Ƙarfin soja ne mataki na ƙarshe da za mu ɗauka a kan Nijar - Sojojin Ecowas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar and Umar Mikail

  1. Majalisar dattawa ta ci gaba da tantance waɗanda za a naɗa ministoci

    Majalisar dattawan Najeriya ta ci gaba da zaman tantance mutanen da shugaba Bola Tinubu ke shirin naɗawa minista.

    A ranar Litinin majalisar ta fara aikin, inda ta tantance mutum 14.

    Ta ci gaba da aikin a ranar Talata inda ta tantance mutum tara, sannan ta sanar da ɗage zaman ta zuwa Laraba don kammala tantance mutane biyar da suka rage.

    Yanzu haka dai mutum na farko, Dele Alake ne yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisar.

    Dele Alake shi ne mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

  2. Masu zanga-zanga sun ɓalla ƙofar shiga Majalisa

    Masu zanga-zanga sun ɓalla ƙofar shiga majalisar dokokin Najeriya da ke Abuja, yayin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ke ci gaba da tattaki a sassa daban-daban.

    Labour Protest
    Bayanan hoto, Ƙofar shuga majalisar dokokin Najeriya da ke Abuja.
    Labour Protest
    Bayanan hoto, Yadda masu zanga-zangar suka kutsa kai cikin majalisar.
    Labour protest
    Bayanan hoto, Ƙofar majalisar dokokin Najeriya a ƙasa, bayan masu zanga-zanga sun ture ta.
    Labour Protest
    Bayanan hoto, Ƴan sanda a tsaye lokacin da masu zanga-zanga suka kutsa cikin majalisar dokokin Najeriya.
  3. Rasha ta kai hari kan tashar fiton hatsi ta Ukraine

    Ukraine attack

    Asalin hoton, OLEH KIPPER/ODESA ODA

    Rasha ta kai hari kan rumbun hatsin UKraine da ke gaɓar tekun Danube a kusa da Romania, ɗaya daga cikin ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO.

    Harin ya lalata rumbun da tashar jirgin ruwa da ke kusa da shi.

    Rasha ta fara kai hari kan tasoshin ruwan Ukraine ne bayan ficewa daga yarjejeniyar fiton hatsi ta kogin Bahar Aswad da Majalisar Dinkin Duniya ta ƙulla a baya.

    Bidiyon da aka wallafa ya nuna yadda wuta ta tashi a tashar Izmail da sanyin safiyar Laraba.

    Shugaban Romania Klaus Iohannis ya yi Allah-wadai da harin da Rasha ke ci gaba da kaiwa kan gine-ginen Ukraine mai maƙwaftaka da ƙasarsa.

  4. Yadda zanga-zangar ƴan ƙwadago ke gudana a jihar Ogun

    Ga hotunan zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago ke gudana a jihar Ogun.

    Nigeria labour protest
    Bayanan hoto, Dandazon ƴan ƙwadago a yayin zanga-zanga a jihar Ogun.
    Nigeria labour protest
    Bayanan hoto, Masu zanga-zanga ɗauke da saƙonnin ''A dawo da tallafin mai wanda soke shi ya jefa talakawa cikin raɗaɗi''
    Nigeria labour protest
    Bayanan hoto, Ƴan ƙungiyar TUC dauke da saƙon ''A ceto talakawanmu''
    Nigeria labour protest
    Bayanan hoto, Tattakin ƙungiyar NLC da TUC a jihar Ogun.
    Nigeria labour protest
    Bayanan hoto, Ƴan ƙwadago ɗuke da tuta, yayin da ƴan sanda ke yi masu rakiya.
  5. Ana ci gaba da zanga-zangar kama Sonko a Senegal

    Senegal protest

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Senegal ta ce tana ɗaukar matakai don wanzar da zaman lafiya yayin da ƴan adawa ke ci gaba da zanga-zanga a sassan ƙasar.

    Ana ci gaba da zanga-zanga a Dakar babban birni ƙasar da kuma Ziguinchor, birnin da Ousmane Sonko ke jagoranta a matsayin magajin gari.

    Kama Sonko da kuma rushe jam'iyyarsa da aka yi ne suka tunzura zanga-zangar ta baya-bayan nan.

    Ana ci gaba da tsare Sonko, kuma a ranar Lahadi ya sanar da fara yajin aikin cin abinci.

    A ranar Litinin ministan harkokin cikin gida na Senegal, Antoine Félix Abdoulaye Diome ya sanar da rushe jam'iyyar Sonko ta Patriots of Senegal (Pastef) saboda zargin tayar da rikici a birnin Dakar.

    Magoya bayan jam'iyyar Pastef sun zargi jam'iyyar shugaba Macky Sall da yunƙurin kawar da manyan ƴan adawar sa.

  6. An tuhumi Donald Trump da yunƙurin murɗe zaɓe

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    An tuhumi tsohon shugaban Amurka, Donald Trump da yunƙurin murɗe zaɓen shekarar 2020 da ya sha kayi.

    Ana zargin Trump da laifuka huɗu da suka haɗa da cin amanar ƙasa da lalata bayanan shaida da kuma yunƙurin tauye yancin ƴan ƙasa.

    Zargin da ake masa ya biyo binciken da aka ƙaddamar ne kan zanga-zangar magoya bayansa a ginin majalisar Amurka ranar 6 ga watan Janairun 2021.

    Mr Trump, ɗan shekara 77 yana fatan yin takara a zaɓen shugaban ƙasar mai zuwa kuma ya musanta laifin da ake zarginsa da su.

    A baya ma an zargi ɗan jam'iyyar Republican da ɓoye takardun bayanan sirri a gidansa da kuma bayar da bayanan ƙarya kan hada-hadar kasuwanci.

    Binciken da aka yi kan zaɓen ya mayar da hankali ne kan matakan da Mr Trump ya ɗauka cikin watanni biyun ƙarshe na mulkinsa da kuma zanga-zangar birnin Washington inda magoya bayansa suka afkawa majalisar dokokin Amurka.

    • Trump ya musanta tuhumar boye bayanan sirri a gidansa
  7. Hotunan yadda gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago ke zanga-zanga a Kano

    b
    Bayanan hoto, shugabannin ƙungiyoyin da mambobinsu da dama ciki har mata sun fito domin gudanar da zanga-zangar a Kano
    ,
    Bayanan hoto, Jami'an 'yan sanda sun gargaɗi gamayyar ƙungiyoyin da cewa da su bari zanga-zangar ta riƙiɗe zuwa tarzoma
    b
    Bayanan hoto, Gamayyar ƙungiyoyin kwadagon na gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin amincewarsu da matakain cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi
    b
    Bayanan hoto, Lamarin da ƙungiyar ta ce ya haddasa tsadar rayuwa a fadin ƙasar
    b
    Bayanan hoto, Ƙugiyar ta ce tana zanga-zangar ne domin kyautata makomar ƙasar
    b
    Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun fito ne riƙe da kwalayen da ke ɗauke da saƙonni daban-daban
    b
    Bayanan hoto, Ana gudanar da zanga-zangar a faɗin jihohin ƙasar da kuma babban birnin tarayyar ƙasar Abuja
    b
    Bayanan hoto, Wasu kasuwanni da wasu ma'aikatu sun kasance a rufe a jihar Kano sakamakon zanga-zangar
    b
    Bayanan hoto, Da dama daga cikin ma'aikata da 'yan kasuwa a Kano sun yi zamansu a gida
  8. Hafsoshin sojin yammacin Afirka za su yi taro kan Nijar

    ECOWAS

    Asalin hoton, AFP

    Manyan hafsoshin sojin ƙasashen yammacin Afirka za su yi taro a yau Laraba don tattaunawa kan juyin mulkin da aka yi a Nijar makon jiya.

    Taron zai gudana ne a Abuja, babban birnin Najeriya.

    A baya dai Ƙungiyar ta gargaɗi sojin da suka yi juyin mulkin su gaggauta mayar da mulki ga shugaba Mohamed Bazoum cikin mako ɗaya ko kuma su yi amfani da ƙarfin soji a kansu.

    A cikin dare jirage uku da Faransa ta tura don kwashe jama'arta sun isa birnin Paris ɗauke da mutane 25.

    Italiya ma ta kwashe mutanenta, da ma na sauran ƙasashen Turai da Amurka.

    Sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar dai sun sanar da buɗe iyakokin ƙasar da Aljeriya da Burkina Faso da Libya da Mali da kuma Chadi. Sai dai iyakarta da Najeriya ta ci gaba da zama a rufe.

  9. Shugaban Tunisia ya kori firaminista Bouden

    Bouden

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Tinusia, Kais Saied ya kori Firai Ministar ƙasar Najla Bouden.

    Ms Bouden ta kasance mace ta farko da ta fara rike mukamin, kuma daman Mr Kais ne ya zaɓe ta ba tare da bata lokaci ba lokacin da ya kori wanda ta gada shekaru biyu da suka gabata.

    Shekaru biyu kenan da shugaban mai salon mulkin danniya ko mulaka'u, ke ɗaukar matakin korar manyan jami'an gwamnatinsa.

    Tuni shugaba Kais ya maye gurbinta da wani dan siyasa Ahmed Hachani, wanda ya rike babban mukami a babban bankin Tinusia.

    Wannan matakin na zuwa ne daidai lokacin da ƙasar ta faɗa rikita-rikitar siyasa da durƙushewar tattalin arziki, da tsadar rayuwa, da garƙame duk mai adawa da gwamnati.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu a wannan shafi, barkan mu da wannan safiya ta Laraba.

    Badamasi Abdulkadir Mukhtar ne ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muka wallafa muku.