'Jirgin yaƙi ya hallaka 'yan fashin dajin da suka kai hari Birnin Gwari'

Wannan shafi ne da zai rinƙa kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kuɗi kan 'ɓatan' kuɗin man fetur

    TWITTER/@FEMIGBAJA

    Asalin hoton, TWITTER/@FEMIGBAJA

    Kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike kan zargin ɓatan kuɗin man fetur ya gayyaci ministar kudin ƙasar Zainab Shamsuna Ahmed, da Sakataren gwamnatin tarraya Boss Mustapha, da kuma ministan shari'a Abubakar Malami.

    Yana neman su bayyana gabansa a wani ɓangare na binciken da yake yi.

    Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah ne ya bayar da umarnin gayyatar jami'an gwamnatin, bayan kwamitin ya koma sauraron bahasi kan zargin ɓacewar kuɗin gangar man fetur miliyan 48 da aka sayar wa China da wasu masu kwarmata bayanai suka bayyana.

    Kwamitin na bincike ne kan zargin ɓatan sama da dala biliyan 2.4 na man fetur da aka fitar ba bisa ƙa'ida ba, domin sayar da shi, tun daga shekarar 2014 zuwa yau.

    Mista Gbillah ya ce kwamitin ya ba da umarnin ne domin sanin irin rawar da - ma'aikatar kuɗi da sauran hukumomin gwamnati - suka taka musamman kan abin da ya shafi tsarin masu kwarmata bayanai.

    ''Mafi yawan matsalolin - abin da ya kamata mu bincika game da tsarin masu kwarmata bayanai - na tasowa ne tsakanin ma'aikatar kuɗi da ofishin ministan shari'a''.

    Tun da farko kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila wanda ya samu wakilcin Isiaka Ibrahim Ayokunle, ya nuna damuwa game da raguwar kuɗin shiga da ƙasar ke samu daga sayar da ɗanyen man fetur.

    Ya ce abu ne mai tayar da hankali zargin da masu kwarmata bayanan suka yi cewa fiye da dala biliyan 2.4 na kuɗin gangar mai miliyan 48 ne suka ɓace a ƙasar.

  2. Atiku bai cika sharuɗɗan cin zaɓe ba - INEC

    Atiku

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta ce ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gaza cika sharuɗɗan da tsarin mulkin ƙasar ya gindaya kafin a ayyana shi matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.

    INEC ta bayyana haka ne a matsayin martani kan ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar ya shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

    Ta dai buƙaci kotun ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar ya shigar gabanta yana ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC nasara.

    Hukumar ta ce Atiku ya gaza samun kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a aƙalla kashi biyu cikin uku na jihohin ƙasar 36 da kuma birnin tarayya Abuja, wanda hakan na cikin sharuɗɗan cin zaɓe a ƙasar.

    Game da ƙorafin saɓa dokar zaɓe, INEC ta ce an gudanar da zaɓen ne bisa dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ba tare da almundahana ba, kamar yadda masu ƙorafin suke zargi.

    Hukumar zaɓen ta sake jaddada cewa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC shi ne halastaccen zaɓaɓɓen shugaban ƙasar.

    Game da ƙorafin rashin samun rinjayen ƙuri'u a Abuja da ake yi wa Tinubu, INEC ta ce kundin mulkin Najeriya bai fitar da wani matsayi na musamman a kan ƙuri'un babban birnin ƙasar ba.

    Domin haka, a cewarta ƙuri'un Abuja daidai suke da ƙuri'un kowacce jiha ta fuskar matsayi.

    Atiku Abubakar tare da jam'iyyarsa ta PDP sun garzaya kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne domin ƙalubalantar sakamakon da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC nasara.

  3. An kashe sojojin Indiya huɗu bayan buɗe wa sansaninsu wuta

    qqq

    Asalin hoton, AFP

    Akalla sojoji huɗu ne aka tabbatar da mutuwar su a harbin da aka yi a sansanin soji da ke yankin Punjab.

    A wata sanarwa da rundunar sojin Indiya ta fitar, ta ce da safiyar yau Laraba ne aka fara harbe-harbe a cikin sansanin sojoji na Bathinda, inda sojojin da iyalansu ke zama.

    Tuni aka yi gaggawar killace wurin da aka yi harbin, da ake zargin wani ɗan bindiga daɗi da buɗe wa sojojin wuta.

    Rundunar 'yan sandan Punjab ta shaida wa kafar yaɗa labaran Indiya cewa harin ba shi da alaƙa da ta'addanci.

  4. MDD na son a gudanar da bincike kan barazanar kashe jami'inta

    Antonio Guterrez

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Sudan ta yi bincike kan barazanar kisa, da ake yi wa babban jami'inta a kasar.

    MDD ta bayyana damuwa kan wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda wani mutum ya nemi fatawa game da halascin kashe jami'in diflomasiyyar na MDD, Volter Perthes.

    Mutumin dai ya yi ta zagi da aibata shugaban shirin MDD a Sudan a wani taro da jam'iyyun addini suka jagoranta.

    Ya zargi Mr Perthes da cire ɓangaren masu kaifin kishin Islama daga tattaunawar da MDD ta jagoranta na mayar da mulki hannun farar hula.

    Sai dai masu shirya taron sun nesanta kansu da kalaman mutumin

  5. Sallama

    Masu bin mu a wannan shafi Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannan safiya ta Laraba.

    Ku kasance da mu domin sanin halin da duniya ke ciki, za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.