Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda gwamnoni 28 suka sha ranstuwar kama aiki a Najeriya
Wannan shafi ne da ke kawo muku yadda ake rantsar da sabon shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi a Najeriya.
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Umar Mikail
Shugabannin Afrika sun isa Abuja domin bikin rantsar da Tinubu
Shugabannin Afrika da dama ne suka isa Najeriya domin halartar bukin rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na 16.
An takaita zirga-zirga a kusa da dandalin Eagle Square a Abuja inda za a gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban Najeriyar.
Rahotanni sun ce akalla shugabannin kasashen Afrika 20 ne za su halarcin bukin.
Shugaban Rwanda, Paul Kagame da na Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da ta Tanzania Samia Suluhu Hassan duk sun isa Abuja domin halartar bukin.
Haka kuma shugaban Ghana, Nana Akufo Ado da na Nijar, Bazoum Mohammed da na Chadi Mahamat Déby duk sun isa Abuja.
Wane ne Kashim Shettima?
An wayi gari ana yayyafi a Abuja
Yayin da ake rantsar da sabon shugaban ƙasa, an wayi gari a birnin Abuja da yayyafi inda gajimare ya lulluɓe sararin samaniya.
Barka da warhaka!
Masu bibiyar mu a wannan shafi barka da safiyar Litinin.
A wannan shafi za mu kawo muku duk abubuwan da ke faruwa a wajen rantsar da sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima a birnin Abuja.
Haka nan za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a jihohi inda ake rantsar da gwamnoni da mataimakansu.
Kuma kamar kullum za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a faɗin Najeriya da ma sassan duniya.
Da fatan za ku bibiye mu a shafukanmu na sada zumunta a facebook da twitter da kuma instagram, haka nan za ku iya kallon dogayen bidiyo a shafinmu na BBC Hausa YouTube.