Gwamnatin Japan ta sanar da wani shirin tallafi don karfafa haihuwa

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES
Firaministan kasar Japan Fumio Kishida, ya sanar da wasu tsare-tsare domin hana raguwar yawan haihuwa a kasar.
Mista Kishida ya shaida wa taron manema labarai cewa wannan ita ce dama ta karshe da kasar Japan ke da ita cikin shekara goma ta tunkarar yawan tsofoffi da suka yi yawa a cikin al'ummarta.
Yayin da ingantuwar rayuwa tsakanin al'ummar Japan ya kara yawan tsawon rai, raguwar yawan haihuwa na barazana ga ɓangaren ayyuka na ƙasar saboda yadda tsofaffi ke yin ritaya.
Za a aiwatar da manufofin da aka sanar daga shekara mai zuwa kuma sun hada da biyan tallafi ga yara da daukar nauyin kudin haihuwa, da hutun musamman ga iyaye da canza yanayin al'adu na wurin aiki ga iyaye.
Firaministan Japan ya yarda cewa masu daukar ma'aikata na nuna wariya ga masu yara saboda suna ganin kasancewar yara na iya zama dalilin rage mayar da hankali kan aiki.
Firaministan ya ce zai yi ƙokarin aiwatar da manufar ba tare da kara haraji ba, ko da yake wasu manazarta sun nuna shakku kan wannan alwashin ganin irin kudaden da za a yi amfani da su wurin aiwatar da manufar.














