Rasha ta gargaɗi Ecowas kan tura sojoji Nijar

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Rabiatu Kabir Runka

  1. An sallami Zuma daga gidan yari saboda rage cunkoso

    Zuma

    Asalin hoton, Reuters

    Tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya tsallake ƙarin hukuncin zaman gidan yari, bayan samun yafiya.

    Ana bayar da irin wannan yafiya ne ga mutanen da ba za su zama barazana ga tsaro ba.

    Ministan shari'a Ronald Lamola ya shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa an ɗauki matakin yafiyar ne domin rage cunkoso a gidajen yari. Ya ce yafiyar ta fara aiki ne daga watan Afirilu.

    Zuma ya miƙa kansa ga gidan yarin Escout da ke KwaZulu-Natal da safiyar Juma'a kuma hukumomi sun karɓe shi.

    Bayan sa'a guda kuma aka sake shi bisa tsarin yafiya ta musamman.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ne ya amince da yafiya ga fursunoni 9,000 waɗanda hukumomi suka tabbatar ba su da barazana ga tsaron ƙasa.

    A watan Yunin 2021 aka yanke wa Zuma hukuncin zaman gidan yari na wata 15, bayan kama shi da laifin ƙin amsa gayyatar kotun da ke binciken zamanin mulkin sa.

    Daga baya aka sallame shi daga gidan yarin domin ya samu damar ganin likita, bayan an tsare shi na tsawon wata biyu.

  2. Wutar daji ta ƙone wani gari ƙurmus a Amurka

    Mau

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnan Hawaii ya ce akwai yiwuwar wutar dajin da ke ci a tsibirin Mau ta haifar da mummunan bala'i a tarihin jihar da ke Amurka.

    Josh Green ya bayyana irin mummunar asarar da wutar ta haddasa a matsayin abin tashin hankali.

    AƘalla mutum 53 sun rasa ransu sakamakon wutar.

    Gwamnan ya yi gargadin cewa adadin waɗanda suka mutum zai iya ƙaruwa. Ya ce ɗaruruwan gidaje duk wutar ta cinye inda ya yi kira ga 'yan jihar da su riƙa taimakawa waɗanda wutar ta cinyewa muhallai da wajen zama.

    Shima wani jami'in ɗan sanda a jihar ya bayyana cewa ba a san mutane nawa ne suka mutu ba.

    Abin da zamu iya cewa ke nan bamu san adadinsu ba. Inda wutar tafi barna shi ne garin Lahaina. Tuni dai shugaba Biden ya amince da kai taimakon gaggawa jihar.

  3. Biden ya nemi ƙara wa Ukraine tallafin dala biliyan 20

    Biden

    Asalin hoton, EVELYN HOCKTEINS

    Gwamnatin Biden ta buƙaci ƴan majalisar dokokin Amurka su bayar da damar ƙara taimakawa Ukraine da dala biliyan 20.

    Za a yi amfani da mafi yawancin kuɗin ne a kan ayyukan taimakon soji.

    Tun bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraine, Amurka ta bai wa ƙasar fiye da dala biliyan 100 a matsayin tallafi.

    Wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce za a ci gaba da bayar da irin wannan tallafi idan har buƙatar hakan ta taso.

    Ko da yake wasu ƴan majalisar daga jam'iyyar Republican sun ce za a soki matakin ci gaba da bayar da irin wannan taimako.

  4. Ivory Coast za ta tura sojoji Nijar

    Ouattara

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ivory Coast ya ce ƙasarsa za ta tura sojoji kimanin 1,000 waɗanda za su bi sahun sauran dakarun ko-ta-kwana da za su zauna cikin shirin ko-ta-kwana don tura wa Nijar.

    Alassane Ouattara na jawabi ne bayan kammala taron gaggawa na ECOWAS a Abuja, inda ƙungiyar ta ba da umarnin tanadar dakarun ko-ta-kwana don tura su Nijar a ƙoƙarin dawo da aiki da tsarin mulki.

    Ya ce ƙungiyar na son a dawo da shugaban ƙasar da sojoji suka hambarar da gwamnatinsa, Mohammed Bazoum a kan mulki.

    Mr Outtara, ya ce sojoji daga Najeriya da Benin da sauran ƙasashe za su haɗu da na Ivory Coast don zama cikin wannan shiri.

  5. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa a wannan shafi barkan mu da safiyar Juma'a.

    Badamasi Abdulkadir Mukhtar ke fatan mun wayi gari lafiya.

    Ku ci gaba da bibiyar mu don samun rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.