta ce mahaifan Bankman-Fried - waɗanda dukkansu farfesoshi ne a Jami'ar Stanford a lokacin - sun yi amfani da "dama da tasirinsu a kamfanin FTX wajen azurta kawunansu kai tsaye da kuma a kaikace, da miliyoyin daloli".

    Sun karɓi kyautar dala miliyan goma tsaba daga wani asusu mallakar Alameda, abokin ƙawancen FTX, yayin da kamfanin FTX kuma ya ba su kadarar dala miliyan 16.4 a Bahamas, cewar takardun kotu.

    • An kama mai kamfanin Crypto na FTX a ƙasar Bahamas
  18. Lamura na cikin hatsari saboda taɓarɓarewar alaƙa tsakanin India da Canada

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Rashin tabbas na ƙaruwa tsakanin ƙasashen biyu, bayan da Canada ta zargi India da kashe wani ɗan gwagwarmaya mabiyin addinin Sikh, Sigh Nijjar.

    Wannan lamari dai zai iya shafar alaƙar ƙasashen biyu ta kasuwanci.

    A ranar Litinin ne, Firaiministan Canada Justin Tredeau ya zargi gwamnatin inda da hannu kan kisan Hardeep Singh Nijjar.

    Bayan haka Canada ta kori jakadan India a ƙasarta. A wani mataki na ramuwa ita ma India ta kora jakadan Canadan gida a ranar Talata.

    India ta yi watsi da wannan zargi kuma ta ce Canada ta ɗauki mataki kan mutanen da ke ƙin India a ƙasarsa.

    Alaƙar abubuwa da dama da ke tsakanin ƙasashen biyu na ciki haɗari saboda taɓarɓarewar alaƙarsu.

    g

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Empoli ta kori kociyanta Paolo Zanetti

  20. Biden ya nemi ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya su tashi tsaye a kan Rasha

    UN General Assembly

    Asalin hoton, REUTERS

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga ƙasashen Majalisar Ɗinkin Duniya da cewa jazaman ne su tashi tsaye a kan abin da ya bayyana da "tsabagen takalar faɗa" daga Rasha.

    A cewarsa, tabbatar da 'yancin cin gashin kai na kowacce ƙasa da kare haƙƙin ɗan'adam jigo ne na tanade-tanaden da ke cikin daftarin Majalisar ƙasashen duniyan.

    Joe Biden yana wannan jawabi ne a wani ɓangare na Babban Taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na shekara-shekara a birnin New York.

    A cikin shekara ta biyu a jere, ya ce, wannan taro ya yi duhu sakamakon inuwar wannan yaƙi, wanda Rasha ta haddasa ba tare da an takale ta ba.

    “Rasha ta yi imanin cewa duniya za ta nuna gajiyawa, kuma duniya za ta bari Rasha ta zalunci Ukraine, ba da tare da sakayya ba.

    Amma ina roƙonku wannan:

    Idan muka bar waɗannan jiga-jigan aƙidoji na Daftarin Majalisar Ɗinki Duniya don lallaɓa mai takalar faɗa, shin wata ƙasa, wakiliyar wannan majalisa za ta samu ƙwarin gwiwar cewa tana da tabbataccen tsaro?

    Idan muka bari aka yanki sashen ƙasar Ukraine, ko 'yancin kowacce ƙasa, zai tabbata cikin tsaro?

    Biden ya ce a'a.

    “Hakan ce ta sa Amurka da abokan ƙawancenmu a faɗin duniya za su ci gaba da mara baya ga mutanen Ukraine masu jarumta a lokacin da suke kare 'yancin cin gashin kai da mutuncin iyakokin ƙasarsu - da kuma 'yancinsu."