Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ministan tsaron Birtaniya ya gana da Badaru Abubakar

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Mukhtari Adamu Bawa

  1. Bankwana

    To a nan ne, muka zo ƙarshen rahotanni da muke kawo muku tsawon wunin rana a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu - za mu dawo da sabbin labarai.

    Zubairu Ahmad Ƙasarawa da Mukhtari Adamu Bawa ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Kamata ya yi Birtaniya ta biya sama da fam tirliyan 18 diyyar cinikin bayi'

    Wani alƙalin Majalisar Ɗunkin Duniya ya ce ya kamata Birtaniya ta dauki alhakin biyan fiye da fam tirliyan 18 a matsayin diyya sakamakon rawar da ta taka wajen cinikin bayi zuwa Turai da Amurka.

    Wani rahoton bincike na haɗin gwiwa da alƙalin, Patrick Robinson ya gudanar, ya ce ya kamata Birtaniya ta biya dala tiriiyan 24 ga kasashen duniya 14 da ta bautar da jama'arsu a wancan lokaci.

    Amma Mista Robinson ya ce wannan adadin "na ƙasa-ƙasa" ne idan aka kwatanta da illar da cinikin bayi ya haifar. Ya bayyana mamakin yadda wasu ƙasashen da suka taɓa bautar da jama'a ke noƙewa.

    "Wajibi ne idan wata ƙasa ta aikata wani kuskure to a tilasta mata biyan wannan ɓarna da ta aikata" in ji Mista Robinson, wanda shi ne ya jagoranci shari'ar da aka yi ma tsohon shugaban Yugoslabiya, Slobodan Milosevic.

    Ya shaida wa BBC haka daidai lokacin da zai gabatar da jawabinsa a taron ranar Tunawa da Cinikin Bayi da Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Ɗunkin Duniya, UNESCO, ta keɓe.

  3. Wike ya yi alƙawarin kammala aikin jirgin ƙasan Abuja nan da wata shida

    Ministan Birnin Tarayya Abuja na Najeriya, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin magance ɗaya daga manyan matsalolin da mazauna birnin ke fuskanta a ɓangaren sufuri.

    Ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai domin ganewa idonsa aikin gyara tashar sufurin jirgin ƙasan fasinja ta cikin birnin Abuja.

    "Sufuri na ɗaya daga cikin ɓangarorin da muke son ingantawa don tabbatar da rage cunkoson ababen hawa a Abuja".

    Wike ya ce yana sane da cewa akwai babbar tashar layin dogo ta Abuja da a yanzu ba ta aiki, inda ya bayyana cewa zai tabbatar da ganin ta tashi don fara aiki gadan-gadan.

    Ya bayyana cewa akwai ɗumbin ayyuka da ba a kammala ba, kuma abin da mutane suka fi son gani shi ne waɗanda aka kammala kuma suke aiki.

    Ya ƙara da cewa babu hikima a fara sabon aiki, ba tare da kammala wanda aka tsoho ba.

    "Ina mai tabbatar wa jama'a cewa za mu kammala aikin gyara wannan layin dogo. Sannan kafin mu fara duk wani sabon aiki za mu duba waɗanne wurare ne ke fama da cunkoson ababen hawa don rage samun hakan".buƙatar," in ji shi.

    Wannan na ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da za mu kammala don ganin an fara amfani da shi nan wata shida"

    A cewar ministan birnin tarayyar, "A yanzu haka ma mun tanadi kuɗaɗen da za mu biya wannan kwangila". "Na ba Babban Sakataren birnin tarayya, Adesola Olusade, umurnin tabbatar da biyan ɗan kwangila da ke aikin".

  4. Bankin Duniya ya samar da turakun sola 103 a ƙauyukan Najeriya

    Hukumar Samar da Wutar Latarki a Karkara (REA) ta ce ta samu nasarar samar da turakun wutar lantarki daga hasken rana har 103 a duk faɗin ƙasar ƙarkashin wani Shirin Gwamnatin Najeriya na samar hasken lantarki ga jama'a.

    Hukumar ta ce Bankin Duniya ne ke ɗaukar nauyin shirin wanda an cimma gagarumar nasara wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito daraktan hukumar, Salihijo Ahmad, na bayyana hakan a lokacin wani taron tattaunawa kan samar da lantarki a yankunan karkara karo na 10, wanda aka gudanar ta kafar bidiyo da haɗin gwiwar wasu ƙwararru a fannin samar da hasken lantarkin a Abuja.

    Ya ce, "wannan muhimmn mataki ne da ya kai ga samun gagarumar nasara wajen inganta fannin samar da wutar lantarki a gidajen jama'a da kuma zai bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana'antu, wanda ci gaba ne a ɓangaren da ya shafi raya karkara musamman yankunan da aka bari a baya a Najeriya".

  5. Larabawan Isra'ila sun nemi a ɗauki mataki kan yawan kashe-kashen gilla

    Larabawan Isra'ila sun yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi wani zaman gaggawa, a wani jerin kashe-kashen gilla na baya-bayan nan a tsakanin al'ummominsu.

    A ranar Talatar nan ne aka harbe mutum huɗu a garin Abu Snan da ke arewacin Galilee, wanda galibin mazaunansa Larabawa ne. Uku daga cikin mutanen da aka harben, iyalai ne 'yan gida ɗaya, ɗayan kuma ɗan siyasa ne da ke takarar magajin gari.

    'Yan adawa na zargin gwamnati da kasawa wajen murƙushe ƙungiyoyi masu aikata miyagun laifuka.

    An dai gano gawawwakin mutanen huɗu ne yashe a cikin wata gona bayan an tabbatar da cewa sun mutu ne sanadin harbin bindiga.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashen mai suna Ghazi Saab, ɗan shekara 53 na daf da sanar da matakinsa na tsayawa takara a matsayin magajin garin yankin Abu Snan a ranar.

    Sauran su ne Zaher al-Din Saab mai shekara 45 da Amir Saab mai shekara 28 da kuma Salman Khala ɗan shekara 66 wanda ya fito daga wani gari mai suna Yarka.

  6. Ban sayi motar alfarma ta naira miliyan 300 ba - Wike

    Ministan Abuja, Mista Nyesom Wike ya musanta rahotannin cewa ya sayi wata danƙareriyar motar alfarma wadda harsashi ba ya huda ta, a kan kuɗi naira miliyan 300, ƙirar Lexus LX600 SUV bayan kama aiki a ranar Litinin.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ambato Wike na musanta wannan labari, jim kaɗan bayan wata ziyara da ya kai tashar jirgin ƙasa na cikin birnin Abuja a ranar Laraba, inda ya duba gyare-gyaren da ake yi wa kayan aikin sufurin jirgin ƙasa na jigilar fasinja a birnin.

    NAN ya ce wasu jaridun Najeriya ne suka wallafa hoton motar wadda harsashi ba ya huda ta, ɗauke da lambar Abuja. wato 'FCT - 01.

    Rahotanni sun yi iƙirarin cewa motar, wadda kuɗinta ya haura naira miliyan 300, mallakar sabon ministan Abuja, Nyesom Wike ce. Sai dai Wike ya ce labaran masu jamhuru ne kawai.

    Ya nanata cewa an rantsar da shi ne ranar Litinin kuma ko zama bai yi ba don kama aiki gadan-gadan. Ya dai ce abin da kawai ya yi bai wuce ganawar musayar ra'ayi da jami'an ma'aikatarsa a ranar Laraba ba, daga nan kuma sai suka rankaya tashar jirgin ƙasa don ganin yadda abubuwa suke.

    “Na ga abin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta, wai Babban Sakatare a hukumar raya birnin Abuja ya sayo min motar miliyan 300 da harsashi ba ya hudawa. “Cikin mutuntawa, kamata ya yi mutane su yi hattara, kada su kassara rayuwar wasu,” in ji Wike.

    Ya ce a lokacin da kama aiki, babban sakatare a ma'aikatar Mista Adesola Olusade ya faɗa masa cewa ma'aikatar tana da motocin da ministoci za su yi amfani da su. “Kuma motar da muke hawa wannan ce (ya nuna wata mota ƙirar Lexus SUV).

    “Ban taɓa amincewa a sayo min wata mota ba kuma ban yi amfani da wata motar hukuma wadda aka ƙera ta musamman ba. Ya nemi 'yan jaridan da yake tare da su a wurin da cewa: "Ina son ku dubi motar da na zo da ita, wadda take da tuta a gaba, ku gani ko motar alfarma ce ta musamman".

    A wani al'amari mai alaƙa da haka kuma, daraktan yaɗa labarai ga sabon ministan, Mista Anthony Ogunleye ya musanta iƙirarin wasu kafofin yaɗa labarai na cewa Nyesom Wike yana shirin ruguza gidaje har 6,000 a cikin unguwannin da ke Abuja, ciki har da ginin Wadata Plaza - shalkwatar babbar jam'iyyar adawar Najeriya.

  7. Harkar haɗa SIM-kad a Najeriya na samar wa ƙasar maƙudan kuɗi

    Ayyukan haɗa layin waya ko simkad ta bunƙasa a Najeriya inda darajar harkar, ta kai naira biliyan 55, shekara ɗaya bayan Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta hana shigar da simkad cikin ƙasar.

    Shugaban Hukumar, NCC, Farfesa Umar Danbatta ne ya sanar da haka lokacin taron da hukumar ta gudanar kan lamurran sadarwa a jihar Legas.

    NCC ta ce "hana shigar da SIM-kad ɗin ya taimaka wajen ragewa hukumar nauyi na neman canjin kuɗaɗen ƙetare, ya kuma samar da wata hanyar kasuwancin da ta kai naira biliyan 55 ga kamfanonin da ke samar da SIM-kad a Najeriya.

    Matakin kuma ya samar da ƙarin guraben aiki ga 'yan ƙasa".

    Ɗanbatta ya kuma ce, "hukumar ta NCC na cikin manyan sassan da ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, duba da irin jerin ci gaban ta sha samu".

    Ya ce, "babu tantama ɓangaren sadarwar Najeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen cire ƙasar daga koma-bayan tattalin arziki da ta taɓa fuskanta da kimanin kashi 12.45, a cikin wata uku na ƙarshen shekarar 2022".

  8. 'Sojoji sun ce ba za su mayar da Bazoum kan mulki ba'

  9. Ministan tsaron Birtaniya ya gana da Badaru Abubakar

    Ministan tsaron Birtaniyar, James Heappey MP, ya gana da manyan shugabannin tsaron Najeriya domin ƙulla alaƙar da za ta kai ga tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu da za ta kai ga duba lamarin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

    A lokacin ziyarar da ya kai Najeriya, Heappey ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a ranar Laraba da suka haɗa da Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, da kuma Hafsan Sojan Ƙasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

    Kazalika, ministan tsaron Birtaniyar samu ya ganawa da Ministan tsaron Najeriya, Abubakar Badaru, da kuma Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle.

    Ya kuma haɗu da Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yama (Ecowas) Omar Touray, inda ya nanata shirin ƙasarsa na tallafa wa ƙungiyar a ƙoƙarin da take yi na ganin an ci gaba da tattaunawar diflomasiyya domin mayar da tsarin dimukuradiyya a Nijar.

    Ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakan da Ecowas ɗin ke ɗauka a rikicin siyasar Nijar.

    "Muna tare da Ecowas wajen yin Allah-wadai da riƙe Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa, da ma sauran jami'an gwamnati, musamman a irin halin da ake ci gaba da tsare su. Don haka muna kira da a gaggauta sakin su".

  10. Likitoci sun yi dashen mahaifa na farko a Birtaniya

    A karon farko, likitocin fiɗa a Oxford cikin Birtaniya sun gudanar da dashen mahaifa.

    Matar da aka bai wa gudunmawar mahaifar mai shekara 34 ce, yayin da wata 'yar'uwarta mai kimanin shekara 40 ta tallafa mata da gudunmawar mahaifa.

    Dukkansu sun nemi a sakaya sunayensu.

    Likitoci dai sun ce su biyun sun warke sarai daga aikin tiyatar da aka yi musu.

    Rukunin likitoci guda 30 ne suka gudanar da aikin a watan Fabrairu, inda suka kwashe sa'a 17 suna aikin a asibitin Churchill.

    Tuni dai ƙanwar tana da ƙananan yara guda biyu, kuma dukkansu 'ya da ƙanwar suna zaune ne a Ingila.

    Likitan fiɗar mata, Farfesa Richard Smith, wanda ya jagoranci ayarin likitocin da suka ciro mahaifar, ya shafe tsawon shekara 25 yana bincike a kan aikin dashen mahaifa.

    Ya dai faɗa wa BBC cewa tiyatar wata "gagarumar nasara ce".

  11. Algeriya ta fara yunƙurin sasanta Ecowas da sojojin Nijar

    Babban jami'in diflomasiyyar Aljeriya ya fara wata ziyarar aiki zuwa kasashen yammacin Afirka ranar Laraba a wani yunkuri na neman mafita bayan juyin mulkin da aka yi a makwabciyarta Nijar

    Aljeriya ba ta goyon bayan duk wani matakin soji a Nijra.

    Shugaban ƙasar Abdelmadjid Tebboune ya buƙaci ministan harkokin wajen ƙasar Ahmed Attaf ya je Najeriya da Benin da Ghana domin tattaunawa da mahukuntan ƙasashen, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Aljeriya ta wallafa a shafinta na X.

    Ecowas ta ce watakila za ta yi amfani da karfin soji wajen mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, wanda sojojin ƙasar ke tsare da shi tun ranar 26 ga watan Yuli.

    Aljeriya mai iyaka da Nijar ta ce yin amfani da karfin sojoji ba zai magance matsalar ba, inda shugaba Tebboune ya ce hakan zai cutar da Aljeriya kai tsaye.

    Shugaban ƙasar ya yi imanin cewa Aljeriya ce ta farko da lamarin juyin mulkin Nijar din ya shafa.

    A ranar Talata ƙungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Nijar har sai an sake samun gwamnatin farar hula.

    Aljeriya ce kasa mafi girma a Afirka kuma tana kan iyaka da Libya da Mali, dukkansu suna fuskantar rikici tsawon shekaru.

  12. Gobarar dajin Girka na ci gaba da ɓarna

    Gobarar daji da ta yi sanadin mutuwar mutane 20 a kasar Girka na ci gaba da yin ta'adi ba tare da kakkautawa ba a tsaunin da ke kusa da Athens da yankin Evros da ke kan iyaka da Turkiyya.

    Daga cikin wadanda abin ya shafa, ana zargin 18 'yan gudun hijira ne da bakin haure da suka shiga kasar kwanan nan domin neman mafaka a dazukan arewacin birnin Alexandroupolis.

    Al'ummar kasar Girka sun mika sakon ta'aziyyarsu kan asarar rayuka da aka yi a dajin Dadia da ke kusa da kan iyakar Turkiyya.

    Tsawon kwanaki biyar, gobarar ta ƙona yankunan da ke kusa da birnin da kuma yammacin gabar teku.

    Jami’an kashe gobara na ci gaba da gwabzawa domin shawo kan gobarar da ke barazanar bazuwa daga gangaren Dutsen Parnitha zuwa arewa maso yammacin Athens.

  13. Su wane ne ƙusoshin gwamnatin Bola Tinubu?

  14. Kumbon da Indiya ta tura ya sauka kan duniyar wata

    Wani kumbo da Indiya ta tura yayi nasarar sauka duniyar wata, abin da ya sa Indiyar ta zama ƙasa ta hudu a duniya da ta yi nasarar yin hakan.

    A lokacin da yake shirin sauka kumbon mai suna Chandrayan 3 ya sassauta saurinsa har sai da ya kai saura mita ɗari daya tsakaninsa da doron watan sannan ya sauka cikin nasara.

    Dukkanin wannan an yi shi ne ta hanyar sarrafa kumbon daga nesa.

    Indiya ta samu nasarar yin hakan ne yan kwanaki bayan da Rasha ta yi yunkurin yin hakan amma ba tare da yin nasara ba.

    Firaiministan Indiya Narendra Modi ya ce gagarumin aikin ƙasar ya bayar da fifiko ga amfani da fasahar ɗan'adam don haka nasarar ta ƴan ƙasar ne da ƙasar.

    Daga bisani kumbon zai tura wata na'ura da za ta lalubo inda ake da ƙanƙara abin da zai ba shi damar kafa mazauni na dindindin bisa doron wata.

    • Chandrayaan-2: Kumbon Indiya zai fara shawagi a duniyar wata
    • Ƙasashen da za su yi rige-rigen zuwa duniyar wata a 2023
  15. Gwamnatin Najeriya za ta fitar da sabon kirarin ƙasar

    Ministar fasaha da harkokin ƙirƙire-ƙirƙire, Hannatu Musa - Musawa, ta buƙaci marubutan waƙoƙi da mawaƙa daga ko'ina cikin Najeriya su samar da wata waƙa ta musamman ga ƙasar.

    Ta ce tana ganin yana da mahimmanci a sami waƙar da ke wakiltar ƙasar gaba ɗaya.

    Ministar ta kara da cewa waƙar, wadda za ta zama sabon kirarin ƙasar, za ta taimaka wa mutane su ƙara yin imani da Najeriya da manufofinta

    A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na ministar ya fitar a ranar Talata, ta bayyana hakan ne jim kadan bayan naɗa ta a kan muƙamin.

    "A gaskiya ina son mu samu wani sabon take na musamman da ke wakiltar Najeriya, ina fata marubuta waka da masu kade-kade daga sassa daban-daban na kasar nan za su fara tunanin hakan." in ji sanarwar

    Hannatu Musawa ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin martabar Najeriya ta inganta.

    Ta ce bai kamata a san Najeriya da munanan abubuwa kamar talauci da zamba da ta’addanci ba.

  16. Akalla mutum 17 sun mutu saboda karyewar gadar jirgin kasa a Indiya

    Jami'ai sun ce akalla mutum 17 sun mutu sannan kuma ana fargabar ɓacewar wasu mutane da dama a wani mummunan lamari da ya faru a arewa maso gabashin Indiya yayin da wata gadar jirgin kasa da ake ginawa ta ruguje.

    Lamarin ya faru ne a kusa da Sairang, kimanin kilomita 20 (mil 12) daga Aizawl babban birnin jihar Mizoram, in ji babban ministan.

    Ma’aikata kusan 40 ne a wurin lokacin da gadar ta ruguje, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin rugujewar gadar ba.

    Babban Ministan Mizoram Zoramthanga, ya ce ma’aikatan gaggawa sun gano gawarwaki 17 ya zuwa yanzu yayin kuma da yawan mutanen yankin ke taimakawa wajen ayyukan ceton.

    • Daruruwa sun mutu a mummunan haɗarin jirgin kasa a Indiya
  17. Emefile bai bayyana a gaban kotu ba

    An sake fuskantar wani tsaiko a shirin gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a gaban kotu, dangane da zargin karkatar da naira biliyan 6.9.

    Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ba ta lissafa shari'ar da ake yi wa Emefiele cikin shari'un da za ta saurara yau Laraba ba.

    Lauyoyin Emefiele da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), wadanda su ne masu gabatar da kara, ba su halarci zaman kotun ba,

    Ba a dai bayar da dalilin da ya sa shari’ar ba ta cikin jerin shari'un da za a saurara a kotun ba.

    Hukumar DSS dai ba ta mayar da martani ga tambayoyin da BBC ta yi ba game da wannan lamari.

    A ranar Alhamis din da ta gabata, Emefiele ya bayyana a kotun amma kotun ta ɗage ƙarar saboda Sa’adatu Yaro, wata ma’aikaciyar babban bankin kasar, kuma wadda ke fuskantar tuhuma tare da Emefiele ba ta bayyana a kotun ba.

    Wannan ne ya sa mai shari’a Hamza Mu'azu, ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.

    Yaro da Emefiele suna fuskantar tuhume-tuhume 20 daga hukumar DSS, da suka hada da " zamba da hadin baki da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan hulda.

    Ana tuhumar Mista Emefiele da bai wa Sa'adatu Yaro, wadda take darakta a April 1616 Investment Ltd, wani kamfani da ake zargi da alaka da lamarin.

    • Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
  18. Faɗa na ci gaba da tsananta a kusa da sansanin soji a Khartoum

    An samu arangama mai ƙarfi tsakanin dakarun sojin Sudan da rundunar mayaƙan RSF, a kusa da sansanin soji da ke birnin Khartoum na ƙasar Sudan.

    Cikin wata sanarwa da sojojin suka wallafa a shafinsu na Facebook ranar Talata da daddare, sun ce sun daƙile wani hari da RSF suka kai sansanin soji da ke yankin Al-Shajara a kudancin birnin Khartoum.

    Sojojin sun kuma yi iƙirarin kashe da yawa daga cikin mayaƙan RSF ɗin.

    A nata ɓangare, mayaƙan na RSF sun ce sun ƙwace iko da wasu yankuna a sansanin tare da kama makamai masu dinbim yawa, cikin wata sanarwa da suka fitar a shafinsu na X da a baya aka fi sani da Twitter.

    Gidan talbijin na Al Arabiyya - da ƙasar Saudiyya ke ɗaukar nauyinsa - ya ce har yanzu sojojin ne ke iko da sansanin bayan kwashe kwana uku ana gwabza faɗa a sansanin.

    A 'yan kwanakin nan faɗa na ci gaba da rincaɓewa a birnin Khartoum da biranen Omdurman da Bahri da wasu yankunan yankin Darfur.

    Majalisar Dikin Duniya ta ce dubban mutane ne suka mutu, yayin da aka raba da sama da mutum miliyan huɗu da muhallansu tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin sojoji da dakarun RSF a tsakiyar watan Afrilu.

    • Rikicin Sudan: Shugabanni sun ɗauki aniyar kawo ƙarshen rikici
    • Me za a yi da gawawwakin mutanen da aka kashe a Khartoum?
  19. 'Gagarumin ɗan kirifto ya koma cin burodi da ruwa'

    Lauyan Sam Bankman-Fried, wanda ya samar da shafin kirifto na FTX - da ya rushe - ya ce Sam ya koma cin burodi da ruwa a gidan yari.

    Gidan yarin - da aka ajiye shi yayin da ake ci gaba da yi masa shari'a - ba shi da abinci mai inganci da Mista Bankman-Fried ke buƙata, kamar yadda lauyan nasa ya bayyana.

    A shekarar da ta gabata ne aka tuhume shi da laifuka bakwai da suka shafi zambatar mutane bayan da shafin kiriftonsa na FTX ya rushe.

    A lokacin zaman kotun da aka gabatar ranar Talata Mista Bankman-Fried ya musanta aikata laifi kan tuhume-tume bakwai d ake yi masa .

    Mista Bankman-Fried - wanda ake yi wa laƙabi da ''Sarkin Kirifto'' - ya hallara gaban kotun ne sanye da kayan fursunoni

    Lauyan tsohon biloniyan Mark Cohen, ya ce rashin wadataccen abinci a gidan yarin da Mista Bankman-Fried ke tsare na kawo tarnaƙi ga yadda suke shirya wa shari'ar, wadda aka tsara farawa cikin watan Octoba.

    Mista Cohen ya kuma koka kan rashin samun wadatattun magungunan da biloniyan ke buƙata a gidan yarin.

  20. Za mu bai wa maraɗa kunya a ɓangaren tsaro - Matawalle

    Sabon ƙaramin ministan tsaro na Najeriya Muhammad Bello Matawalle ya ce shi da takwaransa ministan tsaron ƙasar Muhammad Badaru Abubakar, za su bai wa maraɗa ƙunya a ɓangaren samar da tsaro a Najeriya.

    Yayin da yake jawabi a wani taron liyafa da Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta shirya masa don taya shi murnar samun matsayin a Abuja, Matawalle ya ce ya yi ta jin bayanai kan cewa shi da Badaru ba su da ƙwarewar da za su iya magance matsalar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

    Tsohon gwamnan na jihar zamfara ya ce masu faɗin wannan magana "ba su san me ake nufi da tsaro ba."

    ''To ba a nan gizo ke saƙar ba, domin kuwa za ka iya haifar ɗa, amma ya fi ka ƙwazo, ya fi ka hazaƙa, sannan ya fi ka ilimi''.

    Matawalle ya ce a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara babu abin da bai yi ba, domin daƙile matsalar tsaron da jihar ke fuskanta, inda ya ce an kwashe lokaci mai tsawo ba tare da samun labarin faruwar wani abu na tayar da hankali a jihar ba.

    Ƙaramin ministan tsaron ya ce ya ɓullo da matakai da dabarun yaƙi da 'yan bindiga a lokacin da yake gwamnan jihar ta Zamfara.

    ''Duk matakan da na riƙa ɗauka domin magance matsalar tsaro a zamfara, sai na yi wasu gwamnoni su ɗauka''.

    Bello Matawalle na daga cikin ministocin da za su fuskanci babban ƙalubale a ma'aikatunsu, sakamakon yadda tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar, kama daga ayyukan 'yan fashin daji a arewa maso yamma, da Boko Haram a arewa maso gabas, ga kuma matsalar 'yan awaren IPOB a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

    • Manyan ƙalubalan da ke gaban sabbin ministocin tsaron Najeriya
    • 'Yadda 'yan bindiga suka sace mana zawarawa da 'yan mata 23 a Zamfara'