Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Kimanin mutum 150 sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kwara'

Wannan shafi ne da ke kawo abubuwan da ke wakana a Najeriya da ƙasashe makwabtanta da kuma sauran sassan duniya kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, A'isha Babangida and Haruna Kakangi

  1. Tsohon shugaban Amurka Trump ya isa Miami don gurfana gaban kotu

    Wani alkalin kotun tarayya a Amurka ya yi watsi da bukatar barin kafofin yaɗa labarai su dauki hotuna da bidiyo a bayyanar tsohon shugaban ƙasar Donald Trump a kotu da ke Miami yau Talata.

    Kazalika, an haramta wa 'yan jarida zuwa da wayoyinsu na salula a yayin zaman kotun.

    Mista Trump zai bayyana gaban kotun ne don fuskantar tarin tuhume tuhume game da laifukan da suka danganci rike wasu takardun sirrin ƙasa bayan ya bar mulki da kuma hana jami'an tsaro takardun a lokacin da suka yi ƙoƙarin karɓo su.

    Tuni dai Mista Trump ya musanta aikata ba daidai ba.

    Wani lauya da ya kasance mai bayar da shawara na musamman ga kwamitin harkokin shari’a na majalisar wakilan Amurka lokacin da ake shirin tsige Trump karo na biyu, Norman Eisen, ya faɗa wa BBC cewa tsohon shugaban zai shiga mawuyacin hali a kotun.

    Ya ce; "Ina ganin tuhumar tana da ƙarfi sosai.

    Daga cikin tarin matsalolin Donald Trump, wannan kila za ta kasance laifin shari’a mafi girma. Saboda akwai kwakkwarar shaidar da ke nuna cewa ya dauki abin da muke kira bayanan tsaron ƙasa, da tsare-tsare na kai harin sojoji a kan wasu kasashe da shirye-shirye na yadda za a iya kawo mana hari da bayanai a kan sirrin nukiliya da abokan gabarmu da kuma abokai da kawayenmu.

    Ya ɗauki duka waɗannan ba tare da wani dalili na shari’a da zai sanya shin yin haka ba.''

  2. An yi gargaɗi game da yiwuwar ƙara shiga shiga yunwa a duniya

    Ukraine da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargadin fuskantar gagarumar matsalar abinci a duniya sanadin fashewar madatsar ruwan Kakhovka.

    Shugaban hukumar ayyukan jin kai a Majalisar Dinkin Duniyar, Martin Griffiths ya shaida wa BBC cewa akwai damuwa sosai a kan mummunar illar da aka yi wa abin da ya kira rumbun abinci na duniya.

    Ya ce abin da nake tunani abu ne mai muhimmanci wanda zai iya daukar watanni masu yawa.

    Ya kuma ce akwai yiwuwar farashin kayan abinci zai iya tashi.

    Ministan noman Ukraine, ya ce manyan kayan amfanin gonar da fashewar madatsar ruwan ta shafa sun haɗar da waken suya da dawa da alkama da kuma tsirran da ake sarrafa man girki da su.

  3. Jama'a, barkanmu da safiya

    Masu bibiyar wannan shafi na labarai kai tsaye daga BBC Hausa, barkanmu da sake kasancewa.

    Shafin zai kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Njaeriya da ma sauran sassan duniya.

    Mukhtari Adamu Bawa da Aisha Babangida ne ke muku sallama a yau Talata.

    Ku ci gaba da bibiyarmu don sanin halin da duniya take ciki daga yanzu har zuwa dare.