Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda gwamnoni 28 suka sha ranstuwar kama aiki a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku yadda ake rantsar da sabon shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi a Najeriya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Muhammad Annur Muhammad and Umar Mikail

  1. An rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya

  2. Ana shirin ranstar da Sanwo-Olu a karo na biyu

    An fara bikin rantsar da Cif Babajide Sanwo-Olu a matsayin gwamna a jihar Legas.

    Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya lashe zaben gwamna karo na biyu bayan takara mai zafi tsakaninsa da jam'iyyun adawa da ya sanya jihar cikin yanayi na zullumi a lokacin zaben.

  3. Uba Sani ya sha rantsuwa ya gaji El-Rufai a jihar Kaduna

    Sanata Uba Sani ya zama sabon gwamnan jihar kaduna bayan da aka rantsar da shi inda ya gaji Mallam Nasir El-Rufai a bikin da aka yi yau Litinin a dabdalin Murtala da ke tsakiyar birnin Kaduna.

    Sanatan ya yi nasara ne tare da mataimakiyarsa Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, wadda ta kasance mataimakiyar El-Rufai, a karkashin jam'iyyar APC.

  4. An rantsar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar kano

    An rantsar da Injiniya Abba kabir Yusuf a matsayin sabon gwamnan Jihar kano, a bikin da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata a birnin Kano.

    An rantsar da shi tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

    Dubun dubatar magoya bayan jam'iyyar NNPP ne sanye da fararen kaya da jajayen huluna ga maza yayin da mata ke sanye da jajayen dan-kwali ko mayafi ko hijabi a wurin taron.

    Sarakunan jihar ta Kano da jagoro kuma dan takarar jam'iyyar ta NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan baki ne suka halarci bikin.

    Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya yi nasara ne a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris inda ya kayar da dan takarar jam'iyya mai mulki, APC, Nasiru Yusuf Gawuna.

  5. Ga ƙalubale biyar da ke jiran shugaba Bola Tinubu

    Ana yawan bayyana Najeriya a matsayin uwa ma ba da mama a Afirka saboda yawan al'ummarta da kuma ƙarfin tattalin arziƙinta sai dai tana fama da wasu gagaruman matsaloli - da za su tunkari Bola Tinubu yayin da ya karɓi mulki ranar Litinin.

    Ƴan Najeriya, da waɗanda ma ba su jefa masa kuri'a ba, za su so su ga sauyi cikin hanzari daga Tinubu.

    Ga wasu daga cikin manyan ƙalubalen da zai fuskanta da ma yadda watakila zai warware su.

    • Soke tallafin man fetur
    • Rashin samun cikakken goyon baya
    • Daidaita tattalin arziƙin ƙasa
    • Garkuwa da mutane da matsalar tsaro
    • Ƙoƙarin kula da lafiya da sauran batutuwa
  6. Tinubu ya sha rantsuwa a matsayin shugaban ƙasar Najeriya

    Tsohon gwamnan jihar Lagos, Sanata Bola Ahmad Tinubu ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban ƙasar Najeriya.

    Ya kasance shugaban kasa na goma sha shida a jerin shugabannin ƙasar.

    Ya yi alkawarin yin biyayya a kundin mulkin Najeriya tare da yin aiki ba tare da nuna son zuciya ba.

    Tinubu ya sanya hannu a takardar rantsuwar kama aiki.

  7. Kashim Shettima ya sha rantsuwa a matsayin mataimakin shugaban Najeriya

    Tsohon gwanan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya yi rantsuwar kama aiki a mastayin sabon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya.

    Ya yi alkawarin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya tare da yin aiki ba tare da nuna son zuciya ba.

    Shettima ya sanya hannu a takardar rantsuwar kafin daga bisani ya koma wurin zamansa.

  8. Buhari ya isa Eagle Square

    Yanzu haka ayarin motocin shugaban kasa mai barin-gado Muhammadu Buhari ya isa dandalin Eagle Sqaure.

    Ayarin motocin na tafiya a-hankali-a-hankali tare da sulken ayarin jami'an tsaro, inda suka shiga cikin filin bikin a abin da ke zama girmamawa ta musamman ta karshe ga Buharin a matsayin shugaban kasa.

    Buharin ya kasance sanye da farar babbar-riga inda ya je ya tsaya domin sauraren taken Najeriya, bayan da ya fita daga motarsa.

  9. Manyan baƙi na ci gaba da halartar wajen rantsuwa

    Manyan baki na ci gaba da halartar filin Eagle Square, a Abuja, inda ake shirin musayar mulki tsakanin shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado da kuma mai jiran-gado Bola Ahmed Tinubu.

    Akwai shugabannin kasashe daban-daban da za su halarci mika mulkin da kuma rantsuwa, baya ga manya daga cikin kasar, kama daga ƴan siyasa da ke cikin gwamnati da kuma shugabannin gargajiya.

  10. Lokacin da shugaba Buhari ke ficewa daga fadar shugaban ƙasa

    Wannan ne lokacin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ficewa daga fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock domin zuwa dandalin taro na Eagle Square wajen rantsar da sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

  11. Fadar Shugaban Ƙasa ta yi tsit tana dakon sabon shugaba

    Yayin da ake can ake haramar rantsar da sabon shugaban Najeriya, fadar shugaban ta Aso Villa (Aso Rock Presidential Villa) ta yi tsit tana dakon zuwan sabon shugaban Bola Ahmed Tinubu wanda zai karbi mulki yau a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

    Fadar ta Aso Rock da ke Abuja ita ce mazaunin shugaban kasar, tun bayan da aka kammala ta a 1991, bayan da babban birnin kasar ya koma Abuja daga Lagos.

  12. `Yan kwankwasiyya sun cika a filin kwallo na Sani Abacha a Kano

    Cincirindon magoya bayan jam'iyyar NNPP a Kano kenan, ke kokarin shiga filin wasa na Sani Abacha wurin da za a rantsar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.

    Taron wanda aka shirya za a fara da safiyar yau zai samu halartar manyan baki daga Kano da wajen kasa ciki har da wasu masu rike da mukaman sarauta.

    A lokacin zaben da aka gudanar watanni biyu da suka wuce, Abba na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya doke Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) inda ya lashe zaben.

    Uban siyasar sabon gwamna, Rabi'u Musa Kwankwaso na cikin mutanen da ake sa ran za su halarci bikin rantsar da sabon gwamnan.

  13. Tinubu ya isa dandalin Eagle Square domin shan rantsuwa

    Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa dandalin taro na Eagle Square da ke Abuja, inda za a rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya.

    Tinubu zai sha rantsuwar kama mulki ne tare da zaɓaɓɓen mataimakinsa, Kashim Shettima.

    Mutanen biyu sun lashe zaɓen shugaban ƙasa ne da aka gudanar a watan Fabarairun 2023, sai dai ƴan takara na jam'iyyar adawa na ƙalubalantar nasarar a kotu.

  14. Mutane sun cika dandalin Murtala Square a Kaduna wajen rantsar da sabon gwamna Uba Sani

  15. Kashim Shettima ya isa dandalin rantsar da sabon shugaban ƙasa

    Kashim Shettima, wanda shi ne zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa ya isa dandalin taro na Eagle square, inda shi da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu za su sha rantsuwar kama mulki a yau.

  16. An tsaurara tsoro yayin da ake shirin rantsar da sabon shugaban ƙasa

    Jami’an tsaro sun tsaurara matakai a dandalin Eagle Square, wurin da ake bikin rantsar da sabon zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima don tabbatar da bikin ya wakana lami lafiya.

    Titunan da ke zuwa dandalin Eagle Square sun kasance da shinge, kuma mutanen da ke da takardar shaida ta musamman ne kawai ake ba su damar shiga.

    A yau Litinin, 29 ga watan Mayu Muhammadu Buhari yake mika mulki ga Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban kasar Najeriya.

    Bola Ahmed Tinubu ya ci zaɓenshugaban ƙasar ne wanda aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu na wannan shekara a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, sai dai ƴan hamayya na ƙalubalantar sakamakon a kotu.

  17. An hana Ganduje da Soludo shiga wurin manyan baki na alfarma

    Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bukin rantsar da sabon shugaban kasa a Eagle Square da ke Abuja.

    Ganduje da matarsa Hafsat sun yi kokarin shiga cikin wurin da ake kebe wa manyan baki masu alfarma amma sai jami'an tsaro suka dakatar da shi suka ce takardar gayyatar da yake da ita koriya ce kuma sai mai takardar gayyata mai ruwan gwal ne zai shiga cikin wannan bangaren.

    Ya jira na tsawon fiye da minti 10 kafin ya dauki kaddara ya koma bangaren da aka tanadar wa baki irinsa.

    Shi ma gwamnan jihar Anambra, Charles Soludoya yi kokarin shiga wannan bangaren amma kamar Ganduje shi ma jami'an tsaro sun taka masa birki.

  18. Wane ne Tinubu?

  19. Tinubu ya shafe shekaru takwas a matsayin gwamnan Legas

    Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara takwas.

    Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.

    Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da bangaren aikin gwamnati.

    Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma'aikatu irinsu ma'aikatar gidaje da ma'aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.

    A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.

    Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al'ummarta.

    Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al'umma.

  20. Yau za a rantsar da Tinubu a matsayin sabon shugaban Najeriya

    A yau Litinin za a rantsar da sabon zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, a babban birnin kasar, Abuja.

    Zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari ne wanda ya kammala wa'adinsa na biyu na shekara hudu-hudu.

    Tinubun ya samu wannan matsayi ne bayan da ya yi nasara a zaben shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabarairu a matsayinsa na dan takarar jam'iyya mai mulki AP, nasarar da manyan 'yan hamayya ke kalubalanta a kotu.

    Ana ganin bikin na yau a matsayin wani babban abin murna da cikar buri na Tinubun kasancewar ya jima da wannan buri na mulkar kasar wadda ita ce mafi yawan jama'a a Afirka.

    Za a gudanar da bikin ransatar da shi ne a yau din a filin Eagle Square, inda zai yi alkawarin tafiyar da kasar bisa adalci da kare al'umma da kasar baki daya.

    Asiwajun zai karbi mulkin kasar wadda ta kasance da matukar rarrabuwar kai a wannan lokaci, inda wasu ma ke gani ba a taba samun rarrabuwar kai kamar a yanzu ba sakamakon yadda zaben shugaban kasar ya kasance.

    A jawabin ban-kwana da Shugaba Buhari ya yi jiya Lahadi ya ce ya yi iya kokarinsa wajen hidimta wa kasar.

    Sai dai masu sukar lamirinsa na cewa a mulkinsa kasar ta kara talaucewa ga dimbin bashi da ya ciyo ga kuma tarin kalubale na tsaro fiye da yadda ya same ta a 2015.

    Sabon shugaban kasar zai fuskanci kalubale na tsaro da fatara da talauci da rashin aikin yi da kuma cin hanci da rashawa.

    Bola Tinubun zai gudanar da mulkin kasar tare da kashim Shettima a matsayin mataimakinsa tsawon shekara hudu, bayan nan kuma yana da damar sake neman wani wa'adin na biyu kuma na karshe shi ma na tsawon shekara hudu, idan har ba shari'ar da ke kalubalantar zaben nasa ta zo da sauyi ba.