Ƙarin 'yan Najeriya 137 sun koma gida daga gidajen yarin Libya
Asalin hoton, NEMA
Ƙarin 'yan Najeriya 137 da suka maƙale a gidajen yarin Libya sun koma gida a yau Litinin, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta bayyana.
Hukumar National Emergency Agency (NEMA) ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin ƙarfe 5:17 na yamma.
"Mutanen waɗanda akasarinsu mata ne sun bayyana yadda suka sha wahala lokacin da suke tsare a gidajen yarin da ke arewacin Afirka mai haɗari," kamar yadda wata sanarwa daga NEMA ta bayyana.
Jimillar mutanen da Najeriya ta kwaso daga Libyar sun zama 298 zuwa yanzu, bayan wasu sun saauka a makon da ya gabata.
Daga cikinsu akwai mata manya 119, "waɗanda da yawansu ke ɗauke da ciki", da yara mata uku, da jarirai mata biyu.
Akwai kuma maza manya 170, yara maza uku, da jariri ɗaya.
Asalin hoton, NEMA
Gwamnatin Gombe ta rufe gidajen gala a jihar
Asalin hoton, Gombe State Government
Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen gala a jihar da ke arewacin Najeriya nan take.
Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya sanar da hakan yana mai cewa an ɗauki matakin ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga jama'a kan "ƙaruwar ayyukan rashin tarbiyya da aikata laifuka da kuma taɓarɓarewar tsaro" a irin waɗannan kulob-kulob na dare.
Wata sanarwa da mai magana da gwamnan jihar ya fitar ta ce an umarci 'yan sanda da rundunar tsaron farar hula da jami'an tsaro na Operation Hattara su tura mutanensu don cika umarni da tabbatar da aiki da umarnin.
Sanarwar ta lissafa gidajen gala da matakin rufewar ya shafa kamar Jami'a Gidan Wanka a Mil 3 kan titin zuwa Yola, da Babban Gida a New Mile 3 kan titin zuwa Yola, da Gidan Lokaci a Mil 3 kan titin Reservoir.
Sauran su ne Farin Gida na II a Wuro Karal kan titin Kalshingi, da Gidan Zamani a New Mile 3, da Albarka Entertainment a Wuro Karal kan titin Bypass kusa da hara Form, dukkansu a birnin Gombe.
Haka nan, akwai Gidajen Gala na garin Kuri, da ƙauyen Lubo da Kurba a Yamaltu Deba, da Tauraren Wash a kan titin zuwa Bauchi, da Gidan Gombe, da Gala a garin Bajoga.
Ba mu ba yarjejeniya da 'yan cin amanar ƙasa - Babban Hafsan sojojin Sudan
Asalin hoton, Reuters
Babban hafsan rundunar sojojin Sudan kuma shugaban ƙasar ya mayar da martani ga wata sanarwa da abokin hamayyarsa a rikicin ƙasar ya fitar, da cewa a shirye yake su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dogon lokaci.
Sai dai Janar Abdel Fattah al-Burhan ya ce "ba mu, ba yarjejeniya da 'yan cin amanar ƙasa".
Tun da farko, shugaban dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, ya ce duk wata yarjejeniya da za a ƙulla, sai ta kasance wadda za ta mayar da Sudan kan cikakken tsarin mulkin farar hula.
Ya kuma yi kira a kawo ƙarshen hare-haren da dakarun ƙasar ke kai wa a kan fararen hula.
Sai dai babban hafsan sojojin Sudan Janar al-Burhan ya ce:
"Ba mu, muka fara wannan rikici ba, kuma ba mu neme shi ba. Su [RSF] ne suka fara yaƙi. Don haka, sai an ga bayansu kuma sai sun yi bayani kan laifukan da suka tafka..."
"Duk wanda ya ce an cimma wata yarjejeniya [da RSF] ko wani yana taimakawa, mafarki ne kawai. Ba mu, ba yarjejeniya da masu cin amanar ƙasa ko wasu mutane da suka ci amanar al'ummar Sudan kuma ba za mu yi aiki da duk wani ɓangare da ya ci amanar jama'ar Sudan ba."
Masu rajin kare 'yancin dimokraɗiyya a Sudan sun yi watsi da kalaman Hemedti, inda suka ce akwai tsagwaron munafunci a ciki, ganin ya ba da gagarumar gudunmawa wajen shirya hare-hare a kan fararen hula da kuma tabbatar da ganin sojoji sun ci gaba da mulki a Sudan.
A ranar 15 ga watan Afrilun bana ne faɗa ya ɓarke tsakanin dakarun RSF da rundunar sojin Sudan bayan shugabannin ƙasar biyu sun samu saɓani game da makomar ƙasar da kuma shirin miƙa mulki hannun farar hula.
Dubban mutane ne suka rasu kuma mutane fiye da miliyan huɗu sun tsere wa gidajensu.
'Yadda na haihu a hanya domin tsira da raina'
Yanzu me ya rage wa ƙasar da ta damƙa tsaronta a hannun Wagner?
Sojojin mulkin Nijar sun kama malaman jami'a
Asalin hoton, Reuters
Sojojin mulkin Jamhuriyar Nijar sun kama wasu malaman jami'a sakamakon nuna adawa da juyin mulkin da suka yi a watan Yulin da ya gabata.
An kama malaman ne bayan wasu 37 sun nisanta kansu ne daga wata sanarwa da uwar ƙungiyarsu ta fitar da ke ayyana goyon baya ga juyin milkin.
Shugaban majalisar mulkin sojan, Janar Abdourahmane Tciani, ya saka hannu kan wani umarni da ya cire malaman 37 daga duk wani muƙami da suke riƙe da shi a ƙungiyoyinsu.
Kazalika, daga bisani jami'an tsaro suka yi awon gaba da wasu daga cikinsu.
Tuni dai kungiyoyin fararen hula a kasar suka fara tsokaci kan wannan batu, inda suke kiran da a saki malaman nan take ba tare da sharaɗi ba.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai
Najeriya za ta fara yi wa yara riga-kafin kansar bakin mahaifa
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta fara yi wa yara mata riga-kafin cutar kansar bakin mahaifa daga ranar 25 ga watan Satumban 2023.
Gwamnatin ta ce yi wa mata masu shekaru tara zuwa 15 riga-kafin zai taimaka wajen guje wa kamuwa da cutar ta Human Papillomavirus Vaccine (HPV).
Kansa ko kuma ciwon dajin bakin mahaifa ciwo ne da ke shafar ƙwayoyin halittar wani ɓangare na mahaifa. Nau'o'in HPV kan faru ne ta hanyar saduwa kuma ita ce ta fi yawa a nau'in kansar da ke shafar mahaifa.
Rigakafin ta ka iya kare kashi 90 cikin 100 na sauran na'ukan kansar da HPV ke haifarwa.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce nau'ukan HPV (16 and 18), waɗanda ake yawan samun su a Najeriya, su ne ke haifar da kusan rabin manyan kansar bakin mahaifa a Najeriya.
An ƙiyasta cewa mata kusan 14,000 ne ke ɗauke da cutar a Najeriya, kuma mata 7,968 ne ke mutuwa sakamakon cutar duk shekara.
Me ya sa batun NYSC ɗin Hannatu Musawa ke tayar da ƙura?
Zanga-zanga ta ɓarke kan yunƙurin ƙulla alaƙa da Isra'ila
Asalin hoton, EPA
Zanga-zanga ta ɓarke a Turabulus, babban birnin Libya da wasu biranen ƙasar, bayan fitowar labarin ganawar da ministar harkokin wajen Libya da takwaranta na Isra'ila.
Masu zanga-zanga sun rufe tituna tare da ƙona tayoyi, suna karkaɗa tutocin Falasɗinu, ko da yake ga alama zanga-zangar ba ta gawurta ba.
Firaministan Libya dai ya dakatar da ministar harkokin wajen ƙasar bayan ta gana da takwararta ta ƙasar Isra'ila.
Libya - babbar mai goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa ce - kuma ba ta yarda da Isra'ila a matsayin ƙasa ba, abin da ya sa ganawar ta janyo zanga-zanga a ƙasar wadda mafi yawan jama'arta Larabawa ne.
Ministan harkokin wajen Isra'ila Eli Cohen ya ce ganawar "ta tarihi" wani matakin farko ne na ƙulla hulɗa da Libya.
Isra'ila dai na aiki don ƙara danƙon zumunci da ƙasashen Larabawa da na akasari Musulmai, waɗanda a hukumance ba su yarda da ita ba.
Sai dai, majalisar shugaban ƙasa a Libya wadda ke wakiltar larduna guda uku ta ce haramtaccen abu ne a mayar da hulɗa da Isra'ila.
Ofishin shugaban majalisar dokokin ƙasar ya zargi Najla Mangoush da tafka babbar cin amanar ƙasa, kuma Firaminista Abdul Hamid Dbeibah ya gabatar da ita don gudanar da bincike.
Sanarwar da Isra'ila ta bayyana game da tattaunawar da aka yi, ta zo da mamaki saboda babu wata masaniya cewa Isra'ila tana zawarcin Libya, babbar abokiyar gaba kuma zakara a kan gwagwarmayar al'ummar Falasɗinawa, musamman a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi.
A ranar Litinin, wani jami'in Isra'ila ya faɗa wa BBC cewa tun tuni aka shirya ganawar kuma ba a abu ne da ya zo bagatatan ba, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Libya take nunawa.
Bazoum ya nuna ƙarfin hali da ya ƙi yin murabus - Faransa
Gwamnatinmu ba za ta sake karɓo bashi ba - Ministan kuɗin Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da niyyar sake karɓo bashi a ciki ko wajen ƙasar ba, bayan cire tallafin man fetur da dunƙule tsarin canjin kuɗaɗen waje.
Ministan kuɗi da harkokin tattalin arziƙi, Cif Wale Edun ne ya bayyana haka a ƙarshen taron Majalisar Zartarwar Ƙasar na farko ranar Litinin a Abuja.
Ya ce amfanin da aka samu daga cire tallafin man fetur, za a zuba shi a ɓangarori daban-daban da za su taimaka wajen bunƙasa kuɗaɗen shiga ga gwamnati da inganta kasuwanci a cikin gida da kuma samun zuba jari daga ƙetare.
Wale Edun ya ce bayan ƙarin kuɗin shigar da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur, an tsara matakan fitar da tallafin rage raɗaɗi na taƙaitaccen wa'adi da matsakaici da kuma dogon lokacin.
Ya jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na muradin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya daga mawuyacin halin da yake ciki nan da wani ɗan lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya kuma ruwaito ministar masana'antu da kasuwanci da harkokin zuba jari, Doris Uzoka-Anite na cewa tuni har an fara samun masu tayin zuwa Najeriya don zuba jari a fannoni daban-daban na tattalin arziƙin ƙasar ciki har da ɓangaren man fetur da iskar gas da lafiya da haƙar ma'adanbai da kuma noma.
Taliban ta hana matan Afghanistan fita ƙasashen waje karatun jami'a
Asalin hoton, EPA
"Bayan da Taliban ta hana mata zuwa jami'o'i, burina ɗaya kawai shi ne na samu tallafin karatu da zai ba ni damar samun taimakon zuwa ƙasashen waje don yin karatu," a cewar wata ɗaliba 'yar ƙasar Afghanistan mai shekara 20.
Ɗalibar wadda muka canza mata suna da Natkai saboda tsaron lafiyarta, ta ce ta ci gaba da karatu duk da yake damar da take da ita ta yi karatun jami'a a ƙasar 'yar kaɗan ce.
Ƙungiyar Taliban sun shiga dirar mikiya a kan matan da ke adawa da matakan da suke ɓullowa da su.
Daga nan ɗalibar ta samu tallafin karatu a Jami'ar Dubai cikin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa daga hamshaƙin ɗan kasuwar ƙasar, Sheikh Khalaf Ahmad Al Habtoor.
A watan Disamban 2022 ne aka sanar da shirin ba da tallafin karatun bayan Taliban ta haramta wa mata zuwa jami'a.
BBC ta fahimci cewa jimillar mata 100 ne 'yan Afghanistan suka yi nasarar samun irin wannan tallafin karatu. Wasu ɗaliban Afghanistan da ke zaune a ƙasashen waje tuni suka fara tafiya Dubai.
A ranar Laraba 23 ga watan Yuli ne, Natakai ta yi sallama da iyayenta, inda ta kama hanyar zuwa filin jirgin sama.
Sai dai babu daɗewa sai burinta ya dusashe.
"Lokacin da jami'an Taliban suka ga tikiti da bizar tafiyarmu, sai suka ce an hana mata barin Afghanistan da bizar tafiya karatu," ta faɗa cikin shessheka.
'Ku dage sai kun yi cinikayya da naira tsakanin ku da China'
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, ...
Wani babban Lauyan Najeriya Femi Falana, ya yi kira ga ‘yan kasuwar Najeriya su dage wajen yin hada-hadar kasuwanci da Naira, ciki har da amfani da ita wajen biyan kuɗin kayan da ake shiga da su ƙasar daga China.
Tashar talbijin ta Channels ta ambato Falana na tunasar da 'yan Najeriya game da yadda gwamnatin ƙasar da China suka ƙulla yarjejeniyar musayar kuɗi shekara biyar da ta gabata.
Ya yi nuni da cewa, cinikin wanda ya kai RMB biliyan 16 ko kuma Naira biliyan 720, an yi shi ne don samar da isassun kuɗaɗen gida ga masu masana’antu na Najeriya da China da sauran ‘yan kasuwa, tare da rage matsalolin da ake fuskanta wajen neman dalar Amurka.
An kuma tsara musaya tsakanin ƙasashen biyu don inganta sauri da sauƙaƙawa, da yawan hada-hadar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.
Lauyan ya ƙara da cewa, duk da tabbatar da cewa yarjejeniyar har yanzu tana nan daram kuma tana aiki, amma har yanzu babban bankin Najeriya bai bar ‘yan ƙasar su yi kasuwanci a kasar China ta hanyar amfani da naira ba.
Lamarin da ya ce ya zama dole, inda ya bukaci ‘yan kasuwar Nijeriya su dage su rika hada-hadar kasuwanci da naira, ciki har da biyan kuɗin kayan da ake shiga da su daga kasar China.
Ko ni na tambaye ka fuloti a Abuja, kada ka ba ni - Tinubu ya faɗa wa Wike
Asalin hoton, BOLA TINUBU/ FACEBOOK
Bayanan hoto, ...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya buƙaci ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da kada ya ba shi wani fili a kyauta ko da ya nemi hakan.
Tinubu ya faɗi hakan ne a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na shekara-shekara a Abuja.
A maimakon haka, shugaban ya ja hankalin Wike da ya bayar da fifiko wajen kammala aikin hanyoyin cikin birnin Abuja domin ci gaban mazaunan birnin.
Yayin da yake gabatar da jawabin, Tinubu ya bayyana ministan babban birnin tarayya Abuja, a matsayin "mai gidan Abuja".
Tinubu ya ce manufarsa ba wai ya samu filaye kyauta ba ne, amma ya tabbatar da an samar da jirgin ƙasa wanda zai riƙa jigilar al'umma a birnin.
Wike dai ya riƙa haifar da muhawara tun bayan zama minista sakamakon alwashin da ya ci na rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba.
Ministan, yayin ziyarar gani da ido a ranar Laraba, ya ce ya kamata a kammala aikin layin jiragen kasa na Abuja (ARMT) nan da watanni takwas.
Likitocin Zamfara na barazanar rufe asibitocin gwamnati kan rashin albashi
Asalin hoton, Science Photo Library
Bayanan hoto, ...
Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Zamfara ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin mako guda ta biya ma’aikatan lafiya 17 albashinsu na wata hudu da sauran ma’aikatan lafiya a asibitin kwararru na Yarima Bakura ko kuma su shiga yajin aiki.
Shugaban NMA na jihar, Dakta Sanusi Bello, wanda ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin a Gusau, babban birnin jihar, ya kuma bayar da misali da albashin dukkan likitocin asibitin na watan Yuli 2023, da alawus na wata takwas ga kwararrun likitoci da ba a biya, wanda ya sa suka daina aiki.
Bello ya ce kungiyar ta yanke shawarar bayar da wa'adin mako guda ga gwamnatin jihar Zamfara domin ta magance wadannan bukatun.
Ya kara da cewa ƙungiyar a Zamfara za ta ci gaba da yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Litinin 4 ga Satumba, 2023, idan har gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.
Shugaban ya yi gargadin cewa matakin zai kai ga rufe dukkanin asibitocin da suka hada da asibitocin gwamnatin tarayya da asibitocin jiha da asibitoci masu zaman kansu da kuma janye duk wani aikin lafiya da na hakori da duk likitocin jihar Zamfara ke yi.
Likitoci dubu 54 ne kacal suka rage a Najeriya - Ƙungiyar Likitoci
Yadda tsadar rayuwa ta tilastawa likitocin Najeriya ficewa zuwa ƙasashen waje
Shugannin Somaliya sun lashi takobin murƙushe ƙungiyar al-Shabab
Yan majalisar dokokin Somaliya sun yi wani zama da ba saban ba inda suka jefa ƙuri'ar amincewa da ci gaba da amfani da ƙarfn soji wajen kawo ƙarshen ƙungiyar al-Shabab mai alaƙa da al-Qa'ida ta hanyar yaƙar ta matakin da suke kansa tun a watan Agustan bara.
'Yan majalisar tare da shugabannin gwamnati da na lardunan ƙasar daban-daban sun yi wani zama a babban birnin Dhusamareb a ranar Lahadi inda suka cimma matsayar ci gaba da yaƙar ƙungiyar.
Fadar shugaban Somaliya ta fitar da wata sanarwa a shafin X da a baya aka fi sani da Twitter, cewa sun amince su yi amfani da "tsarin yaƙi da ta'addanci na ƙasa da ƙasa" domin kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyar da ta jima ta na yi.
Ganawar na zuwa ne 'yan sa'a'o'i bayan da dakarun sojin ƙasar suka yi nasarar kama yankin Galgudud wanda nan ne al-Shabab ke da ƙarfin iko, abinda kuma kafafen watsa labarai ke cewa babban koma baya ne ga mayaƙan na al-Shabab.
Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, ya lashi takobin murƙushe ƙungiyar kafin nan da ƙarshen shekarar 2023.
Gabon ta dakatar da ayyukan gidajen yaɗa labaran Faransa a ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Gabon sun dakatar da gidajen yaɗa labarai na gwamnatin Faransa na wani dan lokaci da suka haɗa da TV5 Monde da France 24 da Radio France International (RFI).
Hakan ta faru ne saboda jami'ai na ganin tashoshin ba su nuna adalci da daidaito a lokacin babban zaben da ya gudana a ranar Asabar ba.
Gidan rediyon Faransa ya bayyana damuwarsa kan matsaloli bayan zaben, musamman saboda rashin intanet da kuma sanya dokar hana fita.
Wani mai magana da yawun gwamnati, Rodrigue Mboumba Bissawou, ya ce an rufe intanet da kuma sanya dokar hana fita ne saboda hana ƴaduwar tashin hankali bayan zaben.
A ranar Lahadin da ta gabata, kamfanin da ya mallaki gidajen talabijin din da aka dakatar, France Médias Monde ta ce "ta yi nadama kuma ta yi mamakin wannan dakatarwar ta wucin-gadi wanda hakan zai hana mutanen Gabon amintattun labarai da bayanai."
Har yanzu dai hukumar zaben Gabon ba ta sanar da sakamakon zaben ba.
An kuma dakatar da masu sanya ido kan zaɓe na kasashen waje da 'yan jarida daga yada labaran da suka jiɓanci zaben.
'Yan takara 19 za su fafata a zaben shugaban kasar Gabon
Abin da ya sa wasu kasashen da Faransa ta yi wa mulkin-mallaka ke shiga kungiyar kasashe renon Ingila
Sama da mutum dubu 24 ne suka ɓace ɓat a arewacin Najeriya - ICRC
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar bayar da agaji ta red cross ta ce sama da mutum 24,000 ne suka bace a Najeriya, akasari a yankin arewa maso gabashin kasar, sakamakon rikice-rikece da ake fama da su.
Hukumar ta ce Najeriya tana da sama da kashi 40 cikin 100 na mutanen da suka ɓace a Afirka.
Kamar a sauran sassa na duniya, ƴan Najeriya da dama sun ɓace ne saboda rikici da bala’o’i da kuma ƙaura zuwa sababbin wurare.
Dayawa daga cikinsu ba su koma garuruwansu ba shekaru da dama, kuma danginsu koyaushe suna cikin neman su.
Hukumar ta ƙara da cewa tana sane da iyalan da waɗanda suka ɓace, kuma za ta ci gaba da ƙoƙari don ba su amsoshi da suke buƙata.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa shiga Mariupol
Libya ta dakatar da ministar harkokin wajenta kan tattaunawa da Isra'ila
Asalin hoton, AFP
Libiya ta dakatar da Ministar harkokin wajenta daga aiki bayan wata ganawa da ta yi a birnin Rum na ƙasar Italiya da takwarar aikinta ta ƙasar Isra'ila a makon jiya.
Ƙasar Isra'la ta bayyana ganawar a matsayin ta tarihi da ke zama wani matakin farko na gina danƙon dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Amma jakadar ta Libiya, Najla al-Mangoush, ta ce ganawar na matsayin wadda ta zo bagatatan kuma ba a gwamnatance aka aiwatar da ita ba.
A yanzu gwamnatin Libiyar ta soma gudanar da wani bincike a kan Mis Mangoush, inda a cikin kwana uku rak za a miƙa wa Firaminstan ƙasar sakamakon binciken.
Majalisar ƙasa ta Libya da ta haɗa larduna uku na ƙasar ta bayyana cewa ba a abu ne me yuwa ba yin alaƙa tsakanin ƙasar da Isla'ila. wannan lamarin ya sa ofishin kakakin majalisar dokokin kasar ya zargi Najla al-Mangoush da laifin cin amanar ƙasa tare da kiran wani taron gaggawa a ranar Litinin.
Duk da ana ci gaba da samun ingantuwar dangantaka tsakaninin Isra'ila da kasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmi na duniya amma har yanzu babu wata hulɗar diflomasiyya tsakanin ta da Libiya
Ministoci: 'Tinubu zai iya korar duk wanda ya gaza'
Asalin hoton, STATE HOUSE
Bayanan hoto, ...
Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce shugaba Bola Tinubu ya shafe watanni tun bayan nasarar da ya samu a zaben ƙasar domin ya fitar da manyan manufofin kowane fanni na ƙasar kuma ba zai amince da gazawa daga kowane ne a cikin ministocinsa ba.
Ngelale, babban mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin.
Ya kuma jaddada cewa shugaba Tinubu ya kafa wasu ma'auni na musamman na aiki.
Ya ce “Tambayar a yanzu ita ce ta aiwatar da doka kuma shugaban kasa ya nuna kamar yadda ya yi a lokacin da yake gwamna a jihar Legas, cewa shi ba wanda ke tsoron korar kowa ba ne."
"Shi ba wanda ke tsoron sanya takunkumi cikin gaggawa don tabbatar da cewa an samu sakamakon da yake so ba ne."
Ngelale ya yi karin haske da cewa idan har gwamnatin za ta fuskanci gazawa, laifin ba zai hau kan ministoci kadai ba, maimakon haka, za a dangana ta ne ga shugaban kasa Bola Tinubu.
Ngelale ya kuma bayyana cewa daga lokacin da aka zabe shi zuwa lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, shugaban ya yi amfani da lokacin wajen kafa "jerin kwamitocin kawo sauyi a dukkan bangarori."
Ministocin a Najeriya: Su wane ne ƙusoshin gwamnatin Tinubu?