Dubban mutane sun tarbi gawar Sarauniya a Fadar Buckingham

Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Sani Aliyu and Aisha Shariff Bappa

  1. Hotunan yadda aka wayi gari a birnin Edinburgh

    Kalli hotunan yadda aka wayi gari a Edinburgh gabanin dauko gawar Sarauniya zuwa filin jirgin saman birnin kan hanyarta ta zuwa Landan.

    An armed sniper stands perched on the roof of a building in Edinburgh

    Asalin hoton, Getty Images

    People have continued to queue through the morning

    Asalin hoton, Getty Images

    Members of the public will be able to view the coffin until 15:00 BST on Tuesday

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Yadda wasu mata suka rufa da barguna yayin da suke jiran isowar Sarki Charles III

    Tuni jama'a suka fara taruwa a wajen Fadar Hillsborough Castle da ke arewacin Ireland domin tarbar Sarki Charles III da matarsa Camilla.

    Kuna iya ganin yadda wasu mata suka tanadi barguna domin kare kawunansu daga sanyi yayin da suke jiran isowar manyan bakin nasu, kuma wasunsu ma sun tafi da abinci domin za su shafe sa'o'i suna dakon isowar su.

    Many people have wrapped up warm and some have even brought picnics.
  3. An kama matsafa shida kan yunkurin kashe basarake a Ogun

    Nigerian policemen

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an 'yan sanda a Jihar Ogun da ke Najeriya sun damke wasu mutum shida yayin da suke kokarin kashe wani basarake.

    Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar na cewa mutanen da aka kama sun hada da Michael Ayodele da Monday Samuel da Ademola Matthew da Hammed Jelili da Ogundele Ojeh da kuma Sunkanmi Fadina.

    Kakain rundunar 'yan sandan Abimbola Oyeyemi, ya ce rundunar ta sami rahoto daga sarki G.O. Olukunle na garin Oja Odan da ke karamar hukumar Yewa ta Kudu ta Jihar Ogun da misalin karfe 4:25 na yamma cewa wasu matsafa na shirin kashe shi a cikin fadarsa.

    Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa jami'ansu sun isa wurin kuma bayan musayar wutra sun kama shida a cikin matsafan:

    "Bayan mun bincike su, matsafan sun tabbatar mana cewa dan basaraken ne ya yi hayan su domin su kashe mahaifin nasa saboda wata matsala da ke tsakanin sarkin da mahaifiyarsa."

  4. Dubban jama'a sun cika filin wasa domin halartar rantsar da sabon shugaban Kenya William Ruto

    William Ruto swearing-in

    Asalin hoton, Anne Ngugi

    Dubban 'yan kasar Kenya sun taru a babban filin wasa na birnin Nairobi domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Kenya Mr. William Ruto.

    Tun karfe 3 na dare jama'a suka fara isa filin wasan.

    Jami'an tsaro sun rufe manyan hanyoyin birnin kuma an baza 'yan sanda a harabar filin wasan da kuma a cikin birnin.

    Ana sa ran akalla shugabannin kasa 20 ne za su halarci wannan bikin.

    William Ruto swearing-in

    Asalin hoton, Anne Ngugi

    Yayin bikin shugaba mai barin gado Uhuru Kenyatta za mika kambun iko - wato wani takobi da kuma kundin tsarin mulkin kasar - ga sabon shugaban kasar William Ruto.

    Tun da fari Mista Kenyatta ya ki taya zababben shugaban murnar lashe zaben shugaban kasar, amma a ranar Litinin ya sanar cewa a shirye yake ya tabbatar da an wanzar da zaman lumana a kasar kuma ya bukaci sabon shugaban da ya zama shugaban dukkan 'yan kasar.

  5. Kalli hotunan yadda ake shirin faretin girmama gawar Sarauniya da aka yi da sanyin safiya

    Soldiers march outside Buckingham Palace as part of rehearsals for the procession of Queen Elizabeth II's coffin

    Asalin hoton, PA Media

    Soldiers will walk alongside the coffin as it makes its way from Buckingham Palace to Westminster Hall

    Asalin hoton, PA Media

    The coffin will make its way past Big Ben and the Houses of Parliament

    Asalin hoton, PA Media

    The Queen will lie in state in Westminster Hall until her funeral on Monday morning

    Asalin hoton, PA Media

  6. Zaben 2023: INEC ta goge rajistar mutum 1,126,359 a Najeriya

    Nigerian voters

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar cewa ta soke rajistar wasu mutum 1,126,359 cikin sabuwar rajistar mutum 2,523,458 da ta yi tsakanin 28 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Janairu, 2022.

    Babban kwamishinan hukumar ta INEC Festus Okoye ne ya sanar da haka cikin wani sakon Tiwita da hukumar ta wallafa a shafinta a ranar Litinin a Abuja.

    Ya ce "INEC ta gano cewa wasu mutanen ba su yi rajista daidai da tsarin doka ya tanadar ba, saboda haka ne muka soke rajistar tasu baki daya."

    INEC ta kuma ce mutum 1,397,099 da suka yi sabuwar rajista ne kawai za a saka sunayensu cikin kundin wadanda za su iya zakda kuri'arsu a babban zabe da ke tafe a shekara mai zuwa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Masu son ganin gawar Sarauniya Elizabeth II sun fara taruwa a Landan

    London awaits the Queen

    An fara kafa layuka a birnin Landan yayin da ake jiran isar gawar Sarauniya zuwa dakin Westminster Hall da ke ginin majalisar Birtaniya, wurin da za a ajiye gawar na kwana hudu kafin a binne ta daga baya.

    Za a fara iya ganin gawar daga karfe 5 na yammacin ranar Laraba kuma za a kammala wannan aikin karramawar ranar Litinin 19 ga watan Satumba da karfe 6:30 - wadda ita ce ranar da za a binne Sarauniyar.

    Layukan da aka fara kafawa sun fara ne daga kan gadar Lambeth, kuma da alama masu son ganin gawar za su dade suna jira.

  8. Sarauniya Elizabeth: Abin da ake sa rai zai faru a yau

    Yau ma rana ce da ke cike da hidimomi.

    Da safiyar nan Sarki Charles da matarsa Camilla za su ziyarci birnin Belfast, wurin da ake sa rai sarkin zai gana da sakataren da ke kula da yankin Arewacin Ireland Chris Heaton-Harris, tare da wasu manyan jami'ai daga jam'iyun siyasa.

    Bayan kuma ya gana da wasu shugabannin addini, Sarkin da matarsa za su halarci wani taron adu'o'i a cocin St Anne kafin su koma Landan.

    Queen's vigil

    Karfe 5 na yamma: Za a dauko akwatin gawar Sarauniya Elizabeth daga cocin St Giles da ke Edinburgh zuwa filin jirgin saman birnin, kuma daga can za a saka shi cikin jirgin sama zuwa filin jirgin sama na sojojin sama wato RAF Northolt da karfe 6 na yamma.

    'Yar Sarauniyar wato Gimbiya Anne ce za ta raka gawar, aikin da ta fara yi tun da aka dauko gawar daga Fadar Balmoral ta kasar Scotland.

    Karfe 7 na dare: Ana sa ran gawar ta isa Landan, sannan za a wuce da ita zuwa Fadar Buckingham, wurin da Sarki Charlews da matarsa Camilla za su tarbe ta.

    Ku biyo mu domin sanin abubuwan da za su faru yayin da ake ci gaba da shirin binne Sarauniya Elizabeth.

  9. Budewa

    Barkanmu da wayewar gari! Suna na Sani Aliyu.

    Kamar yadda aka saba, BBC Hausa ta shirya tsaf domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Birtaniya yayin da ake ci gaba da shirin binne Sarauniya Elizabeth.

    Za mu kuma kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassa na duniya.