Najeriya ta fi samun ci gaban tattalin arziƙi lokacin Obasanjo - El Rufa'i

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Gane Mini Hanya: Rawar da matasa za su taka a fagen mulki

    Burin kowace al`umma shi ne ta gina matasa a fannoni daban-daban na rayuwa domin su kasance manyan gobe.

    Sai dai a fannin mulki, musamman a kasashen nahiyar Afirka, ciki har da Najeriya, za a iya cewa an samu akasi.

    Shin me ke yin cikas ga matasa a harkar siyasa, kuma ta wace hanya za a shawo kan matsalar?

    A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da Farfesa Jibrin Ibrahimy, masanin harkokin siyasa a shiyyar Afirka ta yamma.

    Shehin malamin ya fara ne da bayani a kan fa`idar shigar da matasa a cikin harkar mulki

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  2. BUA zai rage kudin sumunti bayan ganawa da Tinubu

    s

    Asalin hoton, Others

    Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya ce kamfaninsa zai rage farashin sumunti zuwa naira 3,500 a Najeriya.

    Abdul-Samad Rabiu ya bayyana haka ne ga manema labarai a fadar shugaban Najeriya, jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu ranar Juma'a da maraice.

    Ya ce ya dauki matakin rage farashin sumuntin ne a wani bangare na mara wa gwamnatin kasar baya wajen daidaita farashin muhimman kayayyaki a kasar

    Abdul-Samad Rabiu ya kuma ce kamfaninsa zai kara gina wasu sabbin kamfanonin sarrafa sumunti biyu a karshen shekara ko farkon shekara mai zuwa.

    Ya ce kamfanonin wadanda shugaban kasar zai kaddamar idan sun kammala, za su sanya kamfanin ya rika samar da metric tan miliyan 17 na sumunti.

    A cewarsa hakan zai sa kamafnin ya rage farashin sumunti zuwa naira 3,500 a kowane buhu.

  3. Faransa ta ce an yi garkuwa da jakadanta a Nijar

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce an yi garkuwa da jakadan kasar a Nijar a ofishin diplomasiyyar Faransa da ke birnin Yamai.

    Mista Macron ya shaida wa manema labarai cewa halin da jakadan ke ciki abin damuwa ne.

    Ya kuma ce sojojin na Nijar sun takura wa jami'an diplomasiyyar da ke zama a kusa da sansaninsu.

    Tun cikin watan Agustan da ya wuce ne sojojin da suka hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, suka bukaci jakadan na Faransa a Nijar ya fice daga kasar.

    Bukatar da hukumomin Faransan suka yi fatali da ita, domin a cewarsu Shugaba Bazoum ne kadai ke ida ikon yin hakan saboda shi ne halastaccen shugaban kasa.

    A wani labarin na daban kuma sojojin na Nijar sun bukaci dakarun Faransa 1,500 da ke kasar, da su fice daga kasar, bukatar da ita ma Faransa ta yi watsi da ita.

  4. An fara taron kungiyar G-77 ta kasashe masu tasowa

    h

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Taron kungiyar G-77

    An bude taron kasashe masu tasowa da aka yi wa lakabi da G-77 a birnin Havana na kasar Cuba.

    Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres ne ya bude taron na kwanaki biyu.

    Shugabannin kasashen Afirka fiye da 30 da na yankin Latin da Asiya ne ke halartar taron.

    A jawabinsa na bude taron Mista Gutteres ya ce duniya ta gaza a kan kasashe masu tasowa, ya kuma jinjina wa kungiyar bisa kokarinta na tallafa wa mambobinta,

    Gutteres ya kara jadda muhimmancin hada karfi waje guda domin magance matsalar sauyin yanayi.

    G-77 dai babbar kungiya ce a Majalisar Dinkin Duniya, wadda ke kunshe da mambobi 134.

    Duk da kasancewarta ba mambar kungiyar ba, kasar China na halartar taron na wannan shekara.

  5. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da wannan safiya ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo irin wainar da ake toyawa a fadin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.