Girgizar ƙasa ta hallaka mutum 12 a Pakistan da Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
Akalla mutum 12 ne suka mutu fiye da 200 suka jikkata bayan da wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta afka wa wasu yankunan ƙasashen Pakistan da Afghanistan.
Girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 6.5 ta lalata gine-gine da nutsewar gidaje, tare da tilasta wa mutane barin gidajensu.
Lamarin ya faru ne ranar Talata da yamma a tsakiyar lardin Laghman da ke arewa maso gabashin Afghanistan kusa da kan iyakar Pakistan.
An jiyo ƙarar girgizar daga garuruwa da dama a ƙasar.
"Girgiza ce mai tayar da hankali. Ban taɓa jin ƙarar girgizar ƙasa, kamar wannan ba a rayuwata,'' kamar yadda wata mazauniyar birnin Kabul ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, bayan ficewarta daga gidanta na bene mai hawa biyar.
An tabbatar da mutuwar mutum tara a yankin Khyber Pakhtunkhwa da ke Pakistan Pakistan.
Sauran mutum ukun ciki har da ƙaramin yaro sun mutu ne a Afghanistan, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar ƙasar ya bayyana.
Mutane da dama ne ke kan titunan biranen ƙasar domin murnar bikin sabuwar shekarar al'adar ƙasar a lokacin da girgizar ƙasar ta auku.
Ma'aikatan agaji a lardin Khyber Pakhtunkhwa sun ce ɓarnar da girgizar ƙasar ta haifar ba ta kai yadda aka yi tsammani ba.


