Masu iƙirarin Jihadi a Mali sun ƙwace ɗaukacin Lardin Menaka

Asalin hoton, Reuters
Masu iƙirarin jihadi a arewacin Mali da ke da alaƙa da ƙungiyar IS sun ƙwace iko da wani ƙauye a Menaka - wani lardi wanda akasari yanzu yake ƙarƙashin gudanarwarsu.
Tun a farkon shekarar da ta wuce ƙungiyar IS ta babban yankin Sahara ta ƙaddamar da wani gagarumin hari a yankin da kuma a cikin Gao - wani lardin da shi yake arewacin Mali.
Tidermene, ba wani babban ƙauye ne - matsuguni ne ga 'yan dubban mutane.
Sai dai a yanzu, ya faɗa hannun mayaƙa masu iƙirarin jihadin da ke da alaƙa da IS, gwamnatin tarayya a ƙasar ta rasa iko da kusan ɗaukacin lardin Ménaka.
Babban birnin lardin ne kawai har yanzu ake samun dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya da sojojin Mali da kuma sojojin haya daga Rasha.
Wani jami'in ƙauyen da ya tsere daga can ya tabbatar da ƙwace matsugunnin har ma ya ce 'yan ta-da-ƙayar-baya suna yawo ko'ina da makamai.








