'Ba don Majalisar Ɗinkin Duniya ba, da mun banu da ta'addanci'

Wannan shafin yana kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza

  1. Gwamnati za ta rufe tashar jirgin saman Legas

    mma

    Asalin hoton, mm2

    Daga ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 2023 za a rufe filin jirgin sauka da tashin jiragen saman Murtala Muhammed da ke Legas bayan wani matakin yin wasu gyare-gyare da za a yi a harabar filin jirgin da aka kwashe kusan shekara 43 da ginawa.

    Ministan ma'aikatar lura da sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan, inda ya shawarci kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje da su yi amfani da sabuwar harabar da aka kammala kafin a kammala aikin.

    Wannan dai ana ganin zai shafi sha'anin sufurin jiragen sama a filin jirgin matuƙar ba an kammala aikin da wuri ba.

    A watan Maris ɗin shekara ta 2022 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabon aikin gyaran filin jiragin, amma aikin na fuskantar tafiyar hawainiya.

    A shekrar 2019, tsohon ministan sufurin jirgen sama Hadi Sirika ya fito da shirin rufe filin jirgin saman, sakamakon mummunar lalacewar da ya yi, amma ba a samu damar aiwatar da hakan ba.

    Haka ministan ya bayar da sanarwar dakatar da shirin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya har sai ya tattauna da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

    Festus Kiyamo ya bayyana cewa za a ɗauki matakan gaggawa da suka haɗa da siyo motocin safa-safa domin ɗaukar fasinjoji a filin jirgin.

    Ya ce babban abin damuwa ga 'yan Najeriya da baƙi shi ne yanayin filin jirgi, abin da ya sa za a yi amfani da sabon da wani kamfanin ƙasar Chana ya gina.

  2. 'Yan bindiga na fito da sabbin dabarun hare-hare a Zamfara

    ll

    Asalin hoton, Faceboo/Lagbaja

    Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda take cewa wasu 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a shiyyar arewa maso yamma da arewa ta tsakiya na amfani da wasu hanyoyin yaudara da za su iya kai wa ga tayar da rikici a ƙasa.

    Bayanin ya ƙara da cewa akwai hujjojin da ke nuna cewa 'yan ta'addan na amfani da dabarun dasa nakiya da sauran abubuwa masu fashewa wajen kai hare-hare, abin da zai jefa tsoro cikin zukatan mutane.

    Sai dai rundunar sojojin ta ce a shirye take domin bankaɗo duk wani makirci da 'yan ta-da-ƙayar-bayan ke amfani da shi, duk girmansa.

    Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a hedkwatar Sojoji da ke Abuja, lokacin da yake karɓar baƙuncin mai taimaka wa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a kan sha'anin yaƙi da ta'addanci, Vladimir Voronkov.

    Babban hafsan sojojin ya kuma ce a shirye rudunar take don yin haɗin gwiwa da Majalisar Ɗunkin Duniyar wajen ganin an maido da zaman lafiya a yankunan ƙasar.

    Ya ce za su yi amfani da kowanne mataki da ya dace domin tabbatar da nasarar hakan.

    Ya kuma nemi tallafin Majalisar Ɗinkin Duniyar da sauran hukumomi domin ɗaukar matakin da ya fi dacewa ga tubabbun 'yan ta-da-ƙayar-baya.

    Mai taimakawa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Vladimir Voronkov, ya sha alawashin cewa hukumarsa za ta tallafawa Najeriya wajen gano da kuma gurfanar da masu aikata muggan laifuka.

  3. Shugaba Ramaphosa ya buƙaci a ɗau matakan gaggawa kan matsalar gobara a ƙasar

    Zimbabwe

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya buƙaci a ɗauki matakin gaggawa don magance matsalar yadda ake gina gidaje, bayan gobara da ta hallaka mutum 74 a birnin Johannesburg.

    Rashin ingancin ginin da cunkushewa na cikin matsalolin da suka janyo kasa ceto mutane.

    Ethel Jack wadda ɗan'uwanta ya faɗo daga taga domin tsira da ransa, ta bayyana wa BBC yadda ginin yake kafin gobarar; Ta ce da mutum ya shiga farfajiyar wurin datti ne zai masa maraba, idan za a hau bene sai an mutane sun yi turmutsutsun.

    Amma a hawan da suke zaune, akwai tsafta da kofa, wadda suke rufewa duk da yake hanya daya ce ta shiga gidan kuma ita ce ta fita.

  4. Kungiyar ƙwadago za ta shiga yajin aikin gargaɗi kan janye tallafin fetur

    NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta sanar da aniyar shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu a kan matsin rayuwa da 'yan ƙasar ke ciki sakamakon janye tallafin fetur.

    NLC ta ce za ta gudanar da yajin aikin ne a ranakun Talata da Laraba mai zuwa.

    A ranar da aka rantsar da shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye tallafin man fetur, yanayin da ya haifar da tsadar litar man fetur a gidajen mai daga naira 197 zuwa 617.

    NLC ta nuna ƙin amincewa da matakin gwamnati da aiwatar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

    Shugaba Tinubu ya sha ganawa da 'yan ƙwadagon a kokarin ganin an cimma daidaito.

  5. Ba za mu ɗaga wa sojojin Nijar ƙafa ba- Ecowas

    Tinubu

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas) ta jadadda cewa babu batun ɗaga ƙafa ko bai wa sojojin Nijar dogon lokaci kafin mayar da ƙasar kan turbar dimokraɗiyya.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Ecowas ta ce an ja hankalinta a kan wasu rahotanni da ke cewa ta ba da shawarar wa'adin miƙa mulki ga sojojin Nijar, wanda ta ce labarin ba daga wajenta ya fito ba.

    Ecowas ta ce rahoton da ake yaɗawa har a kamfanin dillancin labarai na AFP, babu gaskiya a cikinsa.

    Ƙungiyar ta sake jadadda bukatarta ga sojojin Nijar, su mayar da Mohamed Bazoum karagar kan mulki nan take.

    Kafin wannan sanarwa, an jiyo shugaban Ecowas kuma shugaban ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yana cewa babu batun a sakarwa sojojin Nijar mara.

    Bola Tinubu ya ce: "ina ma laifin sojojin da suka yi juyin mulki, su yi koyi da tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, wanda bayan hawa kan mulki ya mayar da ƙasar kan tsarin dimokradiyya a 1999, bayan shafe wata tara yana shugabanci".

    Tinubu ya ce, "wannan misali a yau ya kasance abin da ake cin ribarsa da buɗe sabon babi ga 'yancin dimokraɗiyya a Najeriya".

    Shugaban ya ce shi bai ga wani dalili da zai hana sojojin Nijar yin koyi da Najeriya ba, ta wannan fuskar.

    Gwamnatin sojin Nijar ta buƙaci a ba ta shekara uku a kan mulki, matakin da Ecowas ta yi watsi da shi.

    Tinubu na waɗannan bayanai ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III.

    Shugaban na Ecowas ya ce ba za a ɗage takunkuman da aka sanya wa Nijar ba, har sai sojojin ƙasar sun miƙa wuya.

  6. Brighton ta dauki aron Ansu Fati daga Barcelona

  7. Burkina Faso da Rasha na ƙoƙarin ƙulla kawance soji

    Burkina Faso

    Asalin hoton, Burkina Faso presidency

    Shugaban gwamnatin soja na Burkina Faso, Ibrahim Traore ya tattauna da wakilan Rasha a ƙoƙarin ƙulla kawancen soji, kamar yada fadar gwamnatin ta tabbatar.

    Sanawar da suka fitar na cewa, mataimakin ministan tsaro na Rasha Yunus-bek Yevkurov ya je ƙasar ne domin bibbiyar tattaunawar baya da aka yi tsakanin Mista Traore da Shugaba Vladimir Putin a babban taron ƙasashen Afirka da Rasha da aka gudanar a St. Petersburg a cikin watan Yuli.

    Tattaunawar ta mayar da hankali kan batun taimakon soji da suka haɗa da horar da sojojin Burkina Faso da sauran jami'ai da matuƙan jirgin sama, a cewar sanarwar.

    Sannan sun tattauna batutwuwan da suka shafi bunƙasar tattalin arziki da makamashin nukilliya.

    Ziyarar na zuwa ne adaidai lokacin da Rasha ta ɗaura ɗamarar inganta alaka ta fuskar siyasa da tattalin arziki a Afirka.

    Shugaban sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin wanda ya mutu a haɗarin jirgin sama a makon da ya gabata, ya yi kokarin faɗaɗa ayyukansu a Burkina Faso.

  8. Rabon tallafi ya haifar da tashin farashin shinkafa a Najeriya

    Shinkafa

    Asalin hoton, Getty Images

    Matakin da gwamnatin Tarayyar Najeriya da jahohi ke ɗauka na sayen kayan abinci domin rarrabawa a matsayin tallafi ya haifar da tashi kayan abinci a kasuwanni.

    Rahotanni na nuna cewa 'yan kasuwa da dama na bayyana cewa buƙatar sayen kayan abincin da masu kwangila ke daɗa yi shi ne ya haifar da wannan lamari, ga shi kuma an samu ƙarancin shigo da abinci a kasuwanni.

    Tun bayan da Hukumar da ke lura da tattalin arzikin Najeriya ta fitar da sanarwa a ranar 7 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta amince a fitar da naira biliyan 5 domin sayen abincin da za a tallafawa talakawa, aka soma faɗawa wannan yanayi.

    Gwamnatin ta Najeriya dai ta bayar da umurnin raba buhunan shinkafa ga dukan jihohi 36 domin rage raɗaɗin talaucin da 'yan ƙasar suka shiga sakamakon cire tallafin mai.

    An samu galibin jahohin da suka bayyana cewa sun samu kayan tallafin da aka aike musu, inda wasun suka ce har ma sun soma amfani da wani ɓangare daga naira biliyan 5 da aka ba su wajen sayen kayan abinci da suka haɗa da shinkafa da sauran su domin raba ma jama'a.

    Ko waɗanne motocin tirela biyar da aka rabawa jahohin na ɗauke da buhuna dubu uku masu nauyin kilogiram 50. Wanda kenan an rabawa jahohin 36 haɗi da birnin tarayya Abuja, kimanin buhuna 111,000.

    Wata majiya mai tushe ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa samar da kayan tallafin nada manufar rage tsananin yunwa da talauci da kuma amfani a hanyar juya jama'a yadda ake so.

    "Kwanaki kaɗan da soma sayen kayan abincin a kasuwa, kowane buhu ya ƙara naira 10,000 cikin kwanaki goma kawai da gwamnati ta soma sayen abinci ga masu sari da masu sarrafa shinkafar, saboda gwamnati ba ta da wata shinkafa da ta adana musamman domin irin wannan lokaci".

  9. An soki jami'an DR Congo kan mutuwar masu zanga-zanga 43

    DR Congo

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Rights Watch, ta zargi jami'an tsaron Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da kisan gwamman masu zanga-zanga a yammacin birnin Goma a ranar Larabar nan da ta wuce.

    Ƙungiyar ta ce, jami'an tsaron sun buɗewa masu zanga-zangar da ya kamata su kare rayukansu wuta, domin hana su boren da wata ƙungiyar musulmai ta shirya ta adawa da jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Human Rights Watch ta ce ta na da sahihan bidiyo biyu da suka nuna yadda sojoji suke jefa gawarwakin mutane a bayan akori-kura.

    A ɓangaren hukumomin Congon sun ce an kashe masu zanga-zanga shida lokacin da sojoji suka shiga tsakani bayan an jefe wani ɗan sanda ya mutu.

  10. Ana nuna damuwa kan ɗumbin basukan da ake bin ƙasashen Afirka

    Wani sabon rahoto ya ce idan ba a yi wani abu ba don gyara ɗumbin basukan da ke addabar Afirka, to daga ƙasashen waje za a ji illar da ke tattare da hakan.

    Ƙungiyar yaƙi da talauci da cutuka ta One Campaign ta ce ƙasashen Afirka na biyan bashin fiye da kashi ɗari biyar a kan basukan da suke buƙata wanda zai sanya su tafka asarar kuɗi sama da dala biliyan hamsin nan da wasu shekaru masu zuwa.

    Rahoton ya ce matsalar za ta kara ta'azzara matsalar kwararar 'yan gudun hijira da rage daukar matakin magance sauyin yanayi, da kassara tattalin arzikin duniya da ke tangal-tangal.

    Rahoton ya yi misali da Najeriya wadda ya ce abin da ta biya na bashin da ta ci ya ruɓanya wanda ta ke kashewa a fannin lafiya da ilimi har sau biyu.

  11. Tarayyar Afirka ta dakatar da Gabon daga ƙungiyar

    Gabon

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta dakatar da Gabon daga cikinta bayan juyin-mulkin sojoji na ranar Laraba, wanda ta yi alla-wadai.

    Wannan mataki ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin tsaro da zaman lafiya na ƙungiyar ya gudanar a jiya Alhamis.

    Kafin dakatarwar sojojin da suka ƙwace mulki a Gabon sun ce za su kafa gwamnatin riƙo bayan hamɓarar da Shugaba Ali Bongo.

    Sai dai sojojin ba su shaida tsawon lokacin da za su zauna a mulki ba kafin mayar da ƙasar hannun farar-hula.

    Babbar jam'iyyar adawar ƙasar ta buƙaci a yi zaman sulhu domin sannin inda ƙasar ta dosa.

    Jam'iyyar na cewa al'ummar Gabon sun yi murnar ganin an kawar da zuri'ar Bongo da suka shafe sama da shekaru 50 suna mulkar ƙasar. Sai dai kuma sun buƙaci sojoji su yi abin da ya dace domin ci gaban ƙasar.

  12. An yanke wa wadanda suka kutsa majalisar Amurka hukuncin dauri

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An yanke wa wasu tsofaffin shugabannin kungiyar Proud Boys masu ra'ayin rikau su biyu hukuncin dauri mai tsawo a gidan yari, sakamakon samun su da hannu a rikicin da ya faru a majalisar dokokin Amurka da ke birnin Washington a shekarar 2021.

    An yanke wa Joe Biggs, tsohon sojan Amurka ne zaman kason shekara 17, yayin da Zachary Rehl kuma shekara 15.

    Norman Pattis, wanda shi ne lauyan daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, Joe Biggs; ya ce sakamakon zaman bai yi kyau ba. Ya kara da cewa yanke musu hukuncin daurin shekara 17 da 15 ya yi yawa, mun dauka akwai sassaucin da za su samu kamar shekara 10."

    Dukkansu sun fashe da kuka tare da yin da na sanin abin da suka aikata.

    Masu shigar da kara sun ce Biggs ya jagoranci far wa Capitol don murde nasarar da Joe Biden ya yi a zaben 2020.

  13. Maraba!

    Masu bibbiyar mu a wannan shafi barka da wannan lokaci da fatan kun wayi gari lafiya a wannan rana ta Juma'a.

    Za mu rinka kawo muku labarai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya tsawon wannan rana.

    Da fatan za ku kasance tare da mu, kuma kuna iya tafka muhawara a shafukanmu na facebook da X da kuma kallon hotuna da bidiyoyi masu kayatarwa a shafinmu na instagram..