Buhari da Osinbajo ba su halarci taron kwamitin zartarwar APC ba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Rabiatu Kabir Runka

  1. Sojojin Najeriya sun musanta raɗe-raɗin tura dakaru Nijar

    CDS Nigeria

    Asalin hoton, Defence Headquarters

    Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa dakarunta sun fara shirin ɗaukar matakin soji a kan Nijar.

    Sanarwar da daraktan yaɗa labaran shalkwatar, Birgediya-janar Tukur Gusau ya fitar ta ce dakarunta ba za su iya ɗaukar irin wannan mataki ba tare da amincewar shugabannin ECOWAS ba.

    Sanarwar ta ce matakin sojin shi ne mataki na ƙarshe da za a iya ɗauka kan Nijar, kuma za a yi hakan ne kawai bayan duk wani matakin da zai kai shi tsauri ba ya kasa cimma nasara.

    “Rundunar sojin Najeriya ta farga da wani labari da ake yaɗawa cewa tana tattara dakarunta don ɗaukar matakin soji kan Nijar.

    “A matsayin martani ga ƙwace mulki da soji suka yi, shugabannin ECOWAS sun tattauna kuma sun cimma matsaya kan maakan da za su ɗauka a game da baun.'' in ji sanarwar.

  2. Buhari da Osinbajo ba za su halarci taron kwamitin zartarwar APC ba

    BUHARI/OSINBAJO

    Asalin hoton, @PROFESSORYEMIOSINBAJO

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bayanin dalilin da zai hana shi halartar taron kwamitin zartarwar jam'iyyar APC na ƙasa.

    Ya ce ya aike wa jam'iyyar da saƙon neman uzuri don samun damar halartar wasu abubuwa da ya tsara yi kafin sanarwar taron.

    Tsohon shugaban ƙasar ya kuma jaddada goyon baya ga jam'iyyar da kuma fatan za a kammala taron lafiya.

    Shi ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo ya aike da irin wannan saƙo na neman uzuri, kamar yadda mai magana da yawunsa, Laolu Akande ya sanar.

    Akande ya ce Osinbajo baya ƙasar don haka ba zai samu halartar taron ba, kuma tuni ya sanar da jam'iyyar dalilansa.

  3. ...Daga Bakin Mai Ita tare da Safiya 'Yar Yarinya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  4. Faransa ta buƙaci Nijar ta tabbatar da tsaro a ofishin jakadancinta

    Niger protest

    Asalin hoton, AFP

    Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi kira ga sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar su tabbatar da tsaro a ofishin jakadancinta da ke Yamai.

    Kiran ya na zuwa ne gabanin zanga-zangar da ake shirin yi a babban birnin ƙasar a ranar Alhamis.

    A ranar Lahadi masu zanga-zanga sun kai hari ofishin jakadancin Faransa, lamarin da ya tilastawa ƙasar kwashe jama'arta daga Nijar.

    Masu goyon bayan juyin mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka sun buƙaci Faransa da Amurka su kwashe dakarunsu daga Nijar.

    Tun da farko, Amurka ta shawarci ma'aikata a ofishin jakadancinta da ke Yamai da ma sauran Amurkawa su guji shiga Nijar.

  5. Ƙungiyar ƙwadago ta dakatar da shiga yajin aiki a Najeriya

    NLC/TUC

    Gamayarr ƙungiyar kwadago ta Najeriya ta dakatar da shiga yajin aikin da ta shirya gudanarwar a fadin ƙasar sakamakon cire tallafin man fetur.

    Shugaban haɗaɗdiyar ƙungiyar ƙwadago ta TUC Festus Osifo ne ya bayyana haka lokacin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise News da safiyar ranar Alhamis.

    Ya ce sun ɗauki matakin ne bayan ganawar da shugabbannin ƙungiyar suka yi da shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya nuna zai duba buƙatun ƙungiyar tare da ɗaukar matakai cikin gaggawa.

    Kan haka ne ya ce ƙungiyar ta dakatar da gudanar da yajin aikin da ta shirya gudanarwa a ranar Alhamis.

    A ranar Laraba ne dai ƙungiyar ta fara gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna ɓacin ranta kan matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

    A nata ɓangare fadar shugaban Najeriya ta fitar da wata sanarwa cikin daren Laraba, inda a ciki take bayyana irin ci gaban da ta ce an samu sakamakon ganawar shugabannin ƙungiyar ƙwadagon da kuma shugaban ƙasar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.

    Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban zai yi nazari game da buƙatun da shugabannin ƙungiyar suka gabatar masa a lokacin ganawar, domin dakatar da zanga-zangar da ƙungiyar ke fara gudanarwa a ranar Laraba.

    Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ƙungiyar ƙwadagon cewa matatun mai ta Fatakwal za su fara aiki, nan da watan Disamba mai zuwa, bayan kammala aikin gyara su, da kamfanin mai na ƙasar NNPCL tare da haɗin gwiwar kamfanin Maire Tecnimont SpA na Italiya.

    Sanarwar ta kuma ambato shugaban ƙasar na tabbatar wa shugabannin ƙungiyar cewa zai ci gaba da aiki domin ciyar da ƙasar gaba, sannan kuma ya yi kira ga shugabanin da su haɗa hannu da shi domin samar wa ƙasar yanayin tattalin arziki mai inganci.

  6. Mutum 20 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Uganda

    Boat accidents are not uncommon in Uganda (file photo)

    Asalin hoton, AFP

    Mutane aƙalla 20 sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a Uganda.

    Ƴan sanda sun ce jirgin ruwan ya na ɗauke ne da mutum 34 da kuma tarin kaya masu nauyi a lokacin da ya yi hatsarin.

    Sun kuma tabbatar da cewa an ceto tara daga cikin mutanen.

    Sanarwar da ƴan sandan suka fitar ta ce jirgin ya na ɗauke da tarin kaya da suka haɗa da buhunan gawayi da kifi da kuma sauran kayan abinci.

    Sun alaƙanta hatsarin da ɗaukar kayan da suka fi ƙarfin jirgin ruwan.

    Hatsarin jirgin ruwa ba baƙon abu bane a Uganda.

    A 2020, mutane aƙalla 26 ne suka mutu a wani hatsarin da ya faru a tekun Albert da ke kan iyakar Uganda da Jamhuriyar Congo.

  7. Sojojin Nijar sun yi Allah-wadai da takunkuman ECOWAS

    Gen. Tchiani

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran juyin mulkin da aka yi Nijar ya yi Allah-wadai da takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta sanyawa ƙasar, yana mai bayyana su a matsayin abin da ya saɓawa doka da kuma rashin adalci.

    Cikin wani sako da ya gabatarwa al'ummar ƙasar ta talbijin, janar Abdoramane Tchiani, ya ce gwamnatinsa ba zata yarda ƙasashen yamma ko na yankin Afirka su matsawa ƙasarsa lamba a kan a mayar da Bazoum kan shugabanci ba.

    Janar Tchiani ya kuma ce kada ƴan ƙasar Faransa su ji fargabar komai.

    Tuni dai Faransa ta kwashe mutane kusan dubu guda ciki har da ƴan ƙasarta 560, bayan da masu bore suka kai wa ofishin jakadancinta a Yamai hari a ranar Lahadi.

  8. Sojan Amurka da ake nema na hannun Koriya ta Arewa

    SOJAN AMURKA

    Asalin hoton, Reuters

    Koriya ta Arewa ta fitar da sanarwarta ta farko a kan sojan Amurkan nan da ya tsallaka mata iyaka a watan da ya wuce.

    Rundunar sojan Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta yarda da barin sojoji daga yankin ƙasashen Koriyan, ta karbi saƙo daga Koriya ta Arewan a kan sojan na Amurkatun bayan da ya je bangaren Koriyan a ranar 18 ga watan Yulin da ya wuce.

    Daga ƙarshe dai Koriya ta Arewar ta tabbatar da cewa sojan na Amurka ya na hannunta.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba zata ce komai ba saboda bata so ta janyo wata matsala a kokarin da ake na mayar da sojan zuwa kasarsa.

  9. Assalamu alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkan mu da safiyar Alhamis.

    Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke farin cikin kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Ku ci gaba da bibiyar mu domin kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta don tafka muhawara a kan labaran da muka wallafa.