Faransa ta dakatar da duk wani tallafi da ta ke bai wa Burkina Faso

Asalin hoton, AFP
Faransa ta sanar da dakatar da duk wani tallafi da ta ke bai wa Burkina Faso da suka haɗa da ayyukan ci gaban ƙasa da kasafin kuɗi.
Sanarwar na zuwa ne bayan gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce za ta ɗauki duk wani matakin soji da ake son ɗauka kan jagororin juyin mulki a Nijar, a matsayin ƙaddamar da yaƙi gare su.
Ita ma gwamnatin sojin Mali ta ɗauki irin wannan matakin, da jaddada goyon baya ga sojojin makofciyarsu wato Nijar.



