'Yan bindiga sun sace ɗalibai mata biyu na jami'ar Gusau

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ecuador ta ayyana dokar ta-ɓaci kan miyagun ƙwayoyi

    masu bincike

    Asalin hoton, Getty Images

    Ecuador ta ayyana dokar ta-ɓaci a garin Gauyaquil da kewayensa na gaɓar teku, wanda masu safarar ƙwaya suka yi wa ƙawanya.

    Shugaban ƙasar Guillermo Lasso, ya ce dokar ta-ɓacin ta hada da taƙaita zirga-zirga cikin dare, tun daga ƙarfe shida na yamma zuwa ƙarfe biyar na asubahi.

    A jawabin da ya yi wa 'yan ƙasar, shugaba Lasso ya ce jami'an tsaro za su kafa shingayen binciken ababen hawa, za kuma su riƙa zuwa bincike har cikin gidajen jama'a musamman waɗanda ake zargi da ɓoye kayan laifi.

    Ana samun ƙaruwar safara da tu'ammali da miyagun ƙwayoyi daga gungun masu aikata miyagun laifuka a Ecuador.

  2. Isra’ila ta raunata sojojin Siriya biyar

    Kamfanin dillancin labaran Siriya ya ruwaito cewa sojin ƙasar biyar ne suka jikkata lokacin da hare-hare ta sama da Ira’ila ta ƙaddamar suka faɗa yammacin tsohon birnin Homs.

    Kamfanin SANA ya ce harin ya lalata wurare da dama ciki har da cibiyoyin ayyukan sojin ƙasar.

    Rahotonni sun ce wannan ne karo na uku da Isra’ila take kai hari cikin Siriya a 'yan kwanakin nan.

    Kawo yanzu, Isra’ila ba ta ce uffan game da batun ba, kodayake ta ce tana da haƙƙin ɗaukar matakin soji, idan ta ga wani abu da ba ta gamsu da shi ba a tsakanin ƙasashen Iran da Siriya.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi barkan mu da hutun ƙarshen mako

    Abdullahi Bello Diginza ne ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Idan kun kasance da ni, zan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtan ƙasashe har ma da sauran sassan duniya.