EFCC na neman A.A Zaura ruwa-a-jallo

Wannan shafin na kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. NDLEA ta kama wata mai tsohon ciki 'ɗauke da ganyen wiwi'

    ...

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukumar yaƙi da safarar ƙwaya ta Najeriya NDLEA ta ce jami’anta a jihar Rivers, sun kama wata mai juna-biyu ɗauke da ganyen wiwi wanda nauyinsa ya kai kilogiram 34.3.

    An kama matar ƴar shekara 29 ne a yankin Okrika na jihar.

    Sai dai shugaban hukumar, birgediya janar Buba Marwa mai murabus ya umurci a bayar da belin matar har sai ta haihu, kasancewar cikin nata ya kai wata tara.

    Haka nan kuma sanarwar da hukumar ta NDLEA ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaruta Femi Babafemi ta ce an kama wata tsohuwa mai shekara 60 a jihar Oyo da ganyen wiwi mai nauyin kilogiram 5.5.

    Toshuwar ta yi bayanin cewa ganyen wanda aka ɓoye a cikin lasifika, ya fito ne daga wurin wata ƴarta da ke zaune a Afirka da kudun.

  2. An sace kwamishina a jihar Benuwe

    Samuel Ortom

    Asalin hoton, TWITTER/@GovSamuelOrtom

    Wasu mahara sun sace kwamishinan gidaje da raya karkara na jihar Benuwe, Ekpe Ogbu.

    Mai taimaka wa gwamnan jihar kan tsaro kanar Paul Hemba ya tabbatar wa kafar talabijin ta Channels cewar an sace Mr Ogbu da yammacin ranar Lahadi a mahaɗar Adankari kan hanyar Otukpo-Ado.

    Ya tabbatar da cewa an gano motar da kwamishinan ke ciki a lokacin sace shi, kuma tuni jami’an tsaro suka fara bincike.

    Sai dai ya ce ba a samu wani labari daga waɗanda suka sace shi ba.

  3. Jam'iyyar ANC na tattaunawa kan makomar shugaban Afirka ta kudu

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban kwamitin jiga-jigan jam'iyyar ANC mi mulki a Afirka ta Kudu zai gana da mambobinsa a yau Litinin, domin tattauna makomar shugaba Cyril Ramaphosa.

    Wani rahoto da aka fitar ya zargi Mr Ramaphosa, da aikata ba daidai ba, da yiwuwar take dokokin ofishinsa.

    Ana zargin ya boye tsabar miliyoyin daloli a gidan gonarsa, ba tare da ya sanar da bacewarsu ba a lokacin da aka sace kudaden.

    A jawabin da ya yi a jiya Lahadi, shugaban na Afirka ta Kudu, ya ce makomarsa ta ta'allaka ne a hannun 'yan jam'iyyarsa.

    Wannan danbarwa dai ta janyo an fara tababar ko jam'iyyar ANC za ta sake tsaida shi a matsayin shugabanta a babban taron da za su yi a karshen watan nan.

  4. Ana bincike kan yadda masu jinya ke kai wa malaman asibiti hari a Masar

    Mai shigar da ƙara a kasar Masar ya kaddamar da bincike kan yadda ake ƴan uwan marasa lafiya ke yawan kai hare-hare a kan ma'aikatan asibitin Nile Delta.

    Bayanai sun ce an samu irin wadannan hare-hare a asibitin Quwaisna, da ke arewacin birnin Alkhahira, lokacin da 'yan uwan maras lafiyar suka fusata kan cewa likitan da ke aiki a wannan lokaci, ba zai duba dan uwansu ba, saboda ya na tare da wata mata da za ta haihu a dakin haihuwa.

    Likitan dai ya bukaci a gudanar da wasu gwaje-gwaje kan maras lafiyar da ya ce ba ya bukatar kulawar gaggawa.

    Hatsaniyar da ta kaure ta janyo wata jami'ar lafiya mai juna biyu yin bari, yayin da 'yan uwan majinyacin suka yi amfani da tsumagiya wajen lakada wa likitan duka.

  5. Barka da warhaka

    Masu bibiyar mu a wannan shafi Haruna Ibrahim Kakangi ke maku barka da safiyar Litinin.

    Za mu rinƙa kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya ta wannan shafi a tsawon wannan yini da yardar Allah.

    Da fatan za ku ziyarci shafukanmu na sada zumunta domin bayyana ra'ayoyinku kan waɗannan labarai da ma wasu ƙari a facebook, da tuwita, da instagram @bbcnewshausa.

    Za ku iya kallon shirye-shiryenmu na bidiyo a shafinmu na BBC Hausa youtube.