Ba mu da nufin komai sai alheri ga 'yan Najeriya - Remi Tinubu

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Mukhtari Adamu Bawa and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Za a fara sakin gurɓataccen ruwa daga tashar nukiliya ta Fukushima

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Firaiministan Japan, Fumio Kishida, ya sanar da cewa daga ranar Alhamis za a fara sakin gurbataccen ruwa daga tashar makamashin nukiliya ta Fukushima.

    Za a zubar da ruwan da ya kai yawan tan fiye da miliyan daya daga tashar zuwa tekun Pacific.

    Wani da ke adawa da sakin ruwan ya bayyana cewa sakin ruwan bashi da wata matsala, amma ba su yi wani gwajin kimiyya a kan hakan ba.

    Matakin sakin ruwan wanda hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a watan da ya wuce, ya fuskanci suka daga China da wasu 'yan Japan da Koriya ta Kudu.

  2. Za mu haramta kiwo a kan titunan Abuja - Wike

    ..

    Asalin hoton, RVGH

    Bayanan hoto, ...

    Jim kaɗan bayan kama aiki, sabon ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwon sake a Abuja.

    Ministan ya kuma ce zai tuntuɓi makiyayan a kan wannan batu.

    Wike ya bayyana haka ne lokacin ganawa da manema labarai a ranarsa ta farko a ofis, yayin da ya sha alwashin tsaftace Babban Birnin Tarayyar.

    Sabon ministan ya ce makiyaya za su iya kiwon shanu a wajen birnin amma kuma ba za a bari su ci ciyawar da ake amfani da ita wajen ƙawata birnin ba.

    “Za mu tuntubi makiyayan domin mu ga yadda za mu daina kiwon sake saboda ba za mu iya barin shanu a cikin garin Abuja ba,” in ji shi.

    Wike ya ce an dasa ciyayin ne a birnin domin ƙawata shi ba domin shanu su ci ko su ɓata ba.

    • Ko Fulani Makiyaya na bin dokar hana kiwon sake a kudancin Najeriya?
  3. Sojojin Najeriya sun ceto ƴar makarantar Chibok bayan shekara 9

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok, wadda mayaƙan Boko Haram suka sace bayan shafe shekaru tara a hannunsu.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa an yi nasarar ceton ne a garin Maiduguri na jihar Borno, kuma an gabatar da ita a hedikwatar rundunar Operation Hadin Kai a ranar Litinin.

    Dalibar, wadda ita ce ta hamsin da biyar a jerin ‘yan makarantan da aka sace, ta bayyana cewa mijinta na Boko Haram, ne ya taimaka mata wajen tserewa bayan miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

    Ta kuma shaida wa gidan talabijin din cewa ta haifi ƴaƴa biyu ga mijinta dan Boko Haram sai dai duk sun rasu.

    Kwamandan sojojin, Manjo Janar Gold Chibuisi, ya bayyana cewa an miƙa ɗalibar a asibitin sojoji domin kula da lafiyarta, domin tabbatar da cewa tana cikin ƙoshin lafiya.

    Ya ce za a miƙa ta ga gwamnatin jihar domin sada ta da iyalanta.

    • Ina aka kwana kan ceto ƴanmatan Chibok bayan shekara tara?
    • 'Yan Boko Haram sama da dubu da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin Najeriya
  4. Shugaban Wagner ya iso Afirka ne?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Wagner, Yevgeny Prigozhinya ya fitar da bayani na farko ta faifan bidiyo bayan rashin nasarar boren da ya jagoranta a watan Yuni.

    Magoya bayan kungiyarsa sun nuna cewa an dauki bidiyon ne a wata kasa da ke Afirka.

    An fara wallafa bidiyon ne a tashar telegram mai alaka da kungiyar Wagner "Razgruzka Vagnera" a yammacin ranar 21 ga Agusta.

    An nuna Prigozhin sanye da kayan soja mai tambarin kungiyar Wagner a ƙirjinsa, ana kuma iya ganin sa yana dauke da bindigar Kalashnikov na musamman a lokaci guda.

    A cikin faifan bidiyon, Prigozhin ya bayyana cewa, "Manufarmu ita ce daukaka martabar kasar Rasha a dukkan nahiyoyi! Da kuma inganta 'yancin Afirka."

    Ya kara da cewa, "Muna kokarin tabbatar da adalci da jin dadin al'ummar Afirka."

    Har yanzu dai ba a tabbatar da sahihancin wannan ikirarin ba.

    • Da gaske ne mayaƙan Wagner sun isa Nijar?
    • Shin me juyin mulki Wagner ke yunƙurin yi wa Putin?
  5. Tsohon firaministan Thailand ya koma ƙasarsa bayan gudun hijira

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Tsohon firaiministan Thailand, Thaksin Shinawatra ya koma ƙasarsa bayan shafe shekaru 15 yana neman mafaka biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

    Ya isa Thailand da safiyar Talata a cikin wani jirgin sama, gabanin zaben shugaban kasar wanda ke kan gaba daga jam'iyyarsa ta Pheu Thai.

    Da yawa daga cikin magoya bayansa sun je filin jirgin saman Bangkok don tarbarsa.

    An dai kai tsohon firaiminitsan kotun kolin kasar, wadda zata yanke hukunci akan daurin da za a yi masa a lokacin da baya nan, abin da ya bayyana matakin da bita da kullin siyasa.

  6. Joe Biden ya je ziyarar jaje ga mutanen da gobarar daji ta yi wa ɓarna

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Amurka, Joe Biden, ya kai ziyarar jaje ga jajirtattun mutanen Maui inda ya ziyarci wuraren da suka fuskanci mummunanr wutar daji a tsibirin Hawaii a farkon watan da ake ciki.

    Mr Biden ya ce ƙasar zata basu dukkan goyon baya da taimakon da suke bukata.

    Sannan ya yi alƙawarin cewa za a sake gina garin Lahaina mai tarihi wanda wutar dajin ta ƙona, da kuma samar da dukkan ababan more rayuwar da ake bukata a garin.

    Wakilin BBC ya ce an yi ta sukar shugaban saboda kwasar kwanaki bai ce komai ba game da mummunar wutar dajin, sannan kuma da rashin yin abin da yakamata a kan lokaci wajen kai kayan agaji a Maui.

    • Wutar daji ta ƙone wani gari ƙurmus a Amurka
    • Jiya da yau: Bala'in gobarar dajin da ke addabar duniya
  7. Rasha ta kakkaɓo jiragen Ukraine marasa matuƙa

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce ta dakile wani hari da jirage maras matukin Ukraine suka kai mata.

    Ta ce an harbo jiragen biyu kasa , yayin da wasu biyu kuma suka fada a iyakar Rashan da Ukraine da ke arewa maso gabas.

    Tun da farko wasu rahotanni sun ce an dakatar da zirga zirgar jiragen saman da za su je Rasha ko kuma za su tashi daga Rashan.

    To amma daga baya an bude filayen jiragen saman Sheremetyevo da Domodedovo da ke Rashan.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na kai tsaye, barkan mu da war haka.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Talata domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya lekawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu.