Majalisar Dattijan Najeriya ta zaɓi shugaban masu rinjaye

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Mutane bakwai sun jikkata a wani harin da aka kai Tel aviv

    ...

    Wani Bafalasdine ya raunata akalla mutane bakwai a wani hari da aka kai da mota da wuka a birnin Tel Aviv na Isra'ila, kamar yadda 'yan sandan Isra'ila suka sanar.

    Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce wanda ake zargi ya kutsa cikin masu tafiya a kasa sannan ya yi ƙoƙarin daɓa musu wani abu mai kaifi. Wani farar hula ne ya harbe shi har lahira.

    Kakakin ya kara da cewa, uku daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

    An bayyana maharin a matsayin Bafalasdine dan yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye wanda ya kasance sanannen dan gwagwarmayar Hamas.

    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta yaba da harin, inda ta ce matakin martani ne da ya dace da gagarumin farmakin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da yi a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

    Akalla Falasdinawa 10 ne aka ce an kashe tun bayan da daruruwan sojojin Isra'ila da ke samun rakiyar jiragen sama marasa matuka suka shiga sansanin a safiyar Litinin, lamarin da ya haifar da kazamin fada da 'yan bindiga a ciki.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce yayin da take "ayyukan tabbatar da zaman lafiya a sansanin Jenin ta hanyar kai hari kan ababen more rayuwa na 'yan ta'adda, sakamakon haka ana kai wa fararen hula hari da ta'addanci".

    Hotunan bidiyo na CCTV daga wurin da aka kai harin a Tel Aviv, ya nuna masu tafiya a kafa da masu hada-hada a wani wurin shaye-shaye suna neman fakewa yayin da wata motar daukar kaya ta afkaw a wata tashar bas a titin Pinchas Rosen.

    Ana iya ganin direban yana fitowa daga tagar motar ya ruga da gudu ya nufi wajen wani mutum da ke tsaye kusa da wani shago, wanda alamu suka nuna ya caccaka masa wuka.

    Bidiyo na biyu ya nuna wani mutum sanye da hular kwano yana harbin maharin sau da yawa da bindiga yayin da yake kwance a kasa.

  2. Masu lalurar gani 42 ne suka gudanar da aikin Hajjin bana a Saudiyya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar masu lalurar gani a Saudiyya ta ce ta ɗauki nauyin masu lalluran gani guda 42 maza da mata tare da abokan aikinsu domin gudanar da aikin hajjin bana.

    Mahajjatan sun gudanar da dukkan ayyukan da ake buƙata a lokacin aikin na hajji a cikin tsarin mai sauki.

    Daraktan kula da harkokin mulki da kudi na Kafeef Abdulaziz Al-Mubarak ya taya shugabannin kasar Saudiyya da daukacin hukumomin da suka yi aiki a wannan kakar murnar samun nasarar gudanar da aikin Hajjin na bana.

    Ya yi nuni da cewa kungiyar ta gudanar da wannan aikin Hajji ne ta hanyar shirin Manasik, da nufin saukaka wa mahajjata da ba su gani wahalhalun da suke fuskanta ta yadda za su rika gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali.

  3. Hukumar INEC za ta gurfanar da waɗanda ake zargi da laifukan zaɓe a kotu

    Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
    Bayanan hoto, Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a ranar Talata ta ce za ta gurfanar da wasu da ake zargi da aikata laifukan da suka jiɓanci zaben 2023 a gaban kotu.

    Hukumar ta ce mutanen da za ta gurfanar kan irin waɗannan laifuka sun kai 215 daga ɓangarori daban-daban na kasar.

    Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga daukacin kwamishinonin zabe a babban ofishin hukumar da ke Abuja.

    Ya kara da cewa hukumar zabe za ta hada hannu da kungiyar lauyoyin Najeriya NBA wadda a cewarsa a shirye take ta gurfanar da masu laifin a gaban kotu ba tare da an biya komai ba.

    “Dole ne mu yarda cewa akwai wasu ƙalubale - wasu na rashin kayan aiki, wasu na rashin isassun ma'aikata. Muna duba bayanan wadanda suka aikata laifuka,” in ji Yakubu.

    “Akwai kararraki 215 daga ‘yan sanda kan laifukan zabe, muna aiki tare da NBA don gurfanar da masu laifi. Tuni Hukumar NBA ta gabatar da jerin sunayen lauyoyi 427 wadanda a shirye suke su gurfanar da wadancan kararrakin kyauta.”

    Da yake nazarin zabukan, Yakubu ya ce zabukan 2023 sun samu kyakkyawan idan aka kwatanta da zabukan da aka gudanar a baya.

  4. Ana tafka miyagun laifuka a rikicin Kamaru - Amnesty

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaro, da ‘yan aware da kuma ‘yan bindiga a yankin da ke magana da harshen Ingilishi a kasar Kamaru da aikata miyagun laifuka.

    Amnesty ta yi cikakken bayani kan take hakkin dan Adam da sauran laifuka da suka hada da kisa, azabtarwa da fyade a yankin Arewa maso Yamma.

    Ta ce rikicin ya ritsa da mutane yayin da wasu mayaƙa da dama suka yi arangama a yankin, inda aka yi wa mutanen da suka yi magana kan wannan aika-aika barazana tare da tsare su ba bisa ka'ida ba.

    Kungiyar mai kare hakkin dan'adam ta kuma bayyana "damuwa sosai" kan gazawar da hukumomi suka yi na tabbatar da hadin gwiwa yadda ya kamata tsakaninsu da cibiyoyin kare hakkin bil'adama na ƙasa da ƙasa da na shiyya-shiyya.

    “Muna kira ga hukumomin Kamaru da su binciki zargin take hakkin dan'adam da sauran laifukan da ke ƙarƙashin dokar cikin gida da aka aikata dangane da tashe-tashen hankula a yankin Anglophone, da kuma a hukunta duk wadanda ke da alhakin irin wannan cin zarafi a gaban kotuna masu zaman kansu, marasa son kai, da kuma kotunan da suka cancanta,” in ji Samira Daoud, darektan kungiyar Amnesty International a yammaci da tsakiyar Afirka.

    Kasar Kamaru dai na fama da rikici tun a shekarar 2017 da 'yan aware masu amfani da harshen Ingilishi suka kaddamar da tawaye.

    Rikicin ya haddasa rasa rayuka sama da 6,000 tare da tilasta wa mutane fiye da miliyan daya gudu daga gidajensu, a cewar kungiyar masu bincike kan rikice-rikice ta International Crisis Group.

  5. Masarautar Zazzau ta dakatar da basarake kan yi wa matashi hukunci

    Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli

    Asalin hoton, @ahmed_bamalli

    Bayanan hoto, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli

    Majalisar masarautar Zazzau ta amince da dakatar da Marafan yamman Zazzau bayan wani zama da ta yi a ranar Litinin.

    A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta ce matakin ya biyo bayan samun basaraken da laifin ɗaukar doka a hannun shi.

    Sanarwa ta ƙara da cewa: "A sakamakon haka, Majalisar Masarautar Zazzau ta amince cikin gaggawa da dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, Marafan Zazzau daga masarautar har sai abin da hali ya yi."

    Dakatarwar, kamar yadda sanarwar ta nuna ta biyo bayan koken da al'ummar Unguwar Magajiya da ke cikin birnin suka kai wa majalisar.

    Masarautar ta ce a shirye take ta ɗauki tsauraran matakai kan masu riƙe da muƙamai waɗanda ke saɓa wa doka, inda ta buƙace su da su miƙa duk wani batu da ya shafi hukunci ga mahukunta.

    • Ahmed Nuhu Bamalli: Tarihin sabon Sarkin Zazzau
    • Sarkin Zazzau: Abu 4 da suka faru tun bayan rasuwar Sarki Shehu Idris
  6. Matan Kenya sun rage yawan haihuwa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu ƙarin mata a Kenya da ba su son haihuwa da yawa.

    Wani sabon rahoto na hukumar Kiwon Lafiyar Jama'a na Kenya (KDHS) da aka fitar, ya nuna cewa yawan haihuwa a Kenya ya ragu daga yara 3-9 a kan kowace mace a cikin shekarar 2014, zuwa yara 3-4 a cikin 2022.

    Sai dai gwamnati ta ce wannan ba abun damuwa ba ne, tunda yawan al'ummar ƙasar za su ci gaba da karuwa.

    Akwai yiyuwar mace mai shekaru tsakanin 15-49 a Kenya ta zabi haihuwar yara 3 a maimakon 4.

    A shekarar 1989, matan da ke tsakanin irin waɗannan shekarun suna haihuwar yara har bakwai.

    Masana kiwon lafiya sun ce karuwar samun hanyoyin kayyade iyali ya rage yawan haihuwa. Yawancin mata kuma sukan jinkirta haihuwa sanadiyyar neman ilimi.

    Rahoton ya ce, karuwar tsadar rayuwa a kasar ya shafi yawan haihuwar da mata ke yi.

  7. Na so Manchester City ta ɗauki Mane - Yaya Toure

  8. Matsin lamba ne ya hana Shugaban Senegal yin tazarce - 'Yan adawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ƴan adawa a Senegal sun mayar da martani kan sanarwar da shugaban ƙasar Macky Sall ya bayar cewa ba zai tsaya takara ba a zaɓen 2024, inda suka ce hakan ya samo asali ne daga matsin lamba daga al'ummar ƙasar.

    Abass Fall, ɗan majalisa a jam'iyyar jagoran adawar ƙasar Ousmane Sonko - ya ce hakan ba abin mamaki ba ne.

    “Abin da ya ba mu mamaki shi ne idan Macky Sall ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2024.

    Dukkanmu mun san yana so..Abin takaici ne a gare shi, matsin lamba ya kai ga ba shi da wani zaɓi sai dai mutunta tsarin mulkin ƙasar."

    Aminata Touré, tsohuwar firaminista da ke ɓangaren 'yan adawa a yanzu ta ce shawarar da Mista Sall ya yanke ta mutunta kundin mulki ya kasance ne saboda "tattaunawar 'yan dimokraɗiyyar Senegal" a cikin gida da kuma ƙasashen waje.

    “Babu wanda ya shirya amincewa da koma-bayan dimokraɗiyyar da ake hasashe. Don haka, cikin fidda rai, ya mutunta Tsarin Mulki." in ji ta.

    Ta ce an kashe mutum 16 a zanga-zangar "sannan kwamitin bincike zai bayyana mana su wane ne suka shirya hakan".

    Tsohuwar ministar kasuwanci kuma shugabar jam'iyyar Alliance pour la République Aminata Assome Diatta, ta bayyana wannan lokacin a matsayin "mai cike da tarihi".

  9. Kalli yadda ake fafatawa a gasar zabga mari

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  10. Taliban ta umarci a rufe kantunan gyaran gashi da na kwalliya a Afghanistan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Ƴan Taliban sun ba da umarnin rufe wuraren kwalliya da na gyaran gashi a ƙasar Afghanistan a wani sabon tarnaƙi da mata ke fuskanta.

    Wani mai magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin kyautata ɗabi'u ya shaida wa BBC cewa kantunan suna da wata ɗaya su yi biyayya da umarnin, daga ranar 2 ga Yuli da aka fitar da sanarwa.

    Ƴan Taliban dai tuni suka haramta wa ‘yan mata da mata daukar karatu a azuzuwa da zuwa wuraren motsa jiki da na shaƙatawa, kuma a baya-bayan nan ma sun hana mata yin aiki da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Hukumomin na Afghanistan sun kuma ba da umurnin cewa mata su dinga sanya suturar da za ta bayyana idanunsu kadai, kuma dole ne su kasance tare da muharraminsu a duk lokacin da suka yi tafiya ta sama da kilomita 72.

    Rufe wuraren kwaliya da gyaran gashi, wani ɓangare ne na matakan da 'yan Taliban suka ɗauka a lokacin da suka yi mulki na ƙarshe tsakanin 1996 zuwa 2001. Amma sun sake bude wuraren bayan mamayar da Amurka ta yi wa Afghanistan a shekara ta 2001.

    Da take mayar da martani game da sabon matakin, wata 'yar Afganistan da ba a bayyana sunanta ba, ta shaida wa BBC cewa: "Yan Taliban na kwace mafi yawan ƴancin matan Afghanistan".

    "Da alama 'yan Taliban ba su da wani shiri na siyasa face mayar da hankali kan mata. Suna ƙoƙarin kawar da mata a kowanne mataki na rayuwar jama'a."

    Ƴancin mata na ci gaba da raguwa tun bayan da Taliban ta kwace mulki a shekarar 2021.

    • Taliban ta hana mata aiki a karkashin Majalisar Dinkin Duniya
    • Yadda matan Afghanistan ke rayuwa cikin tsoro da fargaba
  11. An ci tarar Neymar dala miliyan uku a Brazil

  12. Shugabannin Majalisar Wakilan Najeriya da yankunansu

    Majalisar Wakilan Najeriya

    Asalin hoton, NASS

    Shi ma Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Tajudden Abbas ya sanar da sunayen sabbin shugabannin Majalisar ta 10 na jam'iyyarsa ta APC - masu rinjaye ke nan.

    Kazalika, ya sanar da na marasa rinjaye daga jam'iyyun adawa.

    Shugabannin masu rinjaye:

    • Julius Ihonvbere: Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Edo (kudu maso kudu)
    • Halims Abdullahi : Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Kogi (arewa ta tsakiya)
    • Bello Kumo: Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Gombe (arewa maso gabas)
    • Adewunmi Onanuga: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Ogun (kudu maso yamma)

    Shugabannin marasa rinjaye:

    • Kingsley Chinda: Shugaban Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Ribas a (kudu maso kudu)
    • Aliyu Madaki: Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye (NNPP) daga Jihar Kano a arewa maso yamma
    • Ali Isah: Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (PDP) daga Jihar Gombe a arewa maso gabas
    • George Ozodinobi: Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye (LP) daga Jihar Anambra a kudu maso gabas
  13. Yankunan da sabbin shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya suka fito

    Sanatocin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Ɗazun nan ba daɗewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Godswill Akpabio ya sanar da manyan Majalisar ta 10 a jam'iyyarsu ta APC - ɓangaren masu rinjaye ke nan.

    Haka nan ya sanar da na marasa rinjaye, wato na jam'iyyun adawa.

    Ga yankunan da na masu rinjaye suka fito:

    • Sanata Opeyemi Bamidele - Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ekiti (kudu maso yamma)
    • Sanata David Umahi - Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye daga Jihar Ebonyi (kudu maso gabas)
    • Sanata Ali Ndume - Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Borno (arewa maso gabas)
    • Sanata Lola Ashiru - Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye daga Jihar Kwara (arewa ta tsakiya)

    Yankunan da na marasa rinjaye suka fito:

    • Sanata Simon Davou na PDP - Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Filato (arewa ta tsakiya)
    • Sanata Oyewunmi Olarere na PDP - Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye daga Jihar Osun (kudu maso yamma)
    • Sanata Darlington Nwokeocha na LP - Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Abiya (kudu maso gabas)
    • Sanata Rufai Sani Hanga na NNPP - Mataimakin Mai Tsawatarwa na Marasa Rinjaye daga Jihar Kano (arewa maso yamma)
  14. Makomar Kano Pillars da Katsina United na hannun juna ranar Laraba

  15. Hotuna: Mutane na ficewa daga sansanin 'yan gudun hijira na Jenin

    Mambobin kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasɗinu suna taimakawa ƴan gudun hijira don kwashe su daga sansanin Jenin zuwa wani wuri da babu hadari.

    Kungiyar ta ce tana fuskantar babban ƙalubale wajen kai taimako wa mutanen da ke buƙata saboda shingen da Isra'ila ta yi.

    Jenin

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Bayanan hoto, ...
    Jenin

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Bayanan hoto, ...
    Jenin

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Bayanan hoto, ...
  16. Majalisar Dattijan Najeriya ta zaɓi shugaban masu rinjaye

    Nigerian majiority leader

    Asalin hoton, Senator Opeyemi Bamidele/Twitter

    Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya sanar da Opeyemi Bamidele a matsayin, shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai.

    Ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, inda ya bayyana Sanata David Umahi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye.

    Haka zalika ya ce rukunin 'yan majalisar dattijai na jam'iyyar APC mai mulki sun amince da Mohammed Ali Ndume, a matsayin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye a majalisar.

    Sai kuma Sanata Oyelola Yisa Ashiru matsayin mataimakin mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye.

    Jim kaɗan kuma haka ne, sai aka sanar da Sanata Simon Mwadkon Davou a matsayin shugaban marasa rinjaye, yayin da Oyewumi Olalere ya kasance mataimakin shugaban marasa rinjaye.

    Haka zalika, an zaɓi Sanata Darlington Nwokocha, a muƙamin mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye, sai Sanata Rufa'i Sani Hanga, mataimakin mai tsawatarwa na ɓangaren marasa rinjaye a majalisar dattijai.

  17. Hukumomin Abuja sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya sanadin cutar mashaƙo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar kula da babban birnin tarayya, Abuja ta sanar da bullar cutar mashaƙo ko kuma diphtheria a wasu sassan birnin.

    Jaridar Punch ta ruwaito daraktan sashen kula da lafiyar jama'a a hukumar, Dakta Sadiq Abdulrahman yana sanar da ɓullar cutar.

    Abdulrahman ya ce tuni cutar ta kashe wani yaro ɗan shekara hudu, inda ya kara da cewa ɓullar ta tun farko a jihohin Legas da Ondo da kuma Kano a watan Janairu, cutar ta sanya cibiyar yaƙi da cutuka (NCDC) ta Najeriya kai ɗauki a matakin ƙasa gaba ɗaya.

    Diphtheria, cuta ce da ke janyo ƙwayoyin cuta masu guba kuma suna sarƙe numfashi, da janyo matsalolin bugun zuciya, har ma suna iya kaiwa ga mutuwa.

    Daraktan ya ce an tabbatar da bullar cutar ne bayan gwaje-gwajen da aka yi wa samfuran wadanda ake zargin sun kamu a wani yanki da ke kusa da Dei-Dei.

    “Makonni biyu da suka wuce, mun samu bayanai daga wani yanki na birnin Abuja inda aka yi zargin mutum takwas na ɗauke da alamomin cutar kuma hakan ya sa hukumarmu ta dauki samfuran wasu mutane.

    Ya buƙaci mazauna yankin su bayar da rahoton duk wani baƙon alamu, musamman kalubalen numfashi ga hukumomin da abin ya shafa kuma ya shawarci su kula da tsaftar jiki da ta muhalli.

    Abdulrahman ya ce hukumarsu na hada kai da jihohi makwabta, domin daƙile yaɗuwar cutar ta hanyar sanya ido kan iyakoki.

    Haka kuma, babban sakataren hukumar lafiya matakin farko na Abuja, Dokta Yahaya Vatsa, ya yi gargadin cewa mutanen da ba a yi musu alluran riga-kafi ba wadanda ke zaune a wurare masu cunkoso da rashin tsafta na cikin hatsarin kamuwa da cutar mashaƙon.

  18. Sarkin Zulu na Afirka ta Kudu ya musanta batun ba shi guba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Sarkin Zulu na Afirka ta Kudu, Misuzulu kaZwelithini, ya musanta zargin da ake yi cewa watakila an ba shi guba, yana mai cewa yana cikin ƙoshin lafiya.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake taƙaddama bayan da firaministansa na gargajiya ya faɗa a karshen mako cewa sarkin na jinya a Eswatini bisa zargin ya ci guba.

    Cif Mangosuthu Buthelezi ya ce sarkin na kwance a asibiti sakamakon mutuwar daya daga cikin manyan mashawartansa, wanda kuma ake zargin shi ma guba ce ta kashe shi, amma mai magana da yawun sarkin ya musanta hakan inda ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.

    Cikin faifan bidiyon da aka raba wa manema labarai na Afirka ta Kudu, sarkin ya ce an tsara zai dinga zuwa duba lafiyarsa akai-akai, wanda ya yanke shawarar yi a Eswatini.

    "Ni ban ci wata guba ba, ina cikin ƙoshin lafiyata 100 bisa 100.

    "Ina cikin farin ciki saboda ina da ƙoshin lafiya, babu wata guba da na ci. Don haka mutane, al'ummar Zulu, da dangina su tunatar da jama'a cewa kada a saurari duk abin da mutane ke faɗi, ”in ji shi.

    An kuma ambato Sarki Misuzulu yana shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ta wayar tarho daga Eswatini cewa "yana cikin ƙoshin lafiya sosai".

    Sarkin mai shekara 48 ya hau karagar mulki a shekarar da ta gabata bayan rasuwar mahaifinsa Sarki Goodwill Zwelithini a wani zazzafan rikici da ya barke kan gadon sarautar.

  19. Zanga-zangar Faransa: Shugaba Macron zai gana da magadan gari

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da shugabannin yankuna da madagan gari sama da 200 da aka shafe kwanaki ana fama da rashin kwanciyar hankali bayan kisan da 'yan sanda suka yi wa wani matashi.

    Kakakinsa ya ce tattaunawar ƙoƙari ne wajen fahimtar musababbin wannan zanga-zanga.

    Zanga-zangar dai ta barke ne a birnin Paris cikin dare bayan ƴan sanda sun harbe matashin mai shekara 17 wanda ya ƙi tsayawa lokacin da suka umarce shi da ya tsaya a cikin motarsa.

    Ba a kama mutane da yawa ba a jiya Litinin kamar sauran ranakun.

    Wakilin BBC ya ce babbar buƙatar masu zanga-zangar ita ce a fito a sake fitar da bayanai kan ayyukan ƴan sanda.

    Ana kuma cece-kuce a Faransar kan zargin tara kuɗi ga ɗan sandan da ya harbe matashin.

    Ƴan siyasa na ta Allah-wadai da wannan yunƙuri - wanda ake cewa kawo yanzu an tara kudin da ya kai dala miliyan ɗaya da rabi, suna mai cewa abin kunya ne da badaƙala.

  20. Hare-haren Isra'ila sun kori Falasɗinawa 3,000 daga gidajensu

    Palasɗinu

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Mahukuntan Falasdinu sun ce kusan Falasdinawa 3,000 ne suka tsere daga gidajensu a Jenin bayan ɗaruruwan dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da farmaki da hare-hare ta sama a yankin da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan a ranar Litinin.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za a ci gaba da kai farmakin muddin aka ga bukatar hakan, yana mai cewa farmaki ne na fatatakar 'yan ta'adda.

    Wakiliyar BBC ta ce duk da cewa iyalai na ficewa wasu mutane sun shaida mata cewa Isra'ila na tsare da magidanta da ƙananan yara maza a sansanin.

    'Yan siyasar Falasdinu sun bayyana yanayin da yunƙurin mamaye gidajensu.

    Akalla Falasɗinawa 10 aka kashe zuwa yanzu, a cewar hukumomin lafiyar yankin.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a dauki matakan gaggawa domin isar da kayan agaji ga waɗanda aka jikkata.