Juyin mulkin Gabon: Annoba ta kama Afirka - Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umaymah Sani Abdulmumin, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Ana cikin tasku a Tarayyar Afirka yayin da ake samun masu maraba da juyin-mulkin sojoji, Sharhi daga Will Ross

    Gabon

    Asalin hoton, Gerauds Wilfried Obangome/Reuters

    Kusan ya zama abin yayi kwana nan a Afirka - inda ake samun wasu 'yan tsirarun sojoji da ke bayyana a Talabijin suna sanar da juyin-mulki.

    A wannan lokaci maguɗin zaɗe shi ne dalilin da aka yi amfani da shi wajen kifar da gwamnatin Ali Bongo, shugaban ƙasar Gabon, sa'o'i bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen kasar me cike da ce-ce-ku-ce. An haramtawa masu sa ido daga ketare da 'yan jarida shiga ƙasar domin bada rahoton zaɓen.

    A wani yanayi da aka saba ganin yada ake amfani da kuɗi wajen sayen magoya-baya, abu ne mai wahala a iya gane soyayyar gaskiya a wannan lokaci.

    Amma a Gabon babu shaku abubuwa sun bambanta ganin cewa an gaji da ganin iyalan gidan Bongo da ke mulkin ƙasar tun 1967.

    Kusan mulki ya zama wani abin gado ga wannan zuri'a abin da ya damu 'yan kasar da dama. Mutane ba su ja kafa ba, wajen fantsama kan tittuna, cikin raha da farin ciki, yanayin da babu shaka ya nuna zakuwarsu ko gajiya da mulkin gida guda. Har yanzu dai babu alamar nuna turjiya.

    Ga ƙasashen duniya, ciki harda Tarayyar Afirka, wannan yanayi abin damuwa ne. Faransa ta ruga wajen fitar da sanarwar alla-wadai.

    Tasirinta a Afirka na fuskantar kalubale da barazana a shekarun baya-bayanan, sannan tana kiran a bari Ali Bongo ya kara wasu shekaru a mulki wanda ba lallai ya yi wa 'yan kasar daɗi ba.

  2. Ɗan Ali Bongo da sojoji suka garƙame

    Nourideen

    Asalin hoton, Getty Images

    Noureddin Bongo Valentin mai shekara 31 ya kasance makusanci sosai ga mahaifinsa Ali Bongo, sannan mai ba shi shawara kan lamura da dama.

    Sojoji sun garƙame Noureddin tare da shugaban ma'aikatar fadar gwamnati, Ian Ghislain Ngoulou da wasu mataimakansa biyu da wasu jami'an gwannati da na jam'iyyar da ke muki PDG.

    Ana zargin dukkaninsu da cin amanar kasa da almubazaranci da rashawa.

  3. Bayani kan ƙasar Gabon

    A wannan taswirar ana iya ganin inda Gabon take a nahiyar Afirka. Tana ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar mai arzikin man fetur.

    Taswirar ƙasar Gabon

    Harkar man fetur ta samawa kasar kashi 38.5 cikin 100 na tattalin arzikinta, sannan shi ne kashi 70.5 cikin 100 na arzikin da ta fi fitarwa a 2020, a cewar Bankin Duniya.

    Masu suka na cewa Ali Bongo bai taɓuka wani abin kirki ba a fanin inganta tatalin arzikin man fetur ta yada talauci zai ragu sosai a ƙasar.

    Ali Bongo ya inganta fannin haƙo ma'adinai na ƙasar, sannan yana daukan matakai ta fuskar alkinta muhalli da cin gajiyar dazukan da suka mamaye ƙasar.

    A shekara ta 2021, Gabon ta kasance ƙasar Afrika ta farko da aka biya makudan kuɗaɗe kan rage fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli ta hanyar kare gandun dajinta.

  4. Rasha ta bi sahun Faransa da China wajen nuna damuwa kan halin da ake ciki a Gabon

    Manyan ƙasashen duniya na cigaba da mayar da martani kan juyin-mulkin Gabon - Rasha ta ce ta damu mutuƙa kan halin da ake ciki a ƙasar.

    Sannan Faransa ta sake jadadda damuwarta kan yanayin da aka shiga a Gabon; wata sanarwa da Ministan harkokin waje Olivier Véran ya fitar na cewa gwamnatinsu nason a mutunta sakamakon zaɓen da aka kammala a Gabon.

    Shugaba Ali Bongo, mai shekara 64, ya lashe zaɓen kasar a karo na uku wanda aka gudanar a ranar Asabar. Sojoji a yanzu sun ce sun yi masa ɗaurin talala.

  5. Labarai da dumi-dumi, Babban dogarin fadar shugaban Gabon ya zama jagora

    Karin bayani game da sanarwar juyin mulki a Gabon.

    Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun bayyana shugaban dogarai na fadar shugaban kasa a matsayin wanda zai jagoranci kasar kafin a shirya zabe a nan gaba.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya ruwaito hakan samun wadansu bayanai daga jawabin dakarun.

  6. Babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso daga NNPP - Buba Galadima

  7. Sojoji sun buƙaci masu murnar juyin-mulki su koma gidajensu

    Gabon

    Asalin hoton, EPA

    Jim kaɗan bayan sojoji sun sanar da juyin-mulki cuncurundon mutane sun fantsama kan tittuna inda suke bukukuwan murna musamman a dandalin Boulevard Triomphal Omar Bongo, da ke birnin Libreville - a cewar wani ɗan jaridar ƙasar da ya tattauna da BBC.

    Mutanen sun rinka ɗaga tutar ƙasar launin kore da ruwan ɗorawa da shuɗi domin nuna cewa suna murna da matakin sojoji.

    Duk da cewa hakan ya daɗaɗɗawa sojojin, daga bisani sun buƙaci kowa ya koma gida musamman a wuraren da ke da haɗari.

  8. Wane ne Ali Bongo?

    Gabon

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu na kallonsa a matsayin sangartaccen ɗa, wanda ke kallon mulkin ƙasar Gabon a matsayin hakkinsa na gado.

    Ya taba zama mawaki, inda daga baya ya gaji mahaifinsa a matsayin shugaban kasar, ya dora a kan shekara 50 da iyalansa suka kwashe suna mulkin kasar.

    Wasu kuwa na masa kallon mai kawo sauyi, kuma sun ce talakawa ne suka zabe shi bisa tsari na demokuraɗiyya.

    Sai dai rashin lafiyar da ya yi fama da ita a shekarun baya sun haifar da tantama a kasar mai yawan al’umma sama da miliyan biyu.

    A ranar 7 ga watan Janairun 2019 wasu gungun sojoji sun yi yunkurin yi masa juyin Mulki, lamarin da bai yi nasara ba.

    Sojojin sun ce dalilin yunkurin nasu shi ne domin su mayar da mulkin demokuradiyya a kasar bayan zaben shekara ta 2016, inda Mr Bongo ya yi nasara da kyar duk da zarge-zargen cewa an tafka magudi.

  9. China ta buƙaci a bai wa Shugaba Bongo kariya

    Gwamnatin China ta ce tana bibbiyar abubuwan da ke faruwa a Gabon sau da kafa tare da bukatar a bai wa Shugaba Ali Bongo kariya.

    A wani taron manema labarai, kakakin ministan harkokin waje ya buƙaci ɓangarorin ƙasar biyu su hau teburin sulhu domin daidaita lamura da mutunta dimokuraɗiyya.

    Wang Wenbin ya kuma nemi a basu tabbacin kare Ali Bongo da iyalansa daga duk wani hadari.

  10. Sojoji sun yi wa Shugaban Gabon ɗaurin talala

    Rahotanni daga kamfanin dilancin labarai na AFP na cewa sojoji sun yi wa Shugaban Gabon da suka hamɓarar da safiyar yau Laraba ɗaurin talala.

    A wata sanarwa da suka fitar ta kafar Talabijin ƙasar, sojojin sun ce Ali Bongo na hannunsu tare da iyalansa da kuma likitocinsa.

    An kuma kama ɗaya daga cikin 'ya'yan shugaban kan zargin cin amanar kasa, a cewar sanarwar.

  11. Yadda wasu 'yan Gabon ke maraba da sojojin da suka ƙwace mulki a ƙasar

    Waɗannan hotunan da muka samu daga kamfanin dilanci labarai na AFP na nuna yadda mazauna birnin Libreville na Gabon ke murna da jinjinawa sojojin da suka ƙwace mulki bayan sanarwar da suka yi da safiyar Laraba.

    Wani ɗan jaridar Reuters ya ce ɗaruruwan mutane sun fantsama kan titi suna bikin murna a birnin ƙasar.

    Gabon

    Asalin hoton, AFP

    Gabon

    Asalin hoton, AFP

    Gabon

    Asalin hoton, afp

  12. NNPP ta mu ce babu wanda ya isa ya kori Kwankwaso - Buba Galadima

    Kwankwaso

    Tsagin jam'iyyar NNPP ta Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sanar da korar 'yan kwamitin amintattun da suka dakatar da jagoran nasu na kasa, Kwankwaso.

    Ɗaya daga cikin jigo a jam'iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, Injiniya Buba Galadima ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki wannan mataki ne a wani taro da suka gudanar a Abuja a wani yunkurin na fasalta al'amuran jam'iyyar.

    Wannan mataki na zuwa ne bayan a jiya Talata wani ɓari na jam'iyyar ta NNPP ya bayar da sanarwar dakatar da Rabi'u Kwankwaso daga jam'iyyar bisa zargin yi wa jam'iyyar zangon-kasa.

  13. An dakatar da buɗe kogin Lagdo na Kamaru

    Lagdo

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin kogin Lagdo na ƙasar Kamaru sun fitar da sanarwa inda suka ce sun dakatar da buɗe kogin don rage yawan ruwan da ke cikinsa.

    Da farko hukumomin kogin sun yanke shawarar sakin ruwan ne kaɗan-kaɗan, sakamakon bambancin yanayin damina da ke tsakanin Najeriya da Kamaru har ma sun fara sakin ruwan a hankali tun daga makwanni biyu da suka gabata.

    Tun da farko dai hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta gargaɗi mutanen da ke zaune a kusa da wuraren da ka iya fuskantar ambaliyar sakamakon sakin ruwan kogin a kan su tashi, tare da daukar matakan da suka dace don ganin sakin ruwan bai yi ɓarna ba.

    Babban jami'in kai dauki na hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, Bashir Idris Garga, ya shaidawa BBC cewa dama hasashe ake yi don haka da aka fahimci babu wata barazana mai karfi sai aka fasa sakin ruwan.

    A bara dai sakin wannan ruwa ya haddasa ambaliyar ruwa da rusa gidaje da sanadin rayuka da dukiyoyi.

  14. An kai wa jiragen dakon kaya na Rasha hari

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Rasha sun bayyana cewar an kai wa jiragen saman Rasha na dakon kaya hari da jirgi maras matuki a arewa maso yammacin birnin Peskov.

    Biyu daga cikin jiragen sun kama da wuta.

    Hotunan bidiyo daga birnin Peskov na Rasha sun nuna yadda jiragen suka kama da wuta.

    Gwamnan lardi ta sanar da cewar babu wanda ya jikkata amma an lalata wasu jirage huɗu na daukar kaya.

    Tun da farko sojojin Rasha sun bayyana yadda suka harbo jiragen Ukraine marasa matuka yayin da suke shawagi a saman yankunan birnin Moscow.