Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kashi ɗaya cikin uku na arziƙin Najeriya na iya zama kuɗaɗen bashi - DMO

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi, Ibrahim Yusuf Mohammed and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Lokaci na kure wa masu ceton sundukin yawon shakatawa na karkashin ruwa

    Yunkurin ceto mutane biyar da ke cikin jirgin 'yan yawon buɗe ido da suka ɓata kusa da tarkacen jirgin ruwan Titanic da ke Arewacin Tekun Atlantika na shiga wani muhimmin mataki.

    An kiyasta cewa yanzu 'yan sa'o'i na iskar oxygen da suka rage kadan ne - ma'ana iskar da suke shaka za ta iya ƙarewa a nan ba da dadewa ba.

    Sai dai masana sun ce tsawon lokacin da iskar oxygen ke dawwama ya dogara ne da abubuwa daban-daban.

    An bukaci dukkan wani jirgi da ke kewayen yankin ya kai agaji idan zai iya saboda dan karamin lokacin da ya rage.

    A hirarsa ta farko tun bayan bacewar jirgin sundukin a ranar Lahadin da ta gabata, shugaban kamfanin da ya mallaki jirgin ruwan Sean Leet, ya ce suna ci gaba da fatan za a gano mutanen kuma a dawo da su gida lafiya.

    Jami’an tsaron gabar tekun Amurka sun ninka wuraren binciken, kuma wani jirgin ruwa na Faransa dauke da wani mutum-mutumi da ke iya nutsewa kasan teku cikin sauki a kusan kilomita dubu shida na kan hanyar karasawa wajen.

  2. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Aisha Babangida ce ke muku barka da safiya tare da fatan kasancewa da ku a wannan rana ta Alhamis.

    Za mu kawo muku labarai da rahotanni iri-iri daga sassan duniya.

    Sai ku kasance da mu.