Gwamnatinmu ba za ta sake karɓo bashi ba - Ministan kuɗin Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, Jakadanmu ba zai fice daga Nijar ba - Macron

    Macron

    Asalin hoton, AFP

    Jakadan Faransa a Nijar zai ci gaba da zama a cikin kasar duk da matsin lamba daga sojojin da suka yi juyin mulki, in ji Shugaba Emmanuel Macron.

    Macron a jawabinsa ga jakadun kasashen waje ya jaddada goyon bayansa ga hamɓararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum wanda ya ce ba zai yi murabus ba.

    A cewar Macron wannan matakin ya nuna Bazoum mutum ne mai karfin hali.

    Wa'adin sa'o'i 48 da aka bai wa jakadan Faransar, Sylvian Itte domin ya bar Nijar ya riga ya cika.

    Macron ya kara da cewa Faransa ba za ta canza matsayinta ba na yin Allawadai da juyin mulkin soji a Nijar tare da nuna goyon bayanta ga Bazoum.

    Tun a ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji karkashin jagorancin Janar Tchiani suka kifar da gwamnatin shugaba Bazoum.

    • Ci gaba da tsare Mohamed Bazoum na jawo ƙarin barazana
    • 'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'
  2. Jagoran adawa a Zimbabwe ya zargi Shugaban ƙasar da juyin mulki

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran Adawa a Zimbabuwe, Nelson Chamisa, ya zargi shugaba Emmerson Manangagwa da aiwatar da juyin mulki, kodayake bai bayar da hujjojin da za su tabbatar da zargin nasa ba.

    Jagoran adawar na jam'iyyar CCC ya bayyana cewa ba zai amince da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da zaɓen, la`akari da sanarwar da masu sanya ido suka fitar na nuna cewa an samu kalubale a wajen gudanar da zaɓen abin da kuma ka iya shafar sakamakon.

    Nelson Chamisa ya ce zaɓen na je-ka-na-yi-ka ne, inda kuma yawan kuri`u ya tabbatar da tafka magudi a cikin sa.

    Nelson Chamisa ya samu kashi 44 cikin ɗari yayin da shugaba Emmerson Manangagwa ya samu kashi 52.6 cikin ɗari.

    Yanzu dai 'yan adawar na da tsawon mako guda domin shigar da ƙara a kotu.

    Mista Mnangagwa ya yi watsi da sukar da ƙasashen ƙetare suka yi wa zaɓen bayan ya jaddada cewar an gudanar da sahihin zaɓe.

    Masu sanya ido daga ƙasashen waje da suka haɗa da Afirka ta Kudu sun ce zaɓen bai cika ka`idojin da kundin tsarin mulkin Zimbabwe ya yi tanadi ba.

    • Yadda kulle-kulle da kashe-kashen siyasa suke ci gaba da barazana ga zabukan Zimbabwe
  3. Rundunar tsaron RSF ta yi tayin sulhu ga gwamatin sojin Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar dakarun RSF a Sudan sun fito fili sun bayyana manufarsu domin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa tsakaninsu da sojojin gwamnati, inda ta ce a shirye take domin gudanar da tattaunawar da za ta haifar da cikakken sulhu.

    Shugaban dakarun na RSF, Laftanar Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti ne ya fitar da wani dogon bayani a ranar 27 ga watan Agustan nan a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter, yana mai cewa "shirye suke domin kawo ƙarshen tashin hankali da kuma sake gina wata sabuwar ƙasar Sudan".

    Bayanin nasa har wa yau, ya ce kawo karshen yaƙin "zai ɗora ƙasar a kan turbar zama ƙasa mai bin tsarin dimukuradiyya. Za a iya samun tattaunawa tsakanin sassan biyu da za ta ƙunshi dukkan masu ruwa da tsaki a ƙasar wadda kuma za ta tabbatar da an samar da tsagaita buɗa wuta mai ɗorewa".

    Wannan na zuwa ne rana ɗaya da shugaban sojin Sudan Lafanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya isa wani birnin gabashin ƙasar a karon farko, tun bayan ɓarkewar rikicin.

    Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa Mista Abdel Fattah zai bar Sudan domin kai ziyara kwanan nan zuwa ƙasashe Misira da Sudiyya.

    • Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
    • An kashe gwamnan jihar Darfur ta Yamma a Sudan
  4. Dole Najeriya ta ɗauki matakai masu tsauri don kare martabarta - Tinubu

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce dole ne kasar ta samar da sauye-sauye masu tsauri don samun karbuwa da mutuntawa daga sauran kasashen duniya.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Lahadi a farkon taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya na 2023.

    Tinubu ya ce duk da cewa wadannan sauye-sauyen na iya zama masu tsauri da farko, dole ne Najeriya ta kasance a shirye da daukar su don taimaka wa kasar ta bunkasa.

    "Sauye-sauye da muke yi suna da muhimmanci a nan gaba, ba don kanmu kadai ba, muna so mu bar kasar fiye da yadda take a baya ga waɗanda za su zo bayan mu."

    Tinubu ya kuma yi magana kan yadda Najeriya ke bin wasu kasashe makudan kudade, wanda ya ce hakan ba zai dore ba.

    Tinubu ya ce, "Shin za mu iya ci gaba da biyan basussuka da kashi 90 cikin dari na kudaden da muke samu? Wannan hanya ce mai hadari, muna bukatar mu yi manyan sauye-sauye don ɗaukaka kasarmu a kuma girmama mu a duniya."

    Shugaban ya kuma yi kira ga al'ummar Najeriya da su canza tunaninsu da yadda suke yi domin ganin kasar ta gyaru.

    • Yaya ƴan Najeriya suka karɓi shirin rage raɗaɗi na Tinubu?
    • Alƙawura biyar da Tinubu ya yi wa 'yan Najeriya a jawabinsa
  5. Faransa za ta hana dalibai mata sanya abaya a makarantu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Ministan ilimi Gabriel Attal ya bayyana cewa, ƙasar Faransa za ta haramta wa dalibai mata sanya rigunan abaya a makarantun gwamnatin ƙasar.

    Ministan ya ƙara da cewa hukuncin zai fara aiki da zarar dalibai sun koma makaranta a farkon watan Satumba.

    An dai kwashe watannin ana tafka muhawara ko za a bar dalibai su dinga ɗaukar darasi da hijabi inda aka jima da haramta rufe gashin kai.

    Wakiliyar BBC ta ce rahotanni sun bayyana cewa ana samun ƙaruwar daliban da suke sanya irin wannan kaya, abin da ke haifar da rikici tsakanin malamai da iyaye.

    Wata doka da aka amince da ita a shekara ta 2004 ta hana mutane sanya kaya ko daukar wani abu da zai bayyana addinin mutum.

    • Duniya na Allah-wadai da yunƙurin juyin mulki a Nijar
    • Rashin kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma laifin Faransa ne?
  6. An tsaurara tsaro a wani yanki na Indiya saboda rikicin kabilanci

    ...
    Bayanan hoto, ...

    Hukumomi a jihar Haryana da ke Arewacin Indiya sun ƙara tsaurara matakan tsaro a gundumar Nuh, bayan da kungiyoyin mabiya addinin Hindu suka ce za su ci gaba da gudanar da gangami da rikicin kabilanci ya dakatar a watan da ya gabata.

    Mahukuntan jihar dai sun ki bayar da izinin gudanar da taron ne bayan mutuwar wasu mutane shida a lokacin da aka kai hari a watan Yuli.

    Yanzu haka an tura jami'an tsaro zuwa yankunan da suke da mabiya adinin Islama da dama bayan rufe makarantu da dakatar da internet.

    Tun bayan rikicin hukumar tsaro ta hana taron sama da mutane hudu a yankin.

    • Ko rushe-rushen gidaje take haƙƙi ne a Indiya?
  7. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da warhaka.

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a safiyar Litinin domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da makwabtan kasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Mu je zuwa....