Tsohon shugaban Amurka Trump ya isa Miami don gurfana gaban kotu

Asalin hoton, Reuters
Wani alkalin kotun tarayya a Amurka ya yi watsi da bukatar barin kafofin yaɗa labarai su dauki hotuna da bidiyo a bayyanar tsohon shugaban ƙasar Donald Trump a kotu da ke Miami yau Talata.
Kazalika, an haramta wa 'yan jarida zuwa da wayoyinsu na salula a yayin zaman kotun.
Mista Trump zai bayyana gaban kotun ne don fuskantar tarin tuhume tuhume game da laifukan da suka danganci rike wasu takardun sirrin ƙasa bayan ya bar mulki da kuma hana jami'an tsaro takardun a lokacin da suka yi ƙoƙarin karɓo su.
Tuni dai Mista Trump ya musanta aikata ba daidai ba.
Wani lauya da ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kwamitin harkokin shari’a na majalisar wakilan Amurka lokacin da ake shirin tsige Trump karo na biyu, Norman Eisen, ya faɗa wa BBC cewa tsohon shugaban zai shiga mawuyacin hali a kotun.
Ya ce; "Ina ganin tuhumar tana da ƙarfi sosai.
Daga cikin tarin matsalolin Donald Trump, wannan kila za ta kasance laifin shari’a mafi girma. Saboda akwai kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa ya dauki abin da muke kira bayanan tsaron ƙasa, da tsare-tsare na kai harin sojoji a kan wasu kasashe da shirye-shirye na yadda za a iya kawo mana hari da bayanai a kan sirrin nukiliya da abokan gabarmu da kuma abokai da kawayenmu.
Ya ɗauki duka waɗannan ba tare da wani dalili na shari’a da zai sanya shin yin haka ba.''

