Biki ya kankama, Sarki Charles ya fito fadar Buckingham a cikin keke mai adon zinare

Asalin hoton, Reuters


Asalin hoton, PA Media
Wannan shafi ne da ke kawo muku ƙayatattun abubuwan da ke faruwa a wurin naɗin Sarki Charles III, kai-tsaye daga birnin Landan
Haruna Kakangi and Buhari Muhammad Fagge

Asalin hoton, Reuters


Asalin hoton, PA Media

Firaiminista Burtaniya Rishi Sunak ya bayyana wannan rana ta yau a matsayin "gagarumin lokacin da ƙasa ba za ta manta da shi ba" kuma "lokacin haskakawar Burtaniya a sabon yanayi".
"Babu wata ƙasa da za ta iya shirya wannan biki kamar haka" ya wallafa a Twitter.
Ya kuma bayyana wannan taron a matsayin sabon ƙarni da za a shiga.
Ya kuma kammala rubutun Twitter ne da cewa "Allah ya taimaki Sarki".

Asalin hoton, Reuters
Mutane sun yi mata maraba, yayin da Dr Jill Biden, wato mai ɗakin shugaban Amurka, Joe Biden ta isa cocin Westminster a cikin jerin-gwanon motoci uku.
Ta isa wurin ne tare da jikarta Finnegan.

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, PA Media

Yanzu haka dai abubuwa sun fara kankama, musamman a fadar Buckingham da ke birnin Landan wurin naɗin sarautar Sarki Charles.
Tuni masu kallo suka yi dafifi domin ganin abubuwan da za su wakana.
Ko a cikin tsakar dare an ci gaba da hada-hada a birnin Landan, inda mutane suka hallara a wurare na musamman domin ganin yadda bukukuwan za su gudana.

Birnin Landan ya ɗau harami, an kuma kammala duk wasu shirye-shiryen naɗin sarautar sarki Charles na uku, nan da sa'a guda za a fara gagarumin bikin, irin shi na farko shekaru 70 da suka wuce.
A wannan wuri aka naɗa mahaifiyar Sarki Charle, sarauniya Izabel da 2, a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1953, ta na matashiya 'yar shekara 25, bayan rasuwar mahaifinta Sarki George na 6.
An tsaurara matakan tsaro, an kuma girke dubban 'yan sanda.
Dandazon mutane sun kwashe daren jiya a wajen Fadar Buckingham, domin su shaida duk abubuwan da za su faru kama daga fitowar Sarki Charle na 3 da Sarauniya Camilla daga fadar zuwa Westminster Abbey.
Sama da fitattun mutane da shugabannin ƙasashe, da sarakuna 2,000 ne za su shiga Westminster don shaida ɗorawa sabon sarkin kambu mai ɗauke da duwatsu masu daraja har 444, ciki akwai zinare, da lu'u-lu'u da yakutu.



Asalin hoton, Reuters
Ana yin shara ta ƙarshe a barandar sama ta fadar Buckingham gabanin fitowar Sarki Charles domin ɗaga wa masu kallo hannu a jerin abubuwan da za a yi na naɗin sarautar sa a yau.
Jama'a barkanmu da warhaka.
Wannan rana ce mai ɗimbin tarihi inda ake bikin naɗin Charles III a matsayin sarkin Ingila.
Sarkin ya samu hawa kan wannan karaga ce bayan rasuwa mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II a ranar 8 ga watan Satumba, 2022.
Rana ce ta baje-kolin daɗaɗɗiyar al'ada wadda ta samo asali sama da shekaru 1,000 da suka gabata.
Wannan shafi zai kawo muku duk abubuwan da suke faruwa kai-tsaye daga birnin Landan.
Ku latsa alamar kunnawa da ke sama domin kallon yadda komai ke faruwa kai-tsaye.
A sha kallo lafiya!