Ministan Abuja, Mista Nyesom Wike ya musanta rahotannin cewa ya sayi wata danƙareriyar motar alfarma wadda harsashi ba ya huda ta, a kan kuɗi naira miliyan 300, ƙirar Lexus LX600 SUV bayan kama aiki a ranar Litinin.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Wike na musanta wannan labari, jim kaɗan bayan wata ziyara da ya kai tashar jirgin ƙasa na cikin birnin Abuja a ranar Laraba, inda ya duba gyare-gyaren da ake yi wa kayan aikin sufurin jirgin ƙasa na jigilar fasinja a birnin.
NAN ya ce wasu jaridun Najeriya ne suka wallafa hoton motar wadda harsashi ba ya huda ta, ɗauke da lambar Abuja. wato 'FCT - 01.
Rahotanni sun yi iƙirarin cewa motar, wadda kuɗinta ya haura naira miliyan 300, mallakar sabon ministan Abuja, Nyesom Wike ce.
Sai dai Wike ya ce labaran masu jamhuru ne kawai.
Ya nanata cewa an rantsar da shi ne ranar Litinin kuma ko zama bai yi ba don kama aiki gadan-gadan.
Ya dai ce abin da kawai ya yi bai wuce ganawar musayar ra'ayi da jami'an ma'aikatarsa a ranar Laraba ba, daga nan kuma sai suka rankaya tashar jirgin ƙasa don ganin yadda abubuwa suke.
“Na ga abin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, wai Babban Sakatare a hukumar raya birnin Abuja ya sayo min motar miliyan 300 da harsashi ba ya hudawa.
“Cikin mutuntawa, kamata ya yi mutane su yi hattara, kada su kassara rayuwar wasu,” in ji Wike.
Ya ce a lokacin da kama aiki, babban sakatare a ma'aikatar Mista Adesola Olusade ya faɗa masa cewa ma'aikatar tana da motocin da ministoci za su yi amfani da su.
“Kuma motar da muke hawa wannan ce (ya nuna wata mota ƙirar Lexus SUV).
“Ban taɓa amincewa a sayo min wata mota ba kuma ban yi amfani da wata motar hukuma wadda aka ƙera ta musamman ba.
Ya nemi 'yan jaridan da yake tare da su a wurin da cewa: "Ina son ku dubi motar da na zo da ita, wadda take da tuta a gaba, ku gani ko motar alfarma ce ta musamman".
A wani al'amari mai alaƙa da haka kuma, daraktan yaɗa labarai ga sabon ministan, Mista Anthony Ogunleye ya musanta iƙirarin wasu kafofin yaɗa labarai na cewa Nyesom Wike yana shirin ruguza gidaje har 6,000 a cikin unguwannin da ke Abuja, ciki har da ginin Wadata Plaza - shalkwatar babbar jam'iyyar adawar Najeriya.