Kuɗin masaukai ya yi tashin gwauron zabo a Makkah

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Mukhtar Adamu Bawa

  1. Sojojin Amurka da Koriya ta Kudu da Japan na atisayen kwana biyu

    Atisayen soji

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin ruwan ƙasashen Koriya ta Kudu da Amurka da Japan na gudanar da atisayen kwana biyu, don inganta aikinsu.

    A wani mataki na tauna tsakuwa kan barazanar hare-haren makamai masu linzami na Koriya ta Arewa.

    Manufar atisayen shi ne faɗaɗa ikonsu da horon da zai ba su damar kare teku a kan hare-haren makaman nukiliya na ƙarƙashin teku da Koriyar Arewa ta fara yi a baya-bayan nan.

    Za su samu horo ne a kan yadda za su iya gano makamin nukiliya da zarar an harba shi cikin teku.

    IKuma za su sanya wasu motocin teku na musamman a matsayin kan-da-garki.

  2. Trump zai halarci kotu kan tuhumar da ake yi masa

    Trump

    Asalin hoton, AFP

    A yau ne ake sa ran tsohon shugaban Amurka Donald Trump zai je New York daga Florida, gabannin shari'ar da ke jiransa a Manhattan gobe Talata.

    Inda za a gabatar masa da duk tuhume-tuhumen da ake yi masa a bayyane.

    Rahotonni sun ce Mista Trump ya yi duk harkokin da ya saba a ƙarshen mako, cikin har da buga ƙwallon sanda (Golf).

    Duk da haka, ya tuntuɓi masu ba shi shawara a kan hanyar da zai ɓullowa, batun da ya kira maƙarƙashiyar siyasa.

    Ana tuhumar tsohon shugaban Amurkan ne da laifin biyan wata mai shirin fina-finan batsa dubban daloli gabannin zaɓen 2016,a matsayin toshiyar baki.

    Ana zargin ya ba ta ne kada ta yi magana a kan zargin da ake yi masa na mu'amala da ita, kafin zaɓen Amurka na 2016.

    To sai dai, a lokuta da dama Mista Trump ya sha musanta zargin.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi, Abdullahi Bello Diginza ke maraba da ku a safiyar ranar Litinin.

    Barkanmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya leƙa wa shafukanmu na sada zumunta don tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.