Buhari da Osinbajo ba su halarci taron kwamitin zartarwar APC ba

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Rabiatu Kabir Runka

  1. Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty a jerin ministocinsa

  2. Yawan masu kwana kan titi a Landan na ƙaruwa

    Alƙalumma na baya bayanan sun nuna atanni uku da suka gabata kusan mutane 3,300 ne ke kana a bisa titunan birnin Landan.

    Sama da rabin masu kwanan a bakin titunan suna kwana ne a karon su na farko.

    Adadin ya ƙaru da kashi 9 cikin ɗari idan aka haɗa shekarar da ta gabata.

  3. An dakatar da masu haya da tasi a filin jirgin sama na Abuja

    ...

    Asalin hoton, FAAN

    Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya, FAAN ta dakatar da ayyukan masu haya da motoci a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja.

    Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin ƙungiyoyin masu haya da motoci a filin jirgin.

    Hukumar ta shawarci fasinjoji da su yi amfani da duk wata hanyar sufuri amintacciya domin tabbatar da tsaron su a ciki da wajen filin jirgin.

    "Za a dawo da sufurin da zaran kamfanonin sun daidaita kan su,"i n ji sanarwar ta FAAN, wadda ta samu sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Yakubu-Funtua.

  4. Sojoji sun katse shirye-shiryen kafafen watsa labaran Faransa RFI a Nijar

    ...

    Asalin hoton, RFI Hausa/Facebook

    Bayanan hoto, ...

    Hukumomin sojin ƙasar Nijar sun katse shirye-shiryen tashoshin ƙasar Faransa na RFI da France 24.

    Matakin da ke zuwa mako ɗaya bayan da sojojin suka yi juyin mulki a Nijar, tare da bayyana aniyarsu ta raba gari da ƙasar Faransa.

    Da misalin Karfe 3 na yammacin Yau ne aka lura da katse shirye shiryen gidan rediyon RFI da tashar Talabijin ta France 24.

    Hakan ya sa mutane su ka fara tambayar abinda ke faruwa da kuma dalilan da suka sa majalisar ceton ta ƙasa daukar irin wannan mataki, ko da yake waɗannan tashoshi sun fuskanci irin wannan matsala a ƙasashen Mali da Burkina Faso.

    Sai dai tun farkon wannan juyin milki an ji wasu ƙungiyoyi na farar hula suna kira ga hukumomin mulkin sojan da su kori kafofin yaɗa labarun na ƙetare.

    Sakataren yaɗa labarai na cibiyar ƴan jarida ta ƙasa, Souleymane Brah, ya yi Allah wadai da matakin ya kuma yi kira da hukumomin su janye matakin.

    A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar tashoshin na Rfi da France 24 sun nuna rashin jin daɗin su kan lamarin.

  5. Ana ɗauki-ba-daɗi tsakanin sojojin Habasha da masu tayar da ƙayar baya a Amhara.

    Ana samun rahotannin karin dauki-ba-dadi tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya a yankin Amhara.

    Can a wajen Gondar mazauna birnin sun sheda wa BBC cewa an yi ba-ta-kashi mai tsananin gaske domin karɓe iko da filin jirgin sama.

    Daman tun a jiya Laraba mayaƙan sa-kan sun ƙwace filin jirgin sama na birnin nan mai tarihi, Lalibela.

    Akwai kuma rahotannin da ke cewa an fasa ofisoshin ƴan sanda da gidajen yari a garuruwa da dama.

    Yankin na Amahara na fama da faɗace-faɗace tun bayan da hukumomi suka ce za su rushe wata ƙungiya ta masu damara, da ke samun goyon bayan gwamnati.

  6. Tawagar ECOWAS ta fara tattaunawa da sojojin Nijar

    ..

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    Tawagar shiga tsakani ta ƙungiyar Ecowas ta isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, inda ta fara tattaunawa da jagororin soji na ƙasar waɗanda suka hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ne ya tura da tawagar, wadda tsohon shugaban Najeriya, Abdulsalam Abubakar ke yi wa jagoranci.

    ...

    Asalin hoton, PRESIDENCY

    A ɗazu ne shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wata tawaga zuwa jamhuriyar Nijar domin yin sulhu da sojojin da suka yi juyin mulki.

    Hakan na cikin matakan da Ecowas ta cimma a taron gaggawar da ta yi a cikin hutun ƙarshen makon da ya gabata a Abuja.

  7. Tinubu ya tura tawagar ECOWAS zuwa Nijar domin yin sulhu da sojoji

    ...

    Shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Ahmed Tinubu, ya tura wata tawaga zuwa jamhuriyar Nijar domin yin sulhu da sojojin da suka yi juyin mulki.

    Hakan na cikin matakan da Ecowas ta cimma a taron gaggawar da ta yi a cikin hutun ƙarshen makon da ya gabata a Abuja.

    Tsohon shugaban mulki soji na Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar ne ke jagorantar tawagar.

    Sauran yan tawagar sun haɗa da Sarkin Musulumi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III da kuma shugaban hukumar ƙungiyar Ecowas Omar Alieu Touray.

    Shugaban na Ecowas ya kuma tura wata tawagar ta daban ƙarƙashin jagorancin Ambasada Babagana Kingibe, zuwa Libya da Aljeriya kan batun juyin mulkin Nijar ɗin.

    Shugaba Tinubu ya nemi da su zauna da duk masu ruwa da tsaki tare da yin bakin ƙoƙarin su wajen samar da mafita kan halin da ake ciki a Nijar.

    Shugabannin tawagogin biyu sun bayyana cewa za su yi bakin ƙoƙarinsu domin tabbatar da samun abin da su ka je nema.

  8. Zan yi mulkin APC bisa adalci - Ganduje

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/Aminu Dahiru Ahmad

    Sabon shugaban jami'iyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya ce zai kama aiki ba ji ba gani domin tabbatar da jam'iyyarsa ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da za a gudanar ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

    Ganduje ya bayyana haka ne a yau Alhamis, lokacin da yake jawabi bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban jam'iyyar APC, a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar da ya gudana a Abuja.

    An kuma zaɓi tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattijan Najeriya, Ajibola Basiru, ɗan jihar Osun a matsayin sakataren Jam'iyar.

    A jawabin nasa, Ganduje ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, ya kuma jaddada cewa zai tabbatar da zaman lafiyar a cikin jam'iyar.

    Ganduje ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru wajen tabbatar da nasarar jam'iyar a zaɓen gwamnan jihar Kogi da Imo da Bayelsa

  9. Senegal ta ce a shirye take ta tura dakarunta Nijar

    Senegal trops

    Asalin hoton, AFP

    Senegal ta ce a shirye ta ke ta tura dakarunta Nijar idan ƙungiyar ECOWAS ta cimma matsayar yin hakan.

    A ƙarshen mako shugabannin ƙungiyar ECOWAS sun yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan sojojin da suka yi juyin mulkin idan ba su mayar da mulki ga shugaba Mohamed Bazoum ba.

    Cikin makon jiya Sojojin Nijar suka kifar da gwamnatin ƙasar.

    ECOWAS ta ƙaƙaba takunkuman tattalin arziki a kan Nijar.

    Nijar ce ƙasa ta huɗu da ta yi fama da juyin mulki a nahiyar, daga 2020 zuwa yanzu.

    Dubban ƴan Nijar sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan juyin mulkin a babban birnin ƙasar, Yamai.

  10. Morocco ta cire colombia daga gasar cin Kofin Duniya ta mata

  11. Kotun Zimbabwe ta bai wa ƴan adawa damar tsayawa takara

    Zimbabwe

    Asalin hoton, EPA

    Kotun ƙolin Zimbabwe ta wanke ƴan takara 12 daga jam'iyyar adawa ta Citizens Coalition for Change don shiga takara a babban zaɓen ƙasar, lamarin da ya yi watsi da hukuncin wata babar kotu da ta ce sun yi rijista a makare.

    Kotun ta kuma wanke wasu ƴan takara hudu daga ƙananan jam'iyyun adawa don tsayawa takarar duk da cewa ba a bayyana dalilan yin hukuncin ba.

    An shigar da ƙara da yawa kan cancantar yin takara a zaɓen, bayan cikar wa'adin kammala rijistar ƴan takara na ranar 21 ga watan Yuni.

    Rijistar ƴan takarar ta gudana har fiye da lokacin da aka ware.

    Gomman ƴan takara ba su samu yin rijistar ba saboda ƙalubalen biyan kuɗi da sauran tsare-tsare.

    Za a gudanar da zaɓen ne a ranar 23 ga watan Agusta.

  12. Ganduje ya zama sabon shugaban APC

  13. Oxlade-Chamberlain na nazarin komawa Besiktas

  14. An yi babbar zanga-zangar nuna goyon bayan juyin mulki a Nijar

  15. Rauni zai hana Jesus fara gasar Firimiya ta bana

  16. Messi ya ci kwallo biyu a wasan Inter Miami

  17. Jam'iyyar APC a Najeriya za ta sanar da sabon shugaba

    APC

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Bola Ahmed Tiinubu da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC su na halartar taron majalisar zartarwar jam'iyyar na ƙasa karo na 12.

    An fara taron ne da misalin ƙarfe 12:20 bayan zuwan shugaban ƙasar, a ɗakin taro na otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.

    Tun da safe ƴan kwamitin zartarwar jam'iyyar suka fara shiga ɗakin taron, ciki harda muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, sanata Abubakar Kyari.

    Taron ya ɗauki hankali ne, musamman yadda ake hasashen cewa za a naɗa sabbin shugabannin jam'iyyar, inda kuma tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ke kan gaba cikin waɗanda za su iya karɓar ragamar.

    Taron zai mayar da hankali kan abubuwa biyar da suka haɗa da kafa masu binciken kuɗi da cike giɓin muƙaman da ake da su, da kuma sauran batutu da suka shafi jam'iyyar.

    Muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, sanata Abubakar Kyari yana cikin mutanen da shugaba Tinubu ya nemi amincewar majalisa don naɗa su ministoci.

    • Taƙaddama ta ɓarke a APC bayan fitar da ƴan kwamitin yaƙin zaɓen 2023
  18. Mataimakin firaministan Habasha ya bayyana damuwa kan rikicin Amhara

    Ethiopian

    Asalin hoton, AFP

    Mataimakin firaministan Habasha kuma ministan harkokin wajen ƙasar, Demeke Mekonnen ya bayyana damuwa kan taɓarɓarewar tsaro a yankin Amhara na ƙasar.

    Tun daga watan Afrilu tsaro ya taɓarɓare a yankin bayan ɗaukar matakin rushe ƙungiyar tsaro da gwamnati ke goyon baya.

    Sojoji na fafatawa da ƙungiyoyin mayaƙa da ke ayyuka a yankin.

    Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa "Mun kama hanyar kawo ƙarshen junanmu, babu dattawa masu faɗɗa a ji, babu jagororin addini da za su bayar da shawara kuma babu masana da za su fargar da mu,"

    Ya ƙara da cewa "Ƙila akwai dambarwar da aka gaza warwarewa, amma abin da ya fi dacewa shi ne bin haryar sasanci wajen maganin matsalar da kuma gudun duk ani abu da zai ƙara kawo rabuwar kai,"

    Rahotanni sun ce mayaƙan sun ƙwace iko a manyan garuruwan yankin, ciki harda garin Lalibela mai ɗimbin tarihi.

  19. Faransa ta gama kwashe mutanenta daga Nijar

  20. An ɗaure wani ɗan Moroko saboda ya soki sarki a Facebook

    Said Boukioud

    Asalin hoton, AFP

    Lauyan ɗan Morokon da ake zargi da sukar sarkin ƙasar a kafar sada zumunta ya ce an yanke masa hukuncin shekara biyar a gidan yari.

    An tuhumi Said Boukioud da cin mutumcin gidan sarauta saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a 2020, inda ya soki yadda masarautar ke alaƙa da Isra'ila.

    Yana dai zaune ne a Qatar.

    Kundin mulkin Moroko ya ɗora wa sarki Mohammed alhakin tafiyar da huɗɗa da ƙasashen waje, kuma duk wata suka a kansa za ta janyo hukunci mai tsanani.

    Lauyan Boukioud, El Hassan Essouni, ya ce hukuncin ya yi tsauri kuma za su ɗaukaka ƙara.