Wike ya yi barazanar rusa gidaje a ranarsa ta farko a ofis

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotanni kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Talata - idan Allah ya kai mu za mu dawo da sababbi.

    Ahmad Tijjani Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Juyin mulkin Nijar zai shafi yara sama da miliyan biyu - UNICEF

    Nijar

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce rikicin da Jamhuriyar Nijar ke ciki, tun bayan da aka hamɓarar da shugaban ƙasar a watan Yuli, zai shafi miliyoyin yara ƙanana.

    Wata sanarwa da wakiliyar ta UNICEF a Nijar, Stefano Savi, ta fitar, ta ce halin da ake ciki a ƙasar abin damuwa ne da ke ƙara jefa ƴan ƙasar cikin halin ƙaƙaniƙayi da ya saka su buƙatar jin ƙai na gaggawa.

    Sanarwar ta ce rikicin zai shafi kimanin sama da yara miliyan biyu.

    Savi ta ce akwai matukar damuwa ganin yadda ake ci gaba da fuskanatar ƙarancin wutar lantarki a ƙasar, wadda da ita ne ake amfani wajen ajiye alluran rigakafi na yara.

    Haka kuma ta sake nanata damuwar da ake da ita kan yadda har wasu kwantenoninta 21 da ke ɗauke da kayan ceton rai suka maƙale a kan iyakar Nijar da Benin, sannan akwai wasu 29 da za a shigo da su Nijar da ke kan teku ɗauke da abincin gaggawa da sirinji.

    "Muna kira ga Nijar da ECOWAS da su tabbatar da rikicin da suke da juna bai haifar da cikas ba ga ayyukan jin ƙai ga iyalai da yara ƙanana da ke buƙatar kulawa ta gaggawa," in ji Savi.

    Ta buƙaci a bai wa shirye-shiryen jin ƙai da ake gudanar da su a Nijar ɗin kariya daga dukkan wani takunkumi.

    UNICEF ta ce tun ma kafin samun rikici a Nijar, akwai kusan yara miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar da ke da shekaru ƙasa da biyar da aka yi kiyasin suna fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

    Jamhuriyar Nijar da ke yankin sahel na cikin ƙasashen duniya da ke fama da tarin matsaloli da kuma talauci.

  3. Ƴan Siriya sun gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da matsin tattalin arziki

    Ɗaruruwan ƴan Siriya ne suka gudanar da zanga-zangar nuna damuwa da matsin tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta a birnin Sweida.

    Zanga-zangar ita ce ta baya-bayan nan da aka gudanar a kudancin Siriya.

    Lamarin ya ƙara ƙamari ne bayan da gwamnatin ƙasar ta janye tallafin man fetur.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙa rera baitocin da suka haɗa da 'ki daɗe kiyi ƙarko Siriya', a sauke shugaba Assad.

    Birnin Sweida na daga cikin manyan biranen da ƙabilar Druze larabci marasa rinjaye a Siriya ke da yawa, kuma yana cikin biranen da rikicin da aka kwashe shekaru goma sha biyu ana yi a ƙasar bai shafa ba.

  4. An samu gawar jakadan Faransa a Kamaru

    Karamin ofishin jakadancin Faransa a Douala, babban birnin Kamaru, ya tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin manyan jami'ansa Christian Hué.

    Wata sanarwa da ofishin ya fitar, ta ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar jami'in.

    Hué ya kasance shugaban ofishin jakadancin kuma an yi ta yaɗa jita-jitar mutuwarsa a Kamaru a ƴan kwanakin nan.

  5. Sojoji sun sake 'ceto' wata 'yar Chibok

    Sojoji

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar ceto wata ƴar makarantar Chibok Mary Nkeki ‘yar shekara ashirin da bakwai bayan shekara tara da sace ta.

    An gabatar da ita a hedikwatar Operation Haɗin Kai da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Litinin.

    Mary ta ce ɗan Boko Haram da ya aureta mai suna Adam ya taimaka mata wajen tserewa bayan ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

    Ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ta haifi ‘ya’ya biyu ga mijin nata amma duk sun mutu.

    Ita dai Marya wadda ta samu ‘yanci a yanzu, ta ce tana soyayya da mijinta wanda ya kasance ɗan Boko Haram kuma za ta so sake haɗuwa da shi.

    "Mijina yana raye kuma ina son shi har yanzu. Ban san ko yana Dikwa har yanzu ba ko kuma an dawo da shi Maiduguri, amma zan so mu sake haɗuwa idan haka zai yiwu," in ji ta.

    Kwamandan rundunar sojojin a Maiduguri Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ce sun ceto Mary ne a ranar 14 ga watan Agusta.

    Ya ce zuwa yanzu, sun ceto ƴan matan sakandaren Chibok 16 tun fara wannan shekara ta 2023.

  6. Ukraine ta tarwatsa wani jirgin luguden bam ɗin Rasha

    Russian Bomber

    Asalin hoton, X (TWITTER)

    Rahotanni sun ce Ukraine ta tarwatsa wani jirgin luguden bam ɗin Rasha a wani harin jirgi maras matuki da ta kai.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta wanda kuma BBC ta gani sun nuna wani jirgi kirar Tupolev Tu-22 yana cin wuta a tashar jiragen saman Soltsy-2, a kudancin St Petersburg.

    Moscow ta ce hare-haren wani jirgin maras matuki ya lalata wani jirgi. Ukraine dai ba ta ce komai ba.

    Jirgin Tu-22 na iya gudun da ya ninƙa saurinsa sau biyu kuma Rasha ta yi amfani da shi sosai wajen kai hari a biranen Ukraine.

    Ma'aikatar tsaron ƙasar Rasha ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa an kai wani hari da wani makami mai linzami samfurin 'Copter UAV' da misalin karfe 10 agogon ƙasar.

    Sanarwar ta ce wurin da aka kai harin ya kasance filin jirgin sama na soja a yankin Novgorod", inda Soltsy-2 yake.

  7. Hotunan yadda ambaliya da guguwa suka ɗaiɗaita sassan Amurka

    Guguwa tare da ambaliya na ci gaba da ɗaiɗaita wasu jihohin Amurka.

    Ambaliyar ta sanya an rufe hanyoyi da dama, bayan samun mamakon ruwan sama haɗe da tsawa cikin dare.

    Lamarin ya shafi jihar California da Vermont da Texas da kuma garuruwa irin Houston da Illinois.

    Ambaliya

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Ambaliya

    Asalin hoton, EPA

    Ambaliya

    Asalin hoton, Shutterstock

    Guguwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ambaliya

    Asalin hoton, EPA

    Guguwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Ambaliya

    Asalin hoton, EPA-EFE

  8. Mutum 620 sun mutu sakamakon yajin aikin ma'aikatan lafiya a Mozambique

    Mozambique

    Aƙalla mutum 620 sun rasa rayukansu a cikin kwanaki 40 da suka gabata sakamakon yajin aikin da ma’aikatan lafiya a Maputo, babban birnin Mozambique ke yi.

    Wannan ne karon farko a tarihin ƙasar da likitoci suka haɗa kai wajen gudanar da yajin aikin, inda suka zaɓi tsawaita zanga-zanga na tsawon kwanaki 21 duk da barazar kisa da aka yi musu.

    Sai dai likitocin sun yi alkawarin bai wa marasa lafiya kula da ƙankanin lokaci don rage musu raɗaɗin da suke ciki.

    Ma'aikatan lafiyar sun ce sun shiga yajin aikin ne saboda ba su da magunguna da kayan aiki masu mahimmanci - sun ce ta kai ga su ke biya daga aljihunsu don tara motocin ɗaukar marasa lafiya da kayan masarufi.

    Cikin buƙatu da suka nema har da son tsige ministan lafiya Armindo Tiago.

    Sai dai gwamnatin ƙasar ta bayyana nadama kan matakin da likitocin suka ɗauka na tsawaita yajin aikin da suke yi, duk da cewa ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen magance korafe-korafensu.

  9. Wanne hali Abdulrasheed Bawa ke ciki?

  10. Greenwood zai bar Man United bayan zargin cin zarafi

    Mason Greenwood

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta cimma yarjejeniya da Mason Greenwood cewar ba zai ci gaba da taka leda a kungiyar ba.

    Sun cimma wannan matsaya, bayan wata shida da aka yi kan wasu halayyarsa ta rashin kyautawa.

    An tsare Greenwood a Janairun 2022, bayan zargin da ake masa kan wasu abubuwa da ya wallafa a shafinsa na Intanet.

    Cikin zargin da ake yiwa dan wasan mai shekara 21 har da kokarin fyade da cin zarafi.

    Daga baya aka soke dukkan zarge-zargen da ake masa ranar 2 ga watan Fabrairun 2023.

    United ta sanar da jawabin cewar: ''Ta san halin da Mason ya fada da ta kai ta shafi rayuwwarsa ta tamaula a Manchester United''.

    Shi kuwa Greenword cewa ya yi ''Na karbi kuskuren da nayi, amma ban yi abin da ake zargi na da shi ba''.

    Tun farko an ware ranar 14 ga watan Agusta, don fayyace makomar Greenwood a Old Trafford a Premier League.

    A ranar ta bude wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila, United ta yi nasara da cin Wolves 1-0, sai dai ta yi rasshin nasara da ci 2-0 a gidan Tottenham ranar Asabar.

  11. Shettima zai wakilci Tinubu a taron ƙasashen BRICS a Afrika ta Kudu

    Shettima

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Afrika ta Kudu domin wakiltan shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen BRICS karo na 15 da za a yi.

    Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da ƴan kasuwa a faɗin duniya domin halartar taron a Afrika ta Kudu wanda zai gudana daga 22 ga watan Agusta zuwa 24.

    Taron zai tattauna ne kan batutuwan da suka shafi kasuwanci, saukaka zuba jari, samun ci gaba, kirkire-kirkire da kuma garanbawul na yadda ake shugabanci a faɗin duniya.

    Har ila yau, taron zai duba batun ci gaba da tallafawa ƙasashen Afrika da kuma kudancin duniya.

    Manyan shugabanni da za su halarci taron sun haɗa da Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Shugaba Xi Jinping na China, Shugaban Brazil, Luiz da Silva da kuma Firaministan Indiya Narendra Modi.

    Shettima

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    An kuma gayyaci Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Shugaban Hukumar Tarayyar Afrika da kuma Shugaban Sabon Bankin Ci gaba.

    Ƙasashen na BRICS dai sun kunshi Brazil, Rasha, China, Indiya da kuma Afrika ta Kudu, waɗanda suka kasance manyan ƙasashe da ke kawo karfi da kuma masu tasowa.

    Al'ummar ƙasashen ya kai kashi 42 na yawan al'ummomi a faɗin duniya da kuma ke da kashi 23 na tattalin arziki.

  12. Giwar da ta fi tsufa a Indiya ta mutu

    ...

    Asalin hoton, ANI

    Bijuli Prasad, giwa mafi tsufa a Indiya, ta mutu tana da shekara 89 a gundumar Sonitpur ta Assam.

    A cewar kamfanin dillancin labarai na PTI, giwar ta mutu ne da karfe 3:30 na safe a cikin wani lambun rukunin gidaje na Behali ranar Litinin

    Jama'a da dama da ke aiki a cikin lambun noman shayin sun taru don nuna alhininsu game da mutuwar giwar.

    Wani jami’in lambun shayi ya ce an kawo giwar tun tana ƙarama kuma daga baya ta isa kungiyar Williamson Megar bayan an sayar da gonar.

    Shahararren likitan giwaye, Dr. Kushal Konwar Sarma, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na PTI cewa shekarun da giwar ta yi a duniya wani abu ne na ban mamaki.

    Ya jaddada cewa, yayin da giwayen daji na Asiya ke rayuwa kusan shekara 62-65, giwayen gida da aka kula da su sosai za su iya rayuwa har tsawon shekara 80.

    Likitan ya ƙara da cewa kusan shekara goma da suka gabata, haƙoran Bijuli Prasad sun ƙarye, wanda hakan ya hana ta cin abinci da kuma yin barazana ga rayuwar ta.

    Ya kuma bayyana cewa hakan ta sa ya canza abincin da ake bai wa giwar kullum wanda ya ƙunshi dafaffiyar shinkafa da waken suya mai wadataccen sinadarin furotin.

  13. Sabon ministan Abuja ya yi alƙawarin inganta tsaro a babban birnin

    Wike

    Asalin hoton, RVGH PRESS

    Sabon ministan Abuja, Mista Nyesom Wike ya ci alwashin inganta tsaro a babban birnin na Najeriya, jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da shi a kan muƙaminsa.

    Tsohon gwamnan na jihar Ribas, ya bayyana takaici kan taɓarɓarewar tsaro a babban birnin, inda ya ce kamata ya yi Abuja ta kasance, birni mafi aminci a Najeriya.

    Ya bayyana damuwa kan yadda ake zaman ta-ci-barkatai a sassan birni.

    A cewar Wike, wanda ke jawabin kama aiki tare da jami'an ma'aikatar babban birnin, sabon ministan ya ce ba zai lamunci yadda ake kasa kaya a kan titunan Abuja, ba tare da bin tsari ba.

  14. An yi wa malamar jinya ɗaurin rai da rai bisa laifin kashe jarirai a Birtaniya

  15. Uba Sani ya rage kuɗin makaranta a manyan makarantun Jihar Kaduna

    Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani

    Asalin hoton, TWITTER/ SEN UBA SANI

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin rage irin wahalhalun da tsadar kuɗin makaranta ke haifarwa ga al'ummar jihar.

    Sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari na kuɗin makaranta da ɗalibai ke biya a jami'ar jihar Kaduna, wato KASU.

    Haka nan an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.

    Bugu da ƙari sanarwar ta ce an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a Kwalejin ilimi ta jihar da ke Gidan Waya.

    Yayin da aka yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai masu karatun babban difiloma ke biya a Kwalejin koyar da harkokin lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi, inda su ma masu karatun difiloma za su samu ragin kashi talatin cikin ɗari.

    A ƙarshe sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin koyon jinya ta jihar.

  16. Wike ya yi barazanar rusa gidaje a ranarsa ta farko a ofis

    ...

    Asalin hoton, RVGH PRESS

    Bayanan hoto, ...

    Sabon ministan babban birnin tarayyar Najeriya - Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fara rusa gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba.

    Wike ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi domin soma aiki.

    "Idan kun gina gidajenku a wuraren da aka saba ka'ida, sai an rusa su," in ji Wike.

    Tsohon gwamnan Ribas din yana cikin ministoci 45 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da su a fadarsa da ke Abuja.

    Wike ya sha alwashin yin tir da tsarin da ke kawo cikas ga taswirar babban birnin tarayyar.

  17. Ƙungiyar ƙwadagon Ghana na adawa da tura sojoji Nijar

    ...

    Kungiyar Kwadago mafi girma a Ghana ta yi gargadi kan yin amfani da karfin soji wajen kawo karshen juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.

    Kungiyar ta tabbatar da cewa, hanyoyin diflomasiyya za su iya dawo da tsarin mulki a Nijar matukar shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) suka tattauna da gwamnatin soja ta hanyar da ta dace.

    Sakatare-janar na ƙungiyar ƙwadagon, Yaw Baah ya bayyana cewa, "Mun yi imani da gaske cewa duk wani yunkuri na tilasta wa gwamnatin mulkin soji da Tchiani ke jagoranta a Nijar zai kara dagula al'amura da rashin tsaro a yankin."

    Kungiyar Ecowas da ke yammacin Afirka ta bayyana yiwuwar daukar matakin soji kan gwamnatin mulkin soja da ta hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

    Yayin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta bayyana aniyarta ta nayar da mulki ga farar hula cikin shekara, lamarin da kungiyar ta Ecowas ta ƙi amincewa da wannan shawara.

    Dangane da juyin mulkin, Ecowas ta kakaba wa Nijar takunkumi, wanda ya yi tasiri ga tattalin arzikin kasashe makwabta, kamar Ghana.

    ‘Yan kasuwar Ghana sun bayyana kalubalen da suke fuskanta wajen shigo da kayan lambu musamman albasa daga Nijar, lamarin da ya janyo tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ghana dai ta dogara ne kacokan a kan Nijar da kusan kashi 70 cikin dari na albasarta da take shigowa da ita.

    A shekarar 2021, Nijar ta fitar da albasar kusan dala miliyan 23 zuwa Ghana da sauran kasashen yammacin Afirka.

  18. Ana zanga-zangar ƙyamar cin hanci a kotunan zaɓe na Kano

    ...

    Wasu kungiyoyin fararen hula a Kano sun gudanar da zanga-zangar nuna kyamar zarge-zargen cin hanci da rashawa da ya dabaibaye kotunan sauraren kararrakin zabe.

    A makon da ya gabata ne taƙaddama da ɓarke, bayan Mai shari'a Flora Ngozi Azinge, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen 'yan majalisun tarayya da na jihar Kano, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.

    ..

    Rahotanni dai sun ambato Mai shari'a Flora Azinge na cewa karo na biyu ke nan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.

    ..

    Manyan jam'iyyun siyasar jihar guda biyu NNPP mai mulki da APC, babbar mai hamayya a Kano suna nuna wa juna yatsa.

  19. Somaliya ta haramta amfani da tik-tok

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Somaliya ta dakatar da kafofin dandalin sada zumunta na TikTok da Telegram, tare da shafin caca na 1XBet.

    Dalilin da ya sa gwamnatin kasar ta dauki wannan mataki shi ne ikirarin cewa "kungiyoyin 'yan ta'adda da kungiyoyin da ke da hannu wajen yada abubuwan da ba su dace ba" suna amfani da wadannan kafafen yada labarai ne wajen yaudarar jama'a.

    Wannan ya zo ne daidai lokacin da Somaliyya ta bayyana kudurinta na fatattakar mayaƙan al-Shabab, wadanda ke ci gaba da rike madafun iko a wasu sassa na kasar da kuma burin cimma wannan gagarumin buri a cikin watanni biyar masu zuwa.

    Ma'aikatar sadarwa da fasaha ta ƙasar ta umarci kamfanoni masu samar da intanet da su aiwatar da dokar kafin ranar 24 ga watan Agusta inda suka ce rashin yin biyayya zai iya haifar da matakin shari'a da ba a fayyace ba.

    A yayin wani taro na baya-bayan nan kan harkokin tsaro na intanet da na sada zumunta da aka gudanar a birnin Mogadishu, babban birnin kasar, an yi nuni da irin illar da shafukan intanet ke yi wa matasa kuma sun taimaka wajen asarar rayuka.

  20. Kashin ministoci na karshe da suka sha rantsuwa

    ...

    Asalin hoton, Presidency

    Bayanan hoto, ...

    Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli – Bello M. Goronyo

    Karamin Karafa – U. Maigari Ahmadu

    Ministan harkokin 'yan sanda - Ibrahim Geidam

    Ministan tsaro - Bello Matawalle

    Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnatoci - Zephaniah Jisalo