An samu arangama tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan babbar jam'iyyar adawar Saliyo All People's Congress(APC), lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum guda, tare da tilasta rufe kasuwanni a babban birnin ƙasar Freetown.
Lamarin na zuwa ne yayin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa ranar Asabar mai zuwa..
Mutane na ta yin tururuwar zuwa kasuwanni domin sayen kayan abinci, sakamakon fargabar ɓarkewar ƙarin rikici a birnin, kamar yadda wasu mazauna birnin suka shaida wa BBC.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito mai magana da yawun babbar jam'iyyar adawar ƙasar Sidi Yahya Tunis na cewa 'yan sanda sun kashe ɗaya daga cikin magoya bayan jam'iyyar a lokacin arangamar.
Wani bidiyo da BBC ba ta tabbatar da sahihancinsa ba, ya nuna wani mutum na cikin rashin hayyaci, sakamakon harbinsa da aka yi a wuya.
Shugaban rundunar 'yan sandan ƙasar Braima Jah ya ce 'yan sanda ba su yi harbi ba. inda ya zargi masu zanga-zangar da yin harbi har sau biyar, ''Biyu daga ƙaramar bingigar pistol, sannan uku daga bindiga ƙirar AK-47.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an kama mutum 66 kan rikicin.
Rikicin ya ɓarke bayan da jam'iyyar adawar ƙasar ta zargi hukumar zaɓe da tafka kura-kurai a rajistar masu kaɗa ƙuri'a.
Cikin jawabin da shugaban ƙasar Julius Maada Bio ya gabatar, ya sha alwashin ɗaukar matakin ba-sani, ba-sabo kan masu tayar da rikici a ƙasar.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da Birtaniya da Amurka da Ireland da Jamus da Faransa da ƙungiyar EU suka fitar, sun yi kira ga duka ɓangarorin su zauna cikin kwanciyar hankali.
Zaɓen shi ne na biyar tun bayan ƙarshen yaƙin basasar ƙasar a 2002, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum fiye da 50,000, tare da raba dubbai da muhallansu.
Mista Bio na neman wa'adin shugabancin ƙasar na biyu kuma na ƙarshe, inda yake fafatawa da sauran 'yan takara, ciki har da na babbar jam'iyyar adawar ƙasar APC Samura kamara, wanda ya zo na biyu na zaɓen 2018.
Mista Kamara na fuskantar shari'a kan zargin rashawa tun 2021, zargin da ya ce bi-ta-da-ƙulli siyasa ne kawai.
Ana sa rana kusan mutum miliyan 3.4 ne za su kaɗa ƙuri'unsu ranar 24 ga watan Yuni a ƙasar da ke fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da kashi 43 cikin 100.