'Yar gidan Mugabe ta mallaki katafaren gidan $80m - Takardun Kotu

Wannan shafi ne da zai riƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Asuba ta gari

    Nan muka kawo karshen rahotanni a wannan shafi na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Alhamis - idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran abokan aiki, Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Hotunan Sarki Charles yana gwajin hawan naɗin sarauta

    An ga Sarki Charles da Camilla, Sarauniyar Consort, suna cikin annashuwa da kuma murna gabanin naɗin sarautar Sarkin da za a yi. were smiling and looked relaxed as they left a dry run of the big day.

    An kuma ga iyalan gidan sarautar na barin cocin Westminster Abbey bayan gwajin hawan naɗin sarauta da za a yi a ranar Asabar.

    King Charles

    Asalin hoton, JAMES WHATLING/KELVIN BRUCE

    Royal family

    Asalin hoton, JAMES WHATLING/KELVIN BRUCE

    PA MEDIA

    Asalin hoton, PA MEDIA

    Royal family

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Sarauniyar Consort ta samu rakiyar mutane zuwa wajen gwajin naɗin sarautar da za a yi
    Royal family

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, An kuma ga Yarima Louis tare da Yariman Wales bayan halartar gwajin naɗin sarautar
    .

    Asalin hoton, PA MEDIA

    Bayanan hoto, Gimbiya ta haɗu da jami'an soji gabanin shirye-shiryen naɗin sarauta a ranar Asabar, inda suke tattaunawa a ziyarar da suka kai Barikin Wellington.
    Naɗin sarauta

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani ɓangare na jami'an sojoji da suka jeru domin yin hoto a wani ɓangare na shirin naɗin sarautar Sarkin Ingila

    Sarkin ya halarci wata liyafa a fadar Buckingham - na farko a mulkinsa - kuma ya haɗu da baƙi ciki har da Dame Doreen Lawrence da mawaƙi Lionel Richie.

    Sarki Charles

    Asalin hoton, PA Media

    .

    Asalin hoton, PA Media

    .

    Asalin hoton, PA Media

    Tuni mutane sun fara taruwa a wani kanti da ke wajen fadar Buckingham, tare da wasu masoya sarauta kamar Faith Nicholson, inda suke yin sansani a cikin tanti don tabbatar da cewa ba su rasa babban wurin kallo ranar Asabar ba.

    .

    Asalin hoton, PA Media

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jami'ai sun kasance suna sintiri a wajen, gabanin naɗin sarautar mai cike da tarihi zuwa Fadar Buckingham
    .

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Tuni an fara shagulgula kamar yadda za a ga a wajen waɗannan ƴan liyafa a cikin Carter Lane na London
    .

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Wani mai zane Claire Eason ya zana wani hoton Sarkin mai tsayi 90 da ƙafa 65 akan Tekun Bamburgh da ke Northumberland
    .

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Wani mai yanka ciyayi na kammala aiki a wani filin da aka sake shimfidawa a dandalin majalisar ƙasar
    .

    Asalin hoton, HISTORIC ROYAL PALACES

    Bayanan hoto, Masu kula da Hasumiyar London sun yaba da irin kujerar naɗin sarauta da yaran makaranta suka tsara

    Dukkan hotuna na da hakkin mallaka.

  3. Sojojin Mozambique sun sake karɓe iko da wani tafki da ke hannun mayaƙa

    Shugaban ƙasar Mozambique Filipe Nyusi, ya bayyana cewa sojojin ƙasar sun sake kwato ikon wani tafki daga hannun masu iƙirarin jihadi a yankin arewacin Cabo Delgado.

    Ya kuma yaba wa matasan sojojin da ke yaki da masu tada ƙayar-baya.

    "A cikin makon da ya gabata, sun samu nasarori da kuma asarar rayuka, inda suka kwato tafkin Inguri, wanda masu iƙirarin jihadi suka yi amfani da su wajen kamun kifi. Matasa na can, duk da cewa wasu sun shiga faɗan," in ji Mista Nyusi, a wani taro a garin Matola.

    Fiye da mutane 4,000 aka kashe tare da tilasta wa 800,000 barin gidajensu tun bayan da masu iƙirarin jihadi suka kaddamar da tawaye a Cabo Delgado a cikin 2017.

  4. MDD ta yi kira a kawo ƙarshen rikici a Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres, ya yi kira ga ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan da su gaggauta dakatar da faɗan, kafin rikicin ya rikiɗe zuwa yaki.

    Da yake magana a Kenya, Mista Guterres ya ce al'ummar Sudan na fuskantar bala'in jin kai, inda aka lalata asibitoci, an wawushe kayan abinci, yayin da miliyoyin mutane ke fuskantar ƙarancin abinci.

    Tun da farko, babban jami'in kula da ayyukan jin kai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffiths, wanda ke Sudan, ya ce yana kokarin samun kowane ɓangare don ba da damar kai kayayyakin jin kai zuwa yankunan da lamarin ya fi kamari.

    Ɓangarori a Sudan sun amince da sabon tsagaita wuta na kwanaki bakwai da za ta fara daga ranar Alhamis, amma tsagaita buɗe wuta da aka yi a baya ta wargaje.

    Mista Griffiths ya ce an yi awon gaba da manyan motoci shida na hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kan hanyarsu ta zuwa yankin Darfur mai fama da rikici, duk kuwa da tabbacin da aka yi musu na cewa za su tsira.

  5. An gano gawar mutumin da kada ya haɗiye a Australia

    crocodile

    Asalin hoton, Getty Images

    An gano gawar wani masunci ɗan ƙasar Australia a cikin wani kada bayan ya ɓata lokacin da ya je su tare da abokansa.

    An yi wa Kevin Darmody, mai shekara 65 ganin ƙarshe ne a Kennedy's Bend - wani fitaccen ruwa mai kadoji a wani yanki mai nisa da ke arewacin Queensland - a ranar Asabar.

    Bayan an yi nema tsawon kwana biyu ne a yankin, sai 'yan sanda suka yanke shawarar yi wa wasu manyan kadoji guda biyu allurar mutuwa, inda kuma aka gano sassan jikin mutum a cikin ɗaya.

    'Yan sanda sun ce "ƙarshe ne mai tayar da hankali" ga Mista Kevin Darmody.

    Za a gudanar da wani gwajin tantance sassan jikin da aka gano a cikin kadan don tabbatar da haƙiƙanin mutumin da kadan ya ci.

    Mista Darmody, gogaggen masunci ne kuma fitaccen mutum a garin Cape York.

    An harbe kadojin biyu ne waɗanda tsayinsu ya kai mita 4.1 (13.4 ft) da kuma mai tsawon mita 2.8, a ranar Litinin daga wani wuri mai nisan kilomita 1.5 daga inda aka yi wa masuncin ganin ƙarshe.

    An gano sassan jikin mutum a cikin kada ɗaya ne kawai, sai dai jami'an kula da dabbobin sun yi imani cewa dukkan kadojin suna da hannu a lamarin.

  6. Real Madrid za ta dauki Bellingham kan yuro miliyan 100

  7. Mutuwar auren 'yar gidan Mugabe ta kai ga neman raba $80m na ma'auratan

    Mugabe family

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bona Mugabe ce ake iya gani tare da mijinta a lokacin jana'izar mahaifinta a shekara ta 2019

    Wata taƙaddamar rabuwar aure tsakanin 'yar gidan tsohon shugaban Zimbabwe Robert Mugabe da mai gidanta ta ba da damar ƙyalla ido a kan wasu maƙudan kuɗi da iyalan suka tara - ciki har da gidaje da suka kai darajar kusan $80m.

    Bona Mugabe, 'yar shekara 33, ta shigar da ƙarar a raba aurensu ne da wani tsohon direban jirgin sama Simba Mutsahuni Chikore a watan Maris, inda ta nemi a raba kadarorinsu a wata ƙara da ta shigar daban.

    BBC ta ga takardun kotun da Mista Chikore ya shigar a ranar 28 ga wtaan Afrilu don maida martani ga na Bona Mugabe.

    Mijin dai yana neman damar haɗin gwiwa don karɓar riƙon 'ya'yansu da kuma rabon dukiyar wadda ta ƙunshi gonaki guda 21, wasu daga ciki iyalan Mugabe sun mallake su ne a lokaci mai cike da taƙaddama na ƙwace gonaki mallakar fararen fata kimanin shekara 20 da ta wuce, kuma duk da manufar mutum ɗaya gona ɗaya.

    Mista Chikore ya kuma zayyana wasu kadarori guda 25 ciki har da wani tafkeken gida a Dubai - waɗanda jimillar darajarsu ta kai kimanin $80m, da motocin alfarma da kayan noma da dubban ɗaruruwan daloli kuɗi-hannu.

    Ya ce dukiyar an mallake ta ne a lokacin aurensu ta hanyar gado da kuma gudunmawa daga marigayi shugaban ƙasar saboda ayyuka da suka yi masa.

    Simba Chikore ya ƙara da cewa dukiyar da ya lissafa kamar ɗigo ce a cikin ruwa, idan an kwatanta da kuɗin da Bona Mugabe take da su.

    Al'ummar Zimbabwe sun maida martana cikin firgici da tashin hankali a kan dukiyar da ɗaya kawai a cikin 'ya'yan Mugabe ya mallaka.

  8. Ghana ta kwashe ƴan ƙasarta 80 da suka maƙale a Sudan, Fahd Adam: BBC Hausa, Ghana

    Ma`aikatar harkokin waje da ci gaban karkara ta ƙasar Ghana, ta sanar da cewa an samu nasarar tserar da ƴan ƙasar 80 da suka makale a Khartoum babban birnin Sudan inda ake gwabza fada tsakanin bangarorin soja biyu da basa ga maciji da juna.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa 74 daga cikin mutanen da aka kwashe sun iso filin saukar jirage na Kotoka tun jiya, yayin da shida daga cikin su aka bi da su ta Wadi Halfa da ke bakin iyakar Masar.

    Ku danna kasa don sauraron rahoton wakilinmu daga Ghana, Fahd Adam.

    Bayanan sautiKu danna lasifikar da ke sama don sauraron rahoton
  9. Doguwa ya ƙaddamar da neman shugabancin Majalisar Wakilai

    ADO DOGUWA

    Asalin hoton, ADO DOGUWA/FACEBBOK

    Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai ya ce duk mutumin da zai iya riƙe mata huɗu da 'ya'ya 28 kamar shi, zai iya neman shugabancin majalisar wakilai zango na goma.

    Alhassan Ado Doguwa ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba lokacin da a ƙa'idance yake sanar da aniyarsa ta neman kujerar mutum na huɗu mafi girman muƙami a Najeriya.

    Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa daga shugaban masu rinjayen wadda a ciki yake mayar da martani gamasu cewa ba shi da ƙwarewa da kuma taushin halin da zai iya maye gurbin shugaban majalisa na yanzu saboda irin halayyarsa.

    Ya ce, “Ko lokacin da na zama Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, ban taɓa nuna zafin rai ba. Ga masu cewa ni mutum ne mai zafin zuciya, sun yi kuskure don ba su san wane ne Ado Doguwa ba, mutumin da yake da mata huɗu da 'ya'ya 28. Ban taɓa sakin mace ba. Haka kuwa manuniya ce cewa ina da abin da ake neman ga mutumin da zai yi fice a matsayin shugaban majalisar wakilai na gaba".

    A cewarsa “ga mutum kamar ni wanda ya kasance a majalisa tun daga 4 ga watan Yulin 1992, zuwa yau kuma cikin nasara ya smau damar wakilcin jama'ata.

    Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun Wada daga Kano a yanzu haka yana fuskantar shari'a bisa zargin haɗa baki don aikata laifi da aikata kisan kai da mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya da tayar da hankulan jama'a.

  10. Leeds United ta nada Allardyce sabon kociyanta

  11. Labarai da dumi-dumi, Messi zai bar PSG a karshen kakar wasanni ta bana

    Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Lionel Messi zai bar Paris St-Germain a bazara a lokacin da kwantiraginsa na yanzu zai kare.

    Ɗan wasan wanda ya lashe Gasar cin Kofin Duniya da Argentina, ya so ya tsawaita zamansa na shekara guda amma shi da PSG ba sa son saka hannu kan yarjejeniyar.

    Messi bai gamsu da cewa kungiyar za a iya fafatawa da ita ba a Gasar Zakarun Turai, inda PSG ke son mayar da hankali wajen bunkasa hazikan matasa.

    Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a birnin Paris a shekarar 2021 tare da zaɓin sabunta kwantiragin na shekara ɗaya.

    An fahimci cewa mahaifin Messi, Jorge ya sanar da PSG hakan makwanni da suka gabata.

  12. Majalisar dattawan Najeriya ta nemi Birtaniya ta yi sassauci ga Ekweremadu

    Ike Ekweremadu

    Asalin hoton, IKE EKWEREMADU/FACEBOOK

    Majalisar dattawan Najeriya ta bi sahun takwararta majalisar wakila da kuma majalisar dokokin ECOWAS wajen yin kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta London ta yi wa Sanata Ike Ekweremadu da mai ɗakinsa, Beatrice sassauci.

    Matakin majalisar dattawan ya zo ne bayan da Sanata Chukwuka Utazi ya gabatar da wani ƙuduri a zaman da aka yi ranar Laraba.

    A ranar Talata ne majalisar wakilai da majalisar dokokin ECOWAS suka nemi gwamnatin Birtaniya ta yi wa Sanatan da matarsa rangwame.

    A ƙudurin da aka gabatar, Sanata Utazi ya bayyana cewa Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ne tsawon shekara 12 kuma tsohon kakakin majalisar dokokin ECOWAS kuma ya ba da gudunmawa wajen ci gaban dimokraɗiyyar Najeriya da Afirka ta Yamma.

    Ya ƙara da cewa wannan ne karon farko da aka samu Ekweremadu da matarsa da laifi, kuma ba su da wani tarihi na aikata laifuka, a cewarsa tun da batun yana Birtaniya, ya kamata a yi rangwame wajen yanke hukunci ganin yadda shari'ar tuni ta zama izina ga mutane.

    Utazi ya kuma ce ya kamata hukumomin shari'a na Birtaniya su duba irin daɗaɗɗiyar kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da gwamnatin Birtaniya, kuma wannan ne karon farko da majalisar dattawa take miƙa ƙoƙon bararta ga gwamnatin Birtaniyar na neman a yi wa Ekweremadu sassauci.

    Shuagaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, ya ce ya aike da takarda ga hukumomin shari'a a Birtaniya makonni biyu da suka gabata inda ya nemi a yi sassauci a madadin majalisar dattijan.

  13. Mutum 130 sun mutu sanadiyyar ambaliya a Rwanda

    Ambaliya

    Asalin hoton, Getty Images

    Alkaluman waɗanda suka mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a Rwanda ya tashi zuwa 127,a cewar hukumomi.

    Wani gwamna a lardin yammacin ƙasar, François Habitegeko, ya ce abin da suka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne kai wa gidajen da suka zaftare domin tabbatar da cewa an ceto mutane da suka maƙale.

    An kuma ruwaito mutuwar mutum shida saboda ambaliya da zaftarewar laƙa a ƙasar makwaɓta Uganda, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.

  14. Yadda rikicin Sudan ke ta'azzara matsalar ƴan gudun hijira a Darfur

  15. Tinubu ya gode wa Wike bisa gudummawar da ya ba shi

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga

    Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike kan irin gudunmowar da ya bayar wajen tabbatar da nasararsa a zaɓen shugabna ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

    Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnan ya gudanar a jihar.

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na ziyarar ƙaddamar da ayyuka ta kwana biyu da gwamnan jihar ya gayyace shi.

    Tinubu ya ce ''Mai girma gwamna Nyesom Wike kai mutum ne abin dogaro''.

    Ya ƙara da cewa ya fuskanci gangamin yaƙin neman zaɓe mai ''matuƙar mai tsanani'' yana mai cewa ''ba don tallafin tsare-tsare da na samu daga wasu mutane irin su Wike ba, to da samun nasara akan manyan abokan takarata irinsu Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP, zai min wahala''.

    “Don haka Nyesom, ina godiya da goyon bayan da ka ba ni. ba don tallafin wasu tare-tsare da na samu ba, da nasarata ba ta tabbata ba,” in ji tsohon gwamnan na jihar Legas.

  16. An saka sunan Ferdinand cikin gwarzayen Premier League

  17. Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin kashe Putin

    b

    Rasha ta zargi Ukraine da yunƙurin hallaka shugabanta Vladimir Putin bayan da ta harbo wasu jirage biyu marasa matuƙa da suka riƙa shawagi a Moscow cikin daren jiya.

    Bidiyon da ba a tantance ba, da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna wani abu na shawagi a sararin samaniyar fadar gwamnatin ƙasar kafin ya tarwatse.

    Ukraine ta ce babu abin da zai sa ta kai hari da jirgi maras matuƙi.

    Mai magana da yawun shugaban Ukraine ya ce a yanzu abin da ke gaban Ukraine shi ne ƙwato yankunanta da ke hannun dakarun Rasha.

    Wani jami'i ya shaida wa BBC cewa wannan lamari alama ce da ke nuna cewa dole Rasha da shirya wa takalar faɗa daga Ukraine.

    Rasha ta ce ta lalata jiragen biyu marasa matuƙa da suka yi shawagi a fadar Kremlin.

    Mai magana da yawun Mista Putin ya ce shugaban ba ya fadar a lokacin da jiragen suka riƙa shawagin.

  18. An kama wani yaro bayan kashe mutum tara a harin da aka kai makaranta a Sabiya

    Akalla dalibai takwas ne da wani mai gida ɗaya aka kashe bayan harbe-harbe a wata makaranta da ke Beigrade babban birnin Sabiya.

    Ma`aikatar harokin cikin gida ta ƙasar, ta sanar da cewa an jikkata wasu ɗalibai shida da malami daya a harin.

    Yan sanda sun kama wani ɗalibi dan shekara wani dalibi dan shekara 14 a makarantar Vladislav Ribnikar da ke tsakiyar birnin Belgrade bisa zarginsa da hannu a harin harin da aka kai da safiyar Laraba.

    Jami`ai sun ce wanda ake zargin ya yi amfani da bindigar mahaifinsa, ana ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin.

  19. Ronaldo ne na daya a samun kudin shiga tsakanin masu wasanni

  20. An kai hari ofishin jakandancin Saudiyya a Sudan

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiya da ke ɗauke da makamai ta yi wa ofishin jakadancin Saudiyya da ke Khartoum ƙawanya.

    A cikin wata sanarwa da ma`aikatar harkokin wajen Saudiyya ta fitar, ta ce ƙungiyar masu ɗauke da makamai sun lalata kayan aiki da kyamarori.

    Sanarwar ta kuma ce maharan sun ƙwace wasu daga cikin kadarorin ma`aikatar, tare da lalata na`urori da intanet din ofishin.

    Saudiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan aika-aikar tare da yin kira da a tabbatar da mutunta tsarin diplomasiyya ta hanyar hukunta waɗanda suka aikita laifin

    Masarautar ta sake jaddata kiran dakatar da fada tsakanin sojojin ƙasar, tare da kawo ƙarshen tashe tashen hankula, da kuma ba da kariya ga jami'an diflomasiyya da fararen hula.