'Yar gidan Mugabe ta mallaki katafaren gidan $80m - Takardun Kotu
Wannan shafi ne da zai riƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage
`Yan sanda sun kewaye gidan tsohon shugaban ƙasar Zambia a Lusaka

Asalin hoton, Getty Imagesg
`Yan sandan Zambiya sun yi wa gidan tsohon shugaban ƙasar, Edgar Lungu da ke babban birnin kasar Lusaka ƙawanya, inda suka bukaci a basu damar gudanar da bincike a gidan.
Lauyan Mista Lungu, Jonas Zimba ya shaida wa gidan talabijin na Diamond TV cewa jami`an yan sanda na gudanar da bincike, kan wasu motoci uku da ake zargi matar tsohon shugaban ƙasar da mallaka.
Ya ce binciken ya biyo bayan ƙorafin da aka shigar kan matsar tsohon shugaban ƙasar, Esther Lungu kan mallakar motocin.
Kawo yanzu `yan sandan ba su fitar da wata sanarwa game da ci lamarin ba.
Tsohuwar jam`iyya mai mulki ta Patriotic Front a ƙasar (PF), ta bayyana tura jami'an tsaron a mastayin keta kariyar da doka ta bai wa mista Lungu.
A zaɓen watan Agusatn 2021 ne dai mista Lungu ya sha kaye a hannun Hakainde Hichilema.
Tinubu ya isa Rivers a ziyarar kwanaki biyu

Asalin hoton, Nyesom Wike/Twitter
Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa Fatakwal babban birnin jihar Rivers a wata ziyarar kwana biyu da ya kai jihar.
Tinubu ya je jihar ne domin ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnan jihar Nyesom Wike ya gudanar.
Ayyukan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai ƙaddamar sun haɗar da gadar samar da ginin kotun majistare.
Mista Wike tare da muƙarraban gwamnatinsa ne suka tarbi zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman birnin fatakwal.
Ɗaruruwan magoya bayan Tinubu da Wike ne suka taru domin yi wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar tarba.
Tuni gwamna Wike ya ayyana ranar ziyarar a matsayin ranar hutu ga ma'aikata a faɗin jihar domin bai wa al'umma damar tarbar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.
Babban sakataren MDD ya isa Kenya

Asalin hoton, Kenya Foreign Ministry
Babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya isa ƙasar Kenya domin lura da ayyukan jin-ƙai da yanayin tsaro a ƙasar Sudan, sakamakon faɗan da aka kwashe makonni ana gwabzawa.
Ministan harkokin wajen Kenya, Alfred Mutua ne ya tarbi Mista Guterres da safyar ranar Laraba a babban filin jirgin saman Nairobi, babban birnin ƙasar.
A ziyarar tasa ta kwanaki biyu, babban jami`in na MDD zai tattauna da shugaba William Ruto tare da ganawa da dukkan shugabannin hukumomin MDD a Nairobi.
Bagororin da ke rikici da juna a Sudan sun amince da tsagaita wuta na kwanaki bakwai da za a fara ranar Alhamis.
Rikicin Sudan: Ana sa ran jirgin farko ɗauke da 'yan Najeriya zai isa ƙasar

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Najeriya ta ce rukunin farko na 'yan ƙasar da za a ƙwaso daga Saudiyya sakamakon rikicin Sudan za su isa Najeriya nan da sa'o'i masu zuwa.
Shugabar hukumar da ke kula da 'yan Najeriya mazauna ƙetare Abike Dabiri -Erewa ce ta bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar.
Ta ofishin jakadancin Najeriya a Masar ya kammala tattara 'yan ƙasar da aka kwaso daga Sudan zuwa ani gari da ake kira Aqeel na kusa da kan iyakan ƙasar domin ɗauko su.
Ta ƙara da cewa a ranar Laraba da safe ne ake sa ran kammala kwaso 'yan ƙasar da suka rage a Sudan zuwa Masar.
Misis Dabiri ta ce an kammala shirye-shiryen kwaso ɗaliban daga filin jirgin saman Aswan zuwa Abuja.
ta ƙara da cewa tuni jirgin saman Air Peace da na rundunar sojin saman ƙasar na cikin shiri domin ƙwasar ɗaliban zuwa Abuja bayan kammala tantacewa.
Rikicin da ya ɓarke tsakanin manyan hafsoshin sojin ƙasar Sudan ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane, tare da jikkata mutane da birnin Khartoum.
Matsin tattalin arziƙi na tilasta wa iyaye yi wa yara auren wuri - UNICEF

Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi gargaɗin cewa tashin hankalin da duniya ta fuskanta, kamar ɓarkewar annobar korona sun daƙile ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da aurar da ƙananan yara a duniya.
A wani sabon rahoto, UNICEF ta ce a shekaru goma da suka wuce, an samu raguwar aurar da yara ƙanana 'yan ƙasa da shekaru 18, amma ɓarkewar korona da tashe-tashen hankula, da matsin tattalin arziki da sauyin yanayi sun tilasta wa iyaye aurar da 'ya'yansu mata tun kafin su girma.
UNICEF ya yi ƙiyasin cewa yara mata miliyan 12, ake aurarwa a duk shekara, inda suka kira matakin da take hakki tare da tauye wa yaran ƙuruciya, kuma lamarin ya fi munana a ƙasashen Afirka, kudu da hamadar Sahara.
Fasahar Artificial Intelligence na yi wa kamfanoni barazana
Hannayen jarin manyan kamfanonin da ke saida kayan karatu sun fai, sakamakon damuwar da ake nunawa kan fasahar nan ta Artificial Intelligence.
Hannayen jarin kamfanin Chegg na Amurka da ke samar da bayanai kan fasahar, sun fadi da kusan kashi 50 cikin 100 a jiya Talata, ya kuma yi asarar biliyoyin daloli.
Shugaban kamfanin ya ce samun ƙaruwar ɗalibai da ke son bayanai kan fasahar ta AI ya ƙara wa kamfaninsa daraja.
Hannayen jarin kamfanin Pearson na Birtaniya sun fadi da kashi 15, dandalin ɗaukar darasi na Duolingo ya fadi da kashi 10.
A gobe Alhamis Fadar white House za ta gana da shugaban kamfanin Google, da Microsoft, domin tattaunawar ƙeƙe-da-keke kan haɗarin da ke tattare da fasahar AI
Buhari zai tafi Landan bikin naɗin sarkin Birtaniya

Asalin hoton, Nigerian Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai Landan domin halartar bikin naɗin sabon sarkin Birtaniya Charles lll.
A cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari zai bar Najeriya ranar Laraba 3 ga watan Mayu, don halartar bikin naɗin sarki Charles lll.
Za a gudanar da bikin naɗin ne ranar Asabar 6 ga watan Mayu a fadar sarkin da ke Birtaniya.
Sanarwar ta ce gabanin bikin naɗin sarautar, ƙungiyar ƙasashe renon Ingila ta Commonwealth za su gudanar da taron shugabannin ƙasashen ƙungiyar ranar Juma'a 5 ga watan Mayu.
Yayin wannan bulaguron shugaba Buhari zai samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da ministan harkokin ƙasashen waje Geoffrey Onyeama, da ministan yaɗa labarai Lai Mohammed.
Sauran su ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, da Daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar, da wasu manyan jami'an gwamnati.
Mutum 13,000 suka amfana da tallafin ambaliya - Gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, GETTY IMAGES
Gwamnatin Najeriya ta ce fiye da 'yan ƙasar 13,000 ne suka amfana da tallafin ambaliya da ta rabar a fadin jihohin ƙasar da ambaliyar ta shafa.
Babban sakatare a ma'aikatar ma'aikatar Jinkai da kare afkuwar bala'o'i ta Najeriya Dakta Nasiru Sani Gwarzo ne ya bayyana haka ranar Talata Abuja babban birnin ƙasar a wani taron masu ruwa da tsaki na ma'aikatar.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ambato Dakta Gwarzo na cewa ''mutum 13,000 ne suka amfana da tallafiin gwamnatin tarayya a faɗin jihohin ƙasar 16 da ambaliya ta shafa a shekarar 2020 a ƙasar''.
Jihohin da suka samu tallafin sun haɗar da Anambra da Bayelsa da Katsina da Kogi da Benue da Nasarawa da Kwara da Niger da Kebbi da Sokoto da Jigawa da Bauchi da Delta da Rivers da Adamawa da kuma Yobe
Dakta Nasir Gwarzo ya ce wannan ƙari a ne a kan wani asusun tallafin da aka tara domin gudanr da wasu manyan ayyukan a ƙananan hukumomi shida a arewa maso gabashi da arewa maso yammacin ƙasar, inda mutum 27,432 suka amfana.
Ya ƙara da cewa illar da ambaliyar ta yi ya tilasta wa hukumomi haɗa hannu da cibiyoyin bayar da tallafi domin taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.
Ambaliya ruwa ta shekarar 2020 ta haifar da asarar rayuka da ta tarin dukiyoyi a faɗin kasar, kamar yadda Darkat Gwarzo ya bayyana.
Assalamu alaikum
Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.
Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance da ku a daidai wannan lokaci.
