Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Kimanin mutum 150 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara'

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da ƙasashe makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Gwamnatin Japan ta sanar da wani shirin tallafi don karfafa haihuwa

    Firaministan kasar Japan Fumio Kishida, ya sanar da wasu tsare-tsare domin hana raguwar yawan haihuwa a kasar.

    Mista Kishida ya shaida wa taron manema labarai cewa wannan ita ce dama ta karshe da kasar Japan ke da ita cikin shekara goma ta tunkarar yawan tsofoffi da suka yi yawa a cikin al'ummarta.

    Yayin da ingantuwar rayuwa tsakanin al'ummar Japan ya kara yawan tsawon rai, raguwar yawan haihuwa na barazana ga ɓangaren ayyuka na ƙasar saboda yadda tsofaffi ke yin ritaya.

    Za a aiwatar da manufofin da aka sanar daga shekara mai zuwa kuma sun hada da biyan tallafi ga yara da daukar nauyin kudin haihuwa, da hutun musamman ga iyaye da canza yanayin al'adu na wurin aiki ga iyaye.

    Firaministan Japan ya yarda cewa masu daukar ma'aikata na nuna wariya ga masu yara saboda suna ganin kasancewar yara na iya zama dalilin rage mayar da hankali kan aiki.

    Firaministan ya ce zai yi ƙokarin aiwatar da manufar ba tare da kara haraji ba, ko da yake wasu manazarta sun nuna shakku kan wannan alwashin ganin irin kudaden da za a yi amfani da su wurin aiwatar da manufar.

  2. Ƴansanda na bincike kan yadda matasa suka yi wa wata mata tsirara a kasuwa

    Ƴan sanda a Ghana sun fara gudanar da bincike kan wani bidiyo da aka yi wa wata mata mai matsakaicin shekaru tsirara tare da lakaɗa mata a kasuwar Zebilla da ke yankin Gabas.

    A cikin bidiyon, an nuna yadda samari suka fara cire wa matar kaya, kafin daga bisani suka yi ma ta duka tare da cin zarafinta.

    'Yan sanda a cikin wata sanarwa da aka fitar sun bayyana lamarin a matsayin "rashin mutunci da wulakanci."

    Rahotannin cikin gida sun ce an tozarta matar ne a kasuwar Zebilla a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai a baya wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi daga yankin.

    Wasu daga cikin waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin sun yi ikirarin cewa sun afka wa matar ne kasancewarta bafulatana, waɗanda a cewarsu ke kai masu hare-hare tare da yi masu fashi da kuma cin zarafin matansu.

    Wani masani kan harkokin tsaro, Adib Saani ya ce, lamarin na da matukar hadari.

    "Wannan mataki da matasan yankin suka dauka mataki ne mai hadarin saboda yana kara hura wutar ta'addanci. 'Yan ta'adda na son ganin wadannan abubuwan saboda suna fakewa da su wurin kai hare-hare."

    Duk da fulani cewa fulani sun kwashe shekaru da dama suna rayuwa a Ghana. Mafi yawanci ana yi masu kallon bare wadanda ke fafatawa da mutanen yankin don karancin abinci da ruwan shan dabbobinsu.

    Rikici tsakanin manoma da fulani makiyaya ya yi kamari a yammacin Afirka, sai dai har yanzu ba a shawo kan matsalar ba, wanda kuma yakan janyo asarar rayuka da dukiyoyi a yankin.

  3. Amurka ta gargaɗi ƴan kasarta kan zuwa Uganda saboda tsauraran dokokin hana luwaɗi

    Gwamnatin Amurka ta gargadi 'yan kasarta kan tafiya zuwa kasar Uganda, biyo bayan kafa wasu tsauraran dokokin tsananta hukunci kan masu luwadi da maɗigo da kasar Uganda ta ƙaddamar a baya-bayan nan.

    Matakin na zuwa ne makonni biyu bayan da shugaban Uganda, Yoweri Museveni ya amince da dokar da ta janyo cece-ku-ce duk da gargadin da shugabannin kasashen duniya da masu kare hakkin bil'adama suka yi.

    A cikin sanarwar da aka sabunta a ma'aikatar harkokin waje ta Amurka da shafin yanar gizon Ofishin Jakadancin Uganda, gwamnatin Amurka ta bayyana cewa dokar hana luwadi da madigo ta Uganda ta 2023 na da hadari ga ƴan ƙungiyar LGBTQI da matafiya.

    An yi gargaɗin cewa matafiya za su iya fuskantar tuhuma, ɗaurin rai da rai ko kuma hukuncin kisa.

    Gargaɗin mai mataki na uku ya buƙaci matafiya da su yi tunanin sauya shawara kan balaguro zuwa Uganda saboda yana yiwuwa su fuskanci farmaki daga 'yan banga da kuma binciken tilas a ofisoshin 'yan sanda idan ana zargin su da yin luwaɗi.

    Wadanda ke goyon bayan hakkokin masu luwaɗi da maɗigo na iya fuskantar ɗauri na dogon lokaci a gidan yari.

    Dokar hana luwaɗi da maɗigo ta Uganda ta 2023 ta haifar da tofin Allah-tsine kuma ana ɗaukar ta a matsayin ɗaya daga cikin tsauraran dokokin hana luwaɗi a duniya.

    Dokar ta buƙaci a ci tara ko kuma ɗaurin tsakanin shekaru14 zuwa ɗaurin rai da rai, da hukuncin kisa ga waɗanda aka kama da laifin yin luwadi.

  4. Mece ce cutar Anthrax kuma ta yaya ake kamuwa da ita?

  5. An ɗaure wata mata kan laifin yi wa yaro ɗan shekara takwas fyade

    Ana ta ce-ce ku-ce a ƙasar Tanzaniya bayan da aka gano wata mata mai matsakaicin shekaru ta yi wa wani yaro ɗan shekara takwas fyade tare da shafa masa cututtukan da ake yaɗawa ta hanyar jima'i.

    A ranar Juma'a ne aka yanke wa Desderia Mbwelwa, mai shekaru 57 hukuncin ɗaurin shekaru 29 a gidan yari, sai dai kawo yanzu ba a bayar da cikakken bayani kan hukuncin ba.

    A ranar da lamarin ya afku, matar ta tarar da yaron a lokacin da yake kiwon shanu a wani ƙauye da ke kudancin yankin Iringa, sai ta tambaye shi inda abokansa suke.

    Sannan an ce ta yi lalata da shi a ƙarƙashin wata bishiya bayan ya ce abokansa ba su kusa.

    Shari’ar dai ta samu shaidu biyar ciki har da wani likita da ya duba yaron ya kuma tabbatar da cewa ya samu raunuka kuma ya kamu da cutukan da ake samu ta hanyar jima’i sakamakon gurɓacewar da aka samu a al’aurarsa.

    An ce Mbwelwa ta kare kanta da cewa ita babba ce mai ‘ya’ya da jikoki waɗanda suka dogara da ita.

    Lauyanta, Frank Mwela, ya ce yana shirin ɗaukaka ƙara a kan hukuncin saboda ba a gwada wanda yake karewa ba don tabbatar da ko da gaske tana da cututtukan da ake ɗauka ta jima'i.

    “Ba a gwada wadda nake karewa ba ko tana ɗauke da wadannan cututtuka, inda da wanda nake karewa da mai shaidarta sun tabbatar da cewa ba su ɗauke da wata cuta saboda ɗaya daga cikin waɗanda suka yi shaida mijinta ne,” inji shi.

  6. Mutane 11 sun mutu a wani harin makami mai linzami kan mahaifar Zelensky

    Ukraine ta yi ikirarin cewa fararen hula 11 ne suka mutu sannan wasu 28 suka jikkata sakamakon harin makami mai linzami da Rasha ta kai kan mahaifar shugaban kasar Volodymyr Zelensky da ke Crimea.

    A cewar wani jami'in yankin, Oleksandr Vilkul, ana tunanin akwai mutum daya da ke binne a karkashin gine-ginen da suka ruguje sakamakon harin, kuma ana ci gaba da gudanar da ayyukan agaji cikin gaggawa.

    Rahotanni sun ce an tsinto gawarwaki shida daga wata cibiyar kasuwanci yayin da aka tsinto wasu gawarwaki hudu daga wani gini mai hawa biyar.

    Har ila yau, ma'aikatar tsaron Rasha ta yi ikirarin cewa sojojinta sun dakile harin da sojojin Ukraine suka kai a Donetsk a karo na biyu a jere.

    Rasha ta yi ikirarin cewa sojojin Ukraine sun yi nasara, sai dai ita ma nata sojojin sun lalata tankunan yaƙi guda takwas na Ukraine.

    Ukraine ta samu wadannan tankuna daga kawayenta na yammacin duniya.

    Har yanzu dai Ukraine ba ta ce komai game da ikirarin na Rasha ba, amma ta ce ko shakka babu tsarin tsaronta na sama ya hana Rasha kai hare-hare a yankin Kiev.

  7. 'Mutum 150 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara'

    Yanzu haka ana ci gaba da aikin nemo gawarwakin sauran mutane da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Kwara da ke Najeriya.

    Rahotanni sun ce jirgin ya kife ne a ranar Lahadi da daddare, inda yake ɗauke da mutane kimanin 300 waɗanda suka fito daga wajen biki.

    Wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin jihar Kwara, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun gwamnan jihar ta ce jirgin na ɗauke ne da mutane waɗanda suka fito daga garin Egboti na jihar Neja kan hanyarsu ta zuwa Ƙaramar Hukumar Patigi a jihar Kwara.

    Sanarwar ta ce mutanen da lamarin ya rutsa da su ƴan asalin garuruwan Ebu da Dzakan da Kpada da Kuchalu da kuma Sampi ne, duk a ƙaramar hukumar ta Patigi.

    A lokacin da ya yi magana da manema labaru, sarkin Patigi, Alhaji Ibrahim Umar Bologi, ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa kimanin mutum 150 ne suka rasa rayukansu, inda aka samu nasarar ceto mutum 53.

    Ana yawan samun haɗurran jiragen ruwa a Najeriya, lamarin da kan haifar da asarar rayuka.

    Sau da dama akan alaƙanta hakan da ɗaukar mutane a jiragen fiye da ƙa'ida da kuma rashin bin matakan kariya.

  8. Arsenal ta kusan daukar Declan Rice - rahotanni

  9. An gurfanar da wani mutum kan laifin kashe 'waɗanda suka kore shi aiki'

    An gurfanar da wani mutum a Faransa, bisa zargin sa da kashe wasu mata uku da yake zargin cewa sun tagayyara masa rayuwa.

    An kama Gabriel Fortin mai shekaru 48 a shekarar 2021 a birnin Valence da ke kudanci ƙasar.

    Gabanin haka, an harbe wasu mutum biyu masu aiki a ɓangaren ɗaukar ma'aikata wadanda ke da hannu wajen korar sa daga aiki a shekarun da suka gabata.

    Mace ta uku da aka kashe tana aiki ne a wata cibiyar samar da aikin yi. Ana kuma zargin Mista Fortin, wanda kafafen yada labarai suka yi masa lakabi da "mai kisan masu ɗaukar aiki", da kokarin kashe wani babban jami'a.

    Ya ƙi yin magana da masu bincike tun lokacin da aka kama shi.

    Kisan farko ya faru ne a ranar 26 ga Janairun 2021 a yankin Alsace da ke gabashin Faransa. An harbe shugabar hukumar kula da ma'aikata Estelle Luce a kai a wurin ajiye motoci na kamfanin da take aiki bayan ta tashi daga aiki.

    Da yammacin wannan ranar, kimanin kilomita 50 daga inda kisan farko ya afku, wani da ya yi shiga irin ta masu kai gurasar pizza ya harbi wani mai kula da ma'aikata a gidansa. Amma mutumin da aka harba mai suna Bertrand Meichel, ya tsira da ransa.

    'Yan sanda sun yi amfani da lambar motar da ɗan bindigar ya yi amfani da ita a lokacin da yake barin cibiyar aikin wurin kamo Mista Fortin. Nan take aka alaƙanta shi da aikata kisan da aka yi daga baya.

    A shekara ta 2009 Ms Caclin ta jagoranci sauraron ƙorafe-ƙorafen da suka haifar da korar sa daga aiki, bayan da ya yi rashin nasara a nan sai Mista Fortin ya yi rajista da cibiyar aiki ta Valence, kuma a karshe kudaden sallamarsa daga aiki suka kare.

    Ms Pasquion ba ta taɓa yin wanta mu'amala da shi ba, amma 'yan sanda sun yi imanin cewa yana da wata ƙullaliya da ma'aikatan cibiyar.

    Masu bincike cikin sauri suka alaƙanta shi da harbe-harben da aka yi a gabashin Faransa.

    Estelle Luce da Bertrand Meichel na da hannu cikin korar sa daga wani kamfani a 2006, fiye da shekaru 14 da suka gabata.

    'Yan sanda sun kwashe fiye da shekaru biyu suna tantace bayanan da ke kan kwamfutarsa. Sun ce suna da ƙwararan shaidun da ke nuna ɓacin ransa, da kuma ƙoƙarin bin diddigin yanayin rayuwar waɗanda ya kashe daga baya.

  10. Za a bude kasuwar cinikin 'yan kwallo a Ingila daga ranar Laraba

  11. Ghana ta yi ankararwa game da ƙaruwar 'yan damfara ta hanyar soyayya

    Hukumar tsaron Intanet ta Ghana ta fitar da ankararwar ne, tana gargaɗin mutane game da ƙaruwar damfara ta hanyar amfani da soyayya a ƙasar.

    Wani sabon nau’in damfara ne inda mutane suke amfani da bayanan ƙarya a shafukan sada zumunta musamman manhajojin ƙulla soyayya ko kuma ta hanyar aika saƙonnin imel don neman abokin soyayya ga mutanen da suke hari.

    Ƙwararru sun ce ’yan damfara sukan yi bincike mai zurfi a kan wadanda suke hari ta hanyar sa ido kan dabi’unsu a shafukan sada zumunta.

    Da zarar sun samu yardarsu, sai su yi kokarin ci da gumin mutum ta hanyar karɓar kayayyaki masu daraja kamar kudi, dukiya ko jari. Suna kuma amfani da matsalolin da mutum ke ciki kamar kadaici da rashin kwanciyar hankali da sauransu sannan su yi iyakar ƙoƙarinsu wajen kauce wa haɗuwa ido da ido.

    Hukumar tsaron Intanet ta shawarci jama’a kada su ba da tallafin kuɗi ga mutumin da suka hadu ta intanet kawai. Haka kuma su guji bayar da bayanan sirri ko tsiraici ga waɗanda ba su taɓa haduwa da su ba a zahiri.

    A watan jiya, an kama wata ‘yar Ghana mai suna Mona Montrage, wadda aka fi sani da suna Hajia4Real, kuma iza ƙeyarta daga Birtaniya zuwa Amurka domin ta fuskanci shari’a kan zargin soyayyar damfara.

    Ta dai musanta aikata laifin.

  12. Gargadar da jiragen sama ke shiga a sama ta ƙaru

    Gargadar da jiragen sama suke shiga a sararin samaniya lokacin da suke keta iska za ta ƙaru saboda ƙaruwar ɗumamar yanayi a duniya, in ji masu bincike.

    Masu ilmin kimiyya a Jami'ar Reading ta Birtaniya sun yi nazarin gargada a yanayin iska tangararau, wanda ya fi wahalar kauce wa ga matuƙan jiragen sama.

    Sun gano cewa matsananciyar gargada ta ƙaru da kashi 55% daga 1979 zuwa shekara ta 2020 a kan hanyar da ta keta tekun Arewacin Atlantika mai yawan hada-hada.

    Sun alaƙanta ƙaruwar gargadar da aka samu a kan sauye-sauyen gudun iska a ƙololuwar sama sakamakon iska mai zafi daga gurɓataccen hayaƙi.

    "Sakamakon binciken da aka shafe tsawon shekara goma ana yi, ya nuna cewa sauyin yanayi na ƙara haddasa gargadar iskar gari tangaras a nan gaba, a yanzu muna da shaidar da ke nuna cewa tuni aka fara samun hakan," a cewar Farfesa Paul Williams, wani masanin kimiyyar iskar sararin samaniya da suka yi haɗin gwiwar rubuta rahoton.

    "Kamata ya yi mu zuba kuɗi cikin harkokin inganta hasashe da gano gargadar da ke gaba, don hana iska mai tudu da kwari haddasa wa jiragen shiga gargada mai tsanani nan da shekaru masu zuwa.

    "Hanyoyin jiragen sama daga Amurka zuwa yankin Arewacin Atalantika sun samu matuƙar ƙaruwar gargada. Nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya da Kudancin Atalantika ma ana samun gagarumar ƙaruwar gargada.

  13. Mbappe ya sanar da PSG ba zai wuce 2024 a kungiyar ba

  14. Jibrin Falgore ya zama shugaban majalisar dokokin Kano

    An rantsar da Onarabul Jibrin Ismail Falgore na jam'iyyar NNPP daga mazaɓar Rogo a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Kano ta 10, inda kuma Onarabul Muhammad Bello Ɓutu-Ɓutu ya zama mataimakinsa.

    Matakin ya zo ne bayan ‘yan majalisar sun amince da zaɓensu ba tare da hamayya ba.

    Mukaddashin magatakardan majalisar, Ali Maje ne ya rantsar da sabon shugaban majalisar da mataimakinsa.

    Ita ce majalisar dokoki ta goma da ake ƙaddamarwa tun bayan komawar Najeriya kan turbar dimokraɗiyya a 1999.

    Jam’iyyar NNPP ce take da rinjaye a majalisar ta Kano, ɗaya daga cikin majalisun dokokin jihohin Najeriya mafi daɗewa.

    Jam’iyyar APC wadda ta kasancewa mai rinjaye a baya, yanzu ta koma mai adawa a majalisar.

    Garba Yau Gwarmai ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Tsanyawa ya ce duk da haka bangaren masu rinjayen suna buƙatar su.

    Jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano tana da 'yan majalisa 26 a cikin 40, yayin da APC take da 'yan majalisa 14.

  15. 'Yar Najeriya ta kafa tarihin zama wadda ta fi daɗewa tana girki a duniya

    Kundin Bajinta na Duniya, wato Guinness World Records ta tabbatar da 'yar Najeriya, Hilda Bassey a matsayin wadda ta kafa tarihi wajen shafe lokaci mafi tsawo tana girki.

    Masu kula da kundin a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Talata, sun ce “Bayan cikakken nazari kan dukkan shaidu, a halin yanzu kundin tarihin Guinness na iya tabbatar da cewa Hilda Effiong Bassey, wadda aka fi sani da Hilda Baci, ta karya tarihin, inda ta shafe tsawon sa'a 93 da minti 11 tana girki."

    Hilda mai shekara 27 ta fara girkin ne a ranar Alhamis 11 ga watan Mayun 2023 kuma ta ci gaba har zuwa ranar Litinin 15 ga watan Mayu.

    Ta girka abinci iri daban-daban har fiye da 100 a tsawon kwana hudu.

    Hilda dai ta yi yunƙurin kafa tarihin shafe tsawon sa'a 100 tana girki ne ba tare da katsewa ba, amma sai masu kula da kundin tarihin suka cire kusan sa'a bakwai a lissafin da ta yi saboda kuskuren ƙidaya a lokacin gajeren hutu da ta riƙa yi.

    Hilda ta karya tarihin Lata Tondon 'yar Indiya wadda ta yi sa'a 87 da minti 45 tana dafa abinci ba tare da katsewa ba.

  16. Akpabio da Tajuddeen sun zama shugabannin majalisa ta goma a Najeriya

  17. Ana tuhumar mutanen da suka yi azumin mutuwa a Kenya da yunƙurin kashe kansu

    Mutane 65 da suka tsira daga azumin mutawa a Kenya na fuskantar tuhuma kan yunƙurin kashe kansu bayan sun ƙi cin abincin da aka ba su a cibiyar ceto da aka kai su.

    A zaman kotu a ranar Litinin, masu gabatar da kara sun nemi a daure wadanda suka tsira a gidan yari inda za a iya tantance lafiyar kwakwalwa su saboda cibiyar ceto ba za ta iya rike su ba. Ana sa ran yanke hukunci nan gaba a cikin mako.

    Kisan kai laifi ne a Kenya a ƙarƙashin dokokin da Turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka gabatar.

    An soke wadannan ka'idoji a Ingila fiye da shekaru 60 da suka gabata kuma masu fafutuka na Kenya suna fafutukar kawo karshen ƙa'idoji a kasarsu suma.

    Mutanen 65 da suka tsira da ransu an ce mabiyan Fasto Paul Mackenzie ne, wanda ake zargin shi ne shugaban kungiyar asirin, wanda aka ce ya shawo kan mabiyansa da su yi azumi har su mutu domin su shiga aljannah.

    Sama da gawarwaki 280 aka gano a cikin kaburbura marasa zurfi a cikin dajin Shakahola da ke kusa da gabar teku inda faston ya gudanar da aiki an tono 10 a ranar Litinin.

    Rahotan binciken gawarwakin mutane ya nuna cewa yawancin wadanda abin ya shafa da suka hada da ƙananan yara sun mutu ne saboda yunwa amma wasu an shaƙe su ne ko kuma anyi an yi musu dukan tsiya.

  18. Madugun adawar Kamaru John Fru Ndi ya mutu

    John Fru Ndi, wani jigo a siyasar Kamaru tsawon shekaru da dama, ya rasu yana da shekaru 82.

    Ya kafa jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front (SDF) a shekarar 1990, kuma yana kan gaba wajen girka mulkin dimokradiyyar jam'iyyu adawa a kasar Kamaru.

    Ya kasance mai ya kare 'yancin tsiraru masu amfani da harshen Ingilishi a kasar.

    A cewar wata sanarwar manema labarai da abokansa na SDF suka fitar, Fru Ndi ya mutu a Yaoundé babban birnin kasar a yammacin ranar Litinin bayan doguwar jinya.

    Ayyukansa sun hada da takarar shugaban kasa da dama kuma ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben 1992 na gaskiya, wanda aka ce Shugaba Paul Biya ya ci a karo na biyu.

    Fru Ndi ya bai wa kowa mamaki a shekarar 2018 lokacin da ya yanke shawarar kin tsayawa takarar babban mukami inda yake shirin yin ritaya a matsayinsa na shugaban jam'iyyar sa a karshen wannan shekara.

  19. Wane ne Godswill Akpabio, sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya?

  20. Masarautar zazzau ta soke hawan daba a Sallar Idin bana

    Masarautar Zazzau ta soke bikin hawan daba a bikin Babbar Salla mai zuwa.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Mallam Yusuf Abubakar Hayat, sakataren masarautar yana sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 12 ga watan Yuni.

    Ya ce matakin ya zo ne bayan tafiyar da Mai martaba Sarkin Zazzau Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

    Sanarwar ta kara da cewa, Sarkin wanda tuni ya taya al'ummar masarautarsa ta Zazzau murnar barka da sallah, ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya su gudanar da addu’o'i don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

    Ana shafe tsawon kwana uku ana hawan dawaki a Masarautar Zazzau duk shekara, a wani ɓangaren na bikin babbar salla.