Majalisar Dattijan Najeriya ta zaɓi shugaban masu rinjaye

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Zuckerberg zai buɗe sabon shafin da zai yi gogayya da Twitter

    ...

    Asalin hoton, META

    Bayanan hoto, ...

    Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook na shirin buɗe sabon shafi da zai yi goggaya da Twitter, wanda ake cewa zai fara aiki a ranar Alhamis.

    Shafin, da ake kira Threads, za a hada shi da Instagram. Meta ya bayyana shafin Threads a matsayin manhajar tura saƙonni.

    Hotunan shafin da aka fitar sun nuna yana kamanceceniya da Twitter.

    Wakilin BBC ya ce Mark Zuckerberg ya yi fice wajen kwaikwayon ayyukan wasu mutane cikin nasara ba tare da wata targaɗa ba.

    Wannan yunkuri na Meta na zuwa ne daidai lokaci da ake samun hamayya tsakanin Mark Zuckerberg da mai kamfanin Twitter, Elon Musk.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da war haka

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Talata domin kawo muku irin labaran da ke faruwa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.