Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana zirga-zirga a jihar

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Za mu gudanar da gwamnatin da za ta fifita maslahar al’umma - Abba Gida-gida

    Abba

    Asalin hoton, FAMILY

    Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, ya ce zai gudanar da gwamnatin da za ta fifita maslahar al’umma da kuma kyautata ilimi.

    A jiya ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar da ranar asabar din da wuce.

    A tattaunawarsa da BBC Abba Kabira ya ce al'umar jihar sun nuna masu ƙauna a lokacin da yake ya ƙin neman zaɓe da kuma a ranar zaɓe, kan haka ne ma ya ce bai yi mmaki ba da hukumar INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Ya ƙara da cewa ba zai yi sako-sako wajen yaƙi da cin hanci da kyautata rayuwar al’umma ba.

    Sabon zaɓaɓɓen gwamnan na Kano ya ce zai bayar da fifiko wajen kyautata ilimi da lafiya da kasuwanci da tsaro da harkokin noma.

    Abba Gida-gida ya ce cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa zai yi kokarin kyautata ɓangaren ilimin jihar.

    Abba Gida-gida - wanda tsohon kwamishinan ayyukan ne zamanin mulkin tsohon gwaman jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso - ya alƙawarta cewa zai ƙarasa duk ayyukan da gwamnatin jihar ta yanzu ta faro matuƙar za su amfanar da al'ummar jihar.

    Sabon gwamnan ya lashe zaɓen da aka gudanar da ƙuri'u miliyan 1,019,602, bayan doke babban abokin hamayyarsa mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya samu ƙuri'u 890,705.

  2. APC ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bauchi

    baba

    Asalin hoton, Facebook/Air Marshal Sadiq Baba Abubakar

    Jam’iyyar APC a jihar Bauchi, ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar wanda ya bai wa Bala Mohammed na jam'iyyar PDP wanda hukumar zaɓen ƙasar ta sanar cewa ya lashe a karo na biyu.

    A taron manema labarai da ta kira ranar Litinin, ɗan takarar jam’iyyar Air Marshal Sadiq Baba Abubakar mai ritaya ya ce an tafka kura-kurai a zaɓen da dama waɗanda suka tilasta wakilan jam’iyyar ƙin sanya hannu kan takardar shaidar sakamakon zaɓen.

    Jam’iyyar APC a jihar ta yi zargin cewa an tabka maguɗi bayan kura-kurai da ta yi zargi an samu, don haka ta buƙaci hukumar zaɓen ƙasar ta soke sakamakon zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomin Alƙaleri da Kirfi da Toro da Warji da Zaki.

    Sannan ta bukaci bayan soke zaɓen, a kuma bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.

    Air Marshall Abubukar Baba Sadique mai riyata ya yi zargin cewa an razana mutane da makamai, sannan ya yi zargin cewa jam'iyyar PDP ta sayi ƙuri'u a rumfunan zaɓen.

    Ya ce wakilan jam'iyyarsu sun ƙi saka hannu a kan sakamakon da suka yi zargin an tafka maguɗi, amma duk da haka an sanar da sakamakon zaɓen.

    Sannan ya ce za su yi nazari da kuma tattaunawa da al'ummarsu kan sakamakon zaɓen kafin ɗaukar mataki na gaba.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata, Abdullahi Bello Diginza ne zai kasance tare da ku a wannan shafi na kai-tseye.

    Inda za mu ci gaba da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.