Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ministan tsaron Birtaniya ya gana da Badaru Abubakar

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Mukhtari Adamu Bawa

  1. LP ta musanta tattaunawa da PDP da NNPP domin dunkulewa

    Jam’iyyar Labour mai hammaya a Najeriya ta musanta batun tattaunawa da takwarorinta na PDP da NNPP domin samar da jam’iyya guda da za ta tunkari jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓe mai zuwa.

    Jam’iyyar ta Labour ta bayyana haka ne bayan da wasu daga cikin jaridun Najeriya suka rawaito cewar ana wata ganawa tsakanin ‘yan takarar shugabancin ƙasar na PDP Atiku Abubakar, da na NNPP Rabi’u Kwankwaso, da Peter Obi don haɗewa waje guda.

    Mai magana da yawun jam’iyyar Labour na ƙasa, Dr Tanko Yunusa ya ce iya abun da suka sani shi ne, akwai tattaunawa ta fahimta da ake yi tsakanin dan takararsu da na NNPP da na PDP, wanda kuma ba shi da alaka da batun samar da jam’iyya ko wani abu makamancin hakan.

    Haka kuma Dr. Tanko Yunusa ya ce ko da za a haɗe ɗin ma to sai dai a ba su jan ragamar ta fi da komai, kuma a sa su a gaba.

    • Zaɓen Najeriya 2023: Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya
  2. Emefiele zai sake gurfana a gaban kuliya

    Ana sa ran gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele zai sake bayyana a gaban kotu yau Laraba kan tuhumar wasu zarge-zargen da suka shafi almundahar kuɗi da ya kai kusan naira biliyan bakwai.

    Gwamnatin Najeriya ta kai ƙarar dakataccen gwamnan Babban Bankin gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja cikin makon da ya gabata domin fuskantar sabbin tuhume-tuhume.

    A makon da ya gabata ne ya kamata tsohon gwamnan bankin ya bayyana a gaban kotu, to amma hakan ba ta ba samu ba.

    Sakamakon roƙon da lauyan gwamnati Muhammed Abubakar ya yi wa kotun na ɗage zaman saboda ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Sa' adatu Yaro ba ta da lafiya.

    Gwamnatin Najeriya dai na zargin Emefiele da laifuka 20 da suka shafi almundahanar kuɗi da haɗin baki da bayar da cin hanci da fifita makusantansa.

  3. An sake buɗe sansanin NYSC a Maiduguri bayan shekara 13

    Hukumar yi wa Ƙasa Hidima ta Najeriya (NYSC) ta sake buɗe sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima da ke birnin Maiduguri na jihar Borno bayan kwashe shekara 13 da rufe shi.

    A shekarar 2011 ne aka rufe sansanin bayan ta'azzarar hare-haren 'yan ƙungiyar Boko Haram da ta yi wa jihar katutu a shekarun baya.

    Yayin bikin rantar da matasan masu yi wa ƙasa hidimar a sansanin, shugaban hukumar reshen jihar Mohammed Adamu ya yaba wa gwamnan jihar Babagana Umara Zulum kan jajircewarsa wajen sake buɗe sansanin.

    An dai buɗe sansanin ne na wucin-gadi a makarantar horas da malaman Arabiya cikin tsauraran matakan tsaro.

    Masu yi wa ƙasar hidima waɗanda suka hadar da maza 629 da mata 496 ne ke karɓar horo a sansanin.

    Gwamnan jihar ya bayyana farin cikinsa da sake buɗe sansanin da ke jihar, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna yadda zaman lafiya da tsaro a jihar bayan kwashe shekaru ana fama da hare-haren 'yan Boko Haram.

    • 'Tasirin da NYSC ta yi a rayuwarmu'
  4. Sauyin yanayi ne ke janyo gobarar daji - jami'an Canada

    Firimiyan yankin British Colombia na ƙasar Canada, ya ce ya yi amanna sauyin yanayi na daga cikin dalilan da suka janyo gobarar daji ta munanan a yawancin yammacin yankin Canada.

    David Eby ya ce matukar ba a dauki matakin rage dumamar yanayi ba, to za a ci gaba da ganin irin wannan gobara.

    Mista Eby ya yi kalaman ne a lokacin da ya kai ziyara cibiyar da ake taimakon wadanda suka rasa muhallansu a garin Kelona.

    Sama da mutum 3000 ne ke zaune a sansanin da ake taimaka wa mutane da abinci, da kayan sanyawa da barguna da sauran bukatun yau da kullum.

    Mutanen na nuna damuwa kan rashin sanin tsahon lokacin da za su kwashe a sansanin

  5. An buɗe rumfunan zaɓe a Zimbabwe

    An fara kaɗa ƙuri'a a Zimbabwe, inda 'yan ƙasar za su zabi sabon shugaban kasa da 'yan majalisu, da Kansiloli.

    Shugaba Emmerson Mnangagwa da jam'iyyarsa ta ZANU-PF na fatan ci gaba da rike madafun ikon kasar.

    Fafatawar za ta fi zafi tsakanin jam'iyya mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta CCC da Nelson Chamisa ke mata takara.

    Sama da 'yan Zimbabwe miliyan 6.5 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri'a a zaɓen.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta sha alwashin yin aikinta bisa doka domin tabbatar da ingantaccen zaɓe, ba tare da nuna wa wata jam'iyya wariya ba.

    A farkon makon nan Mista Chamisa ya shaida wa BBC cewa ya na da ƙwarin gwiwwar kawo ƙarshen jam'iyyar ZANU PF, bayan shafe sama da shekara 40 ta na murza zarenta a ƙasar

  6. Marabanku

    Masu bin mu a wannan shafi Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya.

    Barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba da Hausawa ke yi wa laƙabi da 'ta Bawa' rabar samu.

    Kuna iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.