Yaƙin Sudan na neman ruguza ƙasar - MDD

Asalin hoton, AFP
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaƙin da ake yi a Sudan na neman durkusar da ilahirin ƙasar, tare da jefa ta cikin mummunan bala'i.
A tsakiyar watan Afrilu ne fada ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF.
MDD ta ce dubban yara ne ke fama da cutar tamowa, waɗanda ke cikin hatsarin mutuwa, sakamakon rashin samun abinci da magunguna.
Babban jami'in bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths,ya ce yunwa da cututtuka da kuma barin gidaje da mutane ke yi na barazana wargajewar Sudan.
Mista Griffiths ya ce matuƙar ba a kawo ƙarshen yaƙin ba, ilahirin ƙasar za ta iya rugujewa.
Cikin wannan makon ne Gidauniyar 'Save The Children' ta ce yaƙin ya tilasta mata dakatar da ayyukanta a ƙasar.
Gidauniyar ta ce fiye da ƙananan yara 30,000 ne suka rasa kulawa a ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar kuan 500.







