Dubai ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. 'Putin na son a warware matsalar Nijar'

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban soji na kasar Mali Kanal Assimi Goïta ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin.

    A yayin zantawarsu, shugabannin biyu sun jaddada buƙatar masalaha a siyasance game da rikicin siyasar Nijar, bayan juyin mulkin da ya hambarar da Shugaba Mohammed Bazoum daga kan mulki a watan Yuli.

    Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun yi gargaɗi kan tsoma bakin ƙasashen waje a ƙoƙarin mayar da shugaba Bazoum kan iko, kamar yadda Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) ta ba da shawarar ɗaukar matakin soja a matsayin zaɓin kawo ƙarshen juyin mulkin.

    Sojojin Mali sun bayyana aniyarsu ta tallafa wa Nijar, matuƙar wasu ƙasashen waje suka kutsa kai cikin ƙasar, sannan za su ƙulla alaka mai ƙarfi da Rasha, ciki har da alaƙar ayyukan sojojin hayar Wagner da ke samun goyon bayan fadar Kremlin.

    Shugaba Putin dai ya jajanta wa Kanal Goïta game da harin ta'addanci da aka kai arewa maso gabashin Mali wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 100.

    Fadar Kremlin ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa, shugabannin biyu sun tattauna a kan matakai masu amfani na inganta ayyukan hadin gwiwa tsakanin Rasha da Mali a fannoni daban-daban da suka hada da kasuwanci da tattalin arziki da jin ƙai da yaƙi da ta'addanci.

    Bugu da ƙari, Kanal Goïta ya nuna godiya ga shugaba Putin a kan goyon bayan da Rasha ta bai wa ƙasarsa lokacin ƙuri'ar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa a kan janye takunkumin da ƙasashen duniya suka ƙaƙaba wa Mali.

    Tun da farko a zaman Kwamitin Sulhun, Rasha ta ƙi amincewa da ƙudurin mayar da takunkumin da aka ƙaƙaba wa Mali tare da tsawaita wa'adin ƙwararrun masu sa-ido a kan cin zarafin da ƙungiyoyi masu dauke da makamai da jami'an tsaro ke yi a Mali.

    • Shin Ecowas ta fara ba da kai ga sojojin Nijar ne?
    • Masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar Nijar
  2. Ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi a Morocco cikin hotuna

  3. Najeriya na buƙatar gida miliyan 28 don cike giɓinmu - Kashim Shettima

    Nigeria's VP

    Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA/FACEBOOK

    Najeriya na buƙatar naira tirliyan 21 don cike giɓin da take da shi a ɓangaren gidaje, duk da ƙoƙarin matakan gwamnati uku.

    Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana haka a Sokoto, lokacin ƙaddamar da bikin gina rukunin gidaje guda 500 da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Kashim Shettima na yaba wa Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto, saboda ƙoƙarinsa wajen magance buƙatun gidaje a tsakanin al'ummar jihar, ya ma nunar da cewa giɓin gidajen da ake da shi a Najeriya, wani babban ƙalubale ne.

    ”Najeriya na da giɓin gida miliyan 28 kuma za mu buƙaci naira tirliyan 21 don cimma buƙatun gidajen da muke da su. Wannan mataki da gwamna ya faro, babban abin yabawa ne kuma ya cancanci koyi daga sauran gwamnatocin jihohi.

    Tun da farko, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Sokoto na gina rukunin gidajen ne saboda ma'aikata, kuma za a sayar musu da su ne da zarar an kammala aikin a kan tsarin ɗan haya ya mallaka.

    • Kwana 100 na mulkin Bola Tinubu
    • Ko yaya yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ya kasance a jihohin Najeriya?
  4. Hotunan ɓarna da tashin hankalin da girgizar ƙasar Moroko ta haddasa a Tafeghaghte

    Girgizar kasar Moroko ta kusan shafe karamin kauyen Tafeghaghte gaba daya inda ta kashe kusan rabin mazaunanta 200.

    Daya wan mutanen kauyen ko dai suna asibiti ko kuma sun mutu kamar yadda wani dan yankin ya shaida wa BBC.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Aƙalla mutum 90 ne suka mutu a garin Tafeghaghte
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wata mata ta fashe da kuka bayan ta samu labarin mutuwar 'yan uwanta
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mutane da dama suna ta ƙoƙarin neman ƴan uwan su
  5. Luis Rubiales ya yi murabus bayan sumbatar ƴar kwallon da ta janyo ce-ce-ku-ce

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Luis Rubiales ya yi murabus daga muƙamin shugabancin hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya, bayan ya sha suka saboda sumbatar ƴar wasan ƙasar, Jenni Hermoso lokacin wasan ƙarshe na Gasar cin Kofin Duniya na Mata.

    Hermoso, mai shekara 33, ta ce sumbatar da ya yi mata bayan doke takwarorinsu na Ingila, ba da yardarta ba ne, kuma ta shigar da ƙara a ranar Talatar da ta gabata.

    Rubiales ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa ya miƙa takardar murabus ga muƙaddashin shugaban gwamnatin tarayya, Pedro Rocha inda ya ce ba zai iya ci gaba da aikinsa ba.

    Ya kuma yi murabus daga muƙaminsa na mataimakin shugaban kwamitin zartarwa na UEFA.

    Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce cikin harkokin ƙwallon ƙafa na Sifaniya a makonnin baya-bayan nan, kuma ya shafi gasar cin kofin duniya da ƙasar ta lashe, lamarin da har ya kai ga gurfanar da Rubiales a gaban kotu

    Rubiales dai ya yi iƙirarin cewa da yardar Hermoso, ya sumbace ta, kuma ita ma ta yi masa.

    • Rubiales ya ƙi ajiye aikinsa kan sumbatar 'yar wasa
    • FIFA za ta binciki Rubiales kan sumbatar 'yar wasa
  6. Ana ƙoƙarin gano gawarwakin mutanen da suka kife a kwale-kwale a jihar Neja

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a jihar Neja na ci gaba da gudanar da bincike kan sauran gawarwakin da ake tsammanin har yanzu suna cikin ruwan da wani kwale-kwale ya kife a ranar Lahadi.

    Haɗarin ya faru ne a yankin Gbajibo na Ƙaramar Hukumar Mokwa a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

    Malam Jibrin Abdullahi Murege shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Mokwa wanda ya ce ya zuwa yanzu mutum 26 sun mutu, yayin da aka ceto sama da mutum 40, cikin kimanin mutum 100 da ke cikin jirgin.

    Mahukunta sun ce mata manoma da yara ƙanana ne kawai a cikin jirgin, kuma suna ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da an gano yawan adadin mutanen da rahotanni suka ce suna cikin jirgin.

    Haɗarin jirgin ya faru ne sakamakon wani ice da jirgin ya daka a tsakiyar ruwa, wanda mahukunta suka ce an yanke shi ne a baya amma damuna ta sa ya ƙara toho kuma ba a iya ganinsa.

    Kifewar jirgin ruwa a jihar Neja ba baƙon abu ba ne, ko wata uku baya sai da aka samu irin wannan kifewar jirgi mai ɗauke da mutane sama da 100 da suke kan hanyarsu ta dawowa daga gidan biki.

    A wani labarin mai kama da wannan, wani jirgin ruwan ya kife a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ɗauke da mutum 23 a ranar Juma'a.

    Rahotanni sun ce mutum 15 sun mutu waɗanda yawancin su manoma ne da 'yan kasuwa da ke tare da ƙananan yara.

    Haɗarin ya faru ne a kan hanyarsu ta zuwa birnin Yola daga ƙauyen Rugange da ke Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu.

    An gano gawarwaki huɗu a lokacin da abin ya faru, sanadin masu aikin ceto da kuma masu ninƙaya na gargajiya.

    Wani wanda abin ya faru a kan idanunsa ya ce, wata iska ce mai ƙarfi ta janyo faɗuwar jirgin.

    • Mahaifiyar da ta rasa 'ya'ya uku a jirgin da ya nutse da 'yan biki a Kwara
  7. Masar ta fusata yayin da Habasha ta cika madatsar ruwa ta kogin Nilu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ƙasar Masar ta fusata kan sanarwar da Habasha ta yi, na cigaba da cike kogin Nilu da kasashen biyu ke tada jijiyar wuya akai.

    Ma'aikatar cikin gida a Masar ta ce maƙociya Habasha ta sabawa doka, kuma ba ta damu da yadda hakan zai shafi kasashensu ba.

    Abiy Ahmed, firai ministan Habasha,ya sanar da ci gaban da aka samu a gina katafariyar madatsar ruwan da kasarsa ta gina da ta lakume dala biliyan 4 a jiya Lahadi,

    Tun shekarar 2011, kasashen Masar da Sudan suke takaddama da Habasha akan batun cike kogin na Nilu.

    Sai dai gwamnatin Habasha ta kafe da cewa madatsar ruwan ta na da muhimmanci wajen samar da wutar lantarki ga miliyoyin 'yan kasar, da ta taka rawa wajen rage talauci.

    • Rikici tsakanin Masar da Habasha: Rikici kan Kogin Nilu
  8. Girgizar ƙasar Moroko: tawagar kasashen waje sun shiga aikin ceton mutane

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ma'aikatan agaji daga kasashen waje sun isa Moroko domin taimakawa takwarorinsu na kasar a aikin ceton wadanda girgizar kasa ta sanya suka makale a baraguzan gini ko tsaunukan da aka gagara isa.

    Sama da mutane 2100 ne suka mutu a girgizar kasar ta daren Juma'a.

    Gwamnatin Moroko ta ce ta amince da taimakon gaggawar da kasashen Qatar, da Hadaddiyar daular Larabawa da Birtaniya da Sufaniya suka yi.

    Daruruwan mutane na ta turuwa asibitico domin bada taimakon jini a Marrakesh.

    Manel Houda, ma'aikaciyar asibiti ta ce lamarin ya munana, amma suna baƙin kokarinsu.

    • Girgizar-ƙasa ta kashe sama da mutum 1,037 a Moroko
    • Girgizar ƙasar Moroko: 'Masu aikin ceto na fuskantar cikas'
  9. Assalamu alaikum

    Ma su bibiyar wannan shafin barkan mu da war haka.

    Aisha Babangida ce ke fatan kun tashi lafiya.

    Ni zan kasance da ku a tsawon wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu.