Dubban mutane sun tarbi gawar Sarauniya a Fadar Buckingham
Wannan shafi ne da zai kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da ke faruwa dangane da rasuwar Sarauniya Elizabeth ta Ingila da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sasan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Sani Aliyu and Aisha Shariff Bappa
Rufewa
Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa da muka wuni muna kawo muku labarai da rahotanni na wasu abubuwan da suka faru a duniya, musamman ma batun mutuwar Sarauniya ELizabeth II.
Sai kuma gobe Laraba inda za mu ci gaba da kawo muku labaran da suka shafe ku.
Sunana Aisha Shariff Baffa, nake cewa mu kwana lafiya.
Mutum biyar sun jikkata, kana gidaje sun kone bayan wata mota dauke da tukwanen gas ta kama da wuta a Jigawa
Hukumar tsaro ta civil defence a Najeriya, ta ce mutum biyar ne suka jikkata kana gidaje da dama suka kone bayan da wata mota dauke da
tukwanen gas ta kama da wuta.
Lamarin dai ya auku ne a ranar Litinin da daddare a karamar
hukumar Babura cikin jihar Jigawa lokacin da motar da ake zargin ta yi
fasa-kwaurin gas daga jam’huriyyar Nijar ta fadi.
Wani mutum da ya shaida lamarin yace motar makare da
tukwanen gas ta fada cikin kwalabati ne bayan da jami’an tsaro suka biyo ta
saboda ana zargin wadanda suke cikin motar sun yi fasa-kwaurin gas din daga Jam’huriyar Nijar.
Mutumin yace jama’a sun shiga firgici da tashin hankali
sakamakon fashewar gas din.
Hukumar tsaro ta civil defence din ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike
don gano musabbabin faduwar motar da ta haddasa gobara.
Bayanai na cewa an tura
karin jami’an tsaro garin na Babura da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar, don dakile
duk wani yunkurin tayar da zaune tsaye musamman daga wadanda suke ganin
al’amarin ya auku ne saboda sakacin wasu jami’an tsaro.
Dubban mutane sun tarbi gawar Sarauniya a Fadar Buckingham
Asalin hoton, PA Media
Dubban mutane ne suka tarbi gawar Saruniyar Ingila a gaban Fadar Buckingham a yau da daddaren nan.
An yi ta jin ƙarar helkwafta da ke alamta isar gawar.
Mutane sun yi ta ɗaga wayoyinsu sama don ɗaukar hoto, sannan ana ta ruwan sama - a lokacin da gawar ta isa.
Mutanen da suka yi cincirindo a ƙofar fadar sun yi ta kuka da share hawaye a yayin da gawar Sarauniya Elizabeth ta isa fadarta a karo na ƙarshe kafin binne ta.
Sarki Charles III da matarsa Camilla sun bar Fadar ta Buckingham jim kadan bayan da suka shaida isar gawar sarauniyar.
Asalin hoton, re
DSS za ta ci gaba da tsare Tukur Mamu har tsawon kwanaki 60
Asalin hoton, OTHER
Bayanan hoto, Tukur Mamu
Wata kotu da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ta ba wa hukumar tsaron cikin gida ta DSS, damar ci gaba da
tsare mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu har na tsawon sama da
kwanaki 60.
Kotun ta yanke
wannan hukunci ne a ranar Talata, bayan da lauyan hukumar ta DSS ya bukaci hakan.
A cikin wata
takarda da ta gabatar wa kotun, hukumar tsaron ta DSS ta bukaci
kotun ta ba ta damar ci gaba da tsare Tukur Mamu, ne domin samun isasshen
lokacin gudanar da bincike.
Tukur Mamu, dai shi ne
ya jagoranci karbo da dama daga cikin fasinjojin jirgin kasa wadanda ake
zargin kungiyar Ansaru da laifin sacewa, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa
Kaduna daga Abuja babban birnin kasar.
Tun farko dai an
kama mawallafin ne a birnin Alkahira na kasar Masar, inda daga baya aka mayar
da shi gida Najeriya.
DSS ta
sanar da cewa ta kama Mamu ne a kokarin ta na ganin ya amsa tambayoyi kan wasu
lamura masu muhimmanci.
Haka nan hukumar
ta tabbatar da cewa jami’anta sun gudanar da bincike a gidansa da ke Kaduna
in da ta gano wasu kaya da kuma kudade masu dumbin yawa.
Saudiyya ta kama mutumin da ya tafi Makka takanas don yi wa Sarauniya Umara
Asalin hoton, Getty Images
Mahukunta a Saudiyya sun kama wani mutum wanda ya tafi Makka takanas don yin Umara a madadin Sarauniya Elizbeth ta II.
A ranar Litinin ne mutumin, wanda dan asalin kasar Yemen ne ya wallafa bidiyonsa a babban masallacin Makka yana dawafi.
A cikin bidiyon ya rubuta cewa na sadaukar da Umarar da na yi ga Sarauniya Elizebeth ta II, ya ce yana addu'ar Allah Ya yafe mata kura-kuranta.
An dai yada bidiyon a kafafan sada zumuntar Saudiyya inda mutane suka rinka kira a shafukansu na Tiwita da a kama shi.
Saudiyya ta haramta wa mahajjatan da suke je kasar daukar kwalaye mai dauke da rubuce-rubuce ko kuma ambatar sunan wasu da zummar kamfe ko wani abu dabam.
Yayin da aka amince cewa wani zai iya yi wa mamaci Musulmi Umrah, ba a amince a yi wa wanda ba Musulmi ba kamar Sarauniya, wadda shugaba ce a Cocin Majami'ar Ingila.
Ana shirye-shiryen tarbar gawar Sarauniya a Fadar Buckingham
Kai kawo da hada-hada na ta ƙaruwa a Fadar Buckingham tun lokacin da gawar Saruaniya ta isa arewa maso yammacin Landan.
An ƙara jibge jami'an ƴan sanda a titin, sannan kuma ana iya ganin yadda jami'an sojoji ma suke kai kawo a yankin.
Fitilun kofar fadar na haskaka wajen tarwal.
Gawar Sarauniya na kan hanyar Fadar Buckingham
Tawagar da ke ɗauke da gawar Saruniya Elizabeth wacce ke tafiya a hankali ta kusa isa FAdar Buckingham.
An wuce da gawar ta Westbourne Terrace kusa da Marble Arch, aka bi ta Park Lane da kwanar Hyde Park, zuwa Constitution Hill sannan aka bulla ta Centre Gate Centre Arch na Fadar Buckingham.
The hearse carrying the Queen's coffin is slowly making its way along the A40 as it heads to Buckingham Palace.
Yawanci a kan shafe awa ɗaya a wannan hanyar.
An daure mai fafutuka saboda ta yi shiga irin ta Sarauniyar Thailand
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mai fafutuka
An daure wata mai fafutuka a Thailand a gidan yari tsawon shekara biyu bayan wata kotu ta same ta da laifin cin mutuncin masarautar kasar saboda ta yi shiga irin ta sarauniyar kasar.
Jatuporn 'New' Saeoueng, mai kimanin shekara 25 da haihuwa, ta sanya kaya ruwan hoda a wajen zanga zangar da aka yi a kan batun siyasar kasar a Bangkok a 2020.
Ta dai musanta cewa ta ci mutuncin masarautar kasar, in da ta ce ta sanya kayanta na gargajiya ne kawai.
To amma Thailand ta sanya tsauraran dokokin da suka haramta sukar sarki da kuma iyalan masarautar kasar.
Tun bayan da sarki Maha Vajiralongkorn, ya karbi mulki a 2019, kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar suka ce mahukunta na kara tsaurara dokokin kasar da kuma murkushe duk wani yunkuri na yin bore da zai bukaci garanbawul a masarautar kasar.
Yaran Somaliya 500 na fama da karancin abinci mai gina jiki
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yaro mai fama da karancin abinci mai gina jiki
Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin yaran da ake kyautata tsammanin za su fuskanci karancin abinci mai gina jiki a Somalia a shekarar nan ya karu zuwa rabin miliyan.
Hasashen ya dara wanda aka yi a 2011, a lokacin da tsananin yunwa ta kashe dubban yara a kasar.
Mai magana da yawun Asusun kula da kananan yara ma Majalisar Dinkin Duniya, James Elder, ya kira yanayin a matsayin abin tashin hankali.
Ya ce yara 700 sun mutu a cibiyoyin kula da yaran da ke fama da karancin abinci mai gina jiki a makon da ya wuce a kasar.
Somaliya da sauran kasashen kusurwar Afirka na fama da fari.
Babba da jaka ta kashe mutumin da ya ajiye ta yana kiwonta
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sandan Australiya sun ce wani mutum mai shekara 77 ya rasa ransa bayan da wata babba da jaka ta kai masa hari wadda ya ajiye yana kiwatawa a gidansa.
Wani dan uwan mutumin ne ya same shi da munanan raunuka a jiya Litinin a gidansa da ke Redmond, kilomita 400 da kudancin Perth.
Lokacin da ma'aikatan motar daukar marasa lafiya suka isa gidan mutumin domin agaza masa, babba da jakan ta hana su ba wa mutumin taimakon da ya kamata.
'Yan sanda sun ce an tilasta musu yin harbi kafin kai wa ga mutumin, inda ya rasa ransa lokacin da ake harbe-harben.
Wani mai magana da yawun 'yan sandan, ya fada wa manema labarai cewa suna da yakinin cewa babba da jaka ce ta farwa mutumin a ranar - wadda dabbar daji ce.
Australiya na da babba da jaka sama da miliyan 50 a cikin kasar, da za su kai nauyin kilogram 90 da kuma ke girma na tsawon mita 2.
Sai dai ba kasafai ake samun babba da jaka da ke farwa mutane ba - wanda wannan ne karon farko da aka samu labarin ta kai wa wani hari tun shekarar 1936.
Babba da jaka na da sassan jiki da ke raunata mutane kamar kaifin hakora da kafafu masu karfi, a cewar wani masani kan dabi'un babba da jaka, Graeme Coulson, a wata hira da ya yi da wani gidan rediyon Australiya.
Shugaban Jamus ya nemi ƴan kasuwa su fitar da ƙasar daga ƙarancin makamashi
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya bukaci shugabannin 'yan kasuwa su kara azama domin fitar da kasar daga karancin makamashi da ake fama da shi, sakamakon yakin da ake yi a Ukraine.
Ya shaida wa taron kolin ma'aikata cewa, kokarin da aka yi na bude toshewar da Tarayyar Soviet ta yi wa yammacin Berlin bayan kammala yakin duniya na biyu, ya nuna za a cimma nasara matukar mutane suka hada karfi da karfe da jajircewa domin tabbatar da hakan.
Mr Scholz ya kara da cewa Jamus ta na da gas din da ta adana domin tunkarar lokacin hunturu da ke tafe.
Ya kuma tabbatar da shirin gwamnatinsa ta yi wa cibiyoyin makaman nukiliyar biyu2 da kasar ke da su shirin ko ta kwana, domin samar da lantarki idan bukatar hakan ta taso.
Kalli Hotunan yadda ake wa Sarauniya addu'o'i a Cocin St Anne's Cathedral
Kalli Hotunan yadda ake wa Sarauniya addu'o'i a Cocin St Anne's Cathedral.
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Sarki Charles III yana gayar da dandazon mutanen da suka taru a Cocin St Anne Cathedral a Belfast
Asalin hoton, PA Media
Bayanan hoto, Firaiminista Liz Truss da Taoiseach Micheal Martin kenan a Cocin St Anne Cathedral
Asalin hoton, PA Media
Asalin hoton, PA Media
Labarai da dumi-dumi, Katafaren jirgin ruwa ɗauke ɗimbin mutane ya kife a kogin Ibi a Taraba
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani katafaren jirgin ruwa ya kife a kogin Ibi yayin da
yake dauke da dimbin mutane.
Galibin mutanen masu zuwa kasuwa ne a garin Sarkin Kudu da ke
yankin na Ibi.
Shaidu sun ce kawo yanzu ba a ga da dama daga cikin wadanda
jirgin ya kife da su ba, yayin da aka gano gawawwaki akalla hudu.
Shugaban
karamar hukumar ta Ibi ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin yana mai cewa ana kan
aikin ceto.
Muna fatan kawo maku ci gaban labarin a
shirye-shiryenmu na gaba.
Shugabannin kasashen duniya na taya sabon shugaban Kenya murna
Asalin hoton, Other
Bayan an rantsar da William Ruto a matsayin sabon shugaban Kenya, shugabnnin kasashen dfa ke makwabtaka da kasar sun ci gaba da aika sakonnin bayyana murnarsu da fatan alheri ga sabon shugaban.
Cikin shugabanni na farko da suka aika da sako akwai Samia Suluhu Hassan, shugabar Tanzaniya wadda ta ce Kenya ta yi wa yankin gabashin Afirka wata babbar kyauta domin ta gudanar da babban zabenta cikin lumana.
Shi ma shugaban Burundi Évariste Ndayishimiye ya mika sakon taya 'yan Kenya murna.
Ya ce yana fatan yin aiki tare da sabon shugaba Ruto domin raya yankin Affirka ta Gabas.
Shugaba Yoweri Museveni ma ya aika da nasa sakon, inda ya taya 'yan kasar murnar gudanar da wannan babban zaben cikin aminci da zaman lumana.
William Ruto shi ne shugaban Kenya na biyar, kuma ya gaji mukamin ne daga Uhuru Kenyatta wanda ya yi mulki tsawon wa'adi biyu.
Sarki ya yi alwashin sadaukar da kai domin jama'ar arewacin Ireland
Bayanan hoto, Sarki Charles na III
Sarki Charles na III ya bayyana cewa "na ji dadin yadda muka taru a wannan fadar ta Hillsborough wadda mahaifiya ta sani sosai."
"Cikin shekarun da suka gabata, wadanda ta sadaukar da kan ta domin yi wa jama'a hidima, mahaifiyata ta ga yadda arewacin Ireland ya sami sauye-sauye cikin tarihin wannan yankin."
Ya kara da cewa tun farkon rayuwarta, mahaifiyar tasa ta sha alwashin sadaukar da kai da yin aiki a karkashin inuwar da tsarin mulkin Birtaniya ya samar - alkawarin da yace ta cika "ko shakka babu."
Ya kuma yi nasa alkawarin:
"Game da wannan kyakkyawan alwashin da ke gabana zan fara nawa aikin, karkashin alwashin nema wa jama'ata da dukkan mazauna yankin arewacin Ireland rayuwa mai inganci."
Mutum 26,000 ne suka sami damar ganin gawar Sarauniya a Edinburgh
Asalin hoton, PA Media
A birnin Edinburgh kuwa, gwamnatin kasar Scotland ta wallafa wani sakon Tiwita da ke cewa layukan mutanen da ke son ganin gawar Sarauniya a cocin St Giles sun kare.
Gwamantin ta ce fiye da mutum 26,000 ne suka sami damar karrama Sarauniyar - ciki har da wadanda suka kwana suka jiran a ba su damar shiga cocin.
Wasunsu sun ce an shaida mu su cewa za su rasa damar kafin a dauke ta daga cocin zuwa birnin Landan.
Kotu ta dage karar da gwamantin Najeriya ta kai ASUU kan yajin aiki
Asalin hoton, OTHER
Kotun da ke shiga tsakanin ma'aikata da wadanda suka dauke su aiki ta dage wata kara da gwamnatin Najeriya ta shigar kan yajin aikin da kungiyar malaman ta shafe watanni tana yi.
Alkalin kotun P.I. Hamman ne ya dage sauraren shari'ar zuwa 16 ga watan Satumba bayan da wata kungiya mai fafutukar kare hakkin dan Adam ta mika bukatar yin haka ga alkalin.
Ita ma kungiyar ta shigar da wata kara mai kama da wadda gwamnatin Najeriya ta shigar, lamarin da ya sa alkalin ya dage karar domin a warware matsalar kafin ta zama karfen kafa ga shari'ar.
Sai dai lauyan da ke wakiltar gwmnati Tijjani Gazali (SAN) ya ki amincewa da bukatar a hada kararrakin biyu wuri guda, yana cewa lokacin yin haka bai yi ba.
Amma lauyan ASUU Femi Falana (SAN) ya sanar da manema labarai cewa a sane yake da bukatar da aka gabatar wa kotun na hade kararrakin wuri guda.
Shugaban Najeriya ya kai ziyara Jihar Imo
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jihar Imo domin kaddamar da wasu ayyukan raya kasa.
Ayyukan da shugaban zai kaddamar sun hada da na hanyoyin mota kamar ta Orlu zuwa Okigwe da kuma ta Orlu zuwa Owerri.
Gwamnan Jihar Hope Uzodinma ne ya tarbi shugaban a filin jirgin saman birnin Owerri.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Sarki Charles na III ya isa birnin Belfast
Bayan wata gajeriyar tafiya ta minti 31 daga birnin Edinburgh zuwa arewacin Ireland, Sarki Charles III tare da matarsa Camilla sun sauka a birnin Belfast inad jama'an da suka taru suka tarbe su.
Sarkin ya gaisa da manyan jami'an birnin da kuma sakatare mai kula da arewacin Ireland Chris Heaton-Harris.
An kuma gabatar da shugaban filin jirgin sama na Belfast Mathew Hall da kwasu kananan yara biyu daga wata makarantar firamare da ke yankin.
Yaran biyu - Ella Smith da Lucas Watt masu shekara goma-goma da haihuwa dalibai ne na makarantar firamare ta Forge Integrated, kuma sun ba Sarkin wasu kayaututtuka.
Asalin hoton, The Chocolate Manor
Bayanan hoto, Kamfanin yin cakula The Chocolate Manor ya hada wani cakula na musamman domin karrama sabon Sarki Charles III
An rantsar da William Ruto a matsayin shugaban Kenya
A Kenya, dazun nan an rantsar da Willaim Samuel Ruto a matsayin shugaban kasar Kenya na biyar.
Babban magatakardan ma'aikatar shari'a ne ya rantsar da sabon shugaban.
Abokin adawar Mista Ruto Raila Odinga bai halarci bikin ba, inda ya ce yana da "damuwa mai yawa" game da sakamakon zaben.
Baya ga rantsar da Mista Ruto, an kuma rantsar da mataimakinsa Rigathi Gachagua.
An gudanar da bikin ne a filin wasan birnin Nairobi mai daukar nauyin mutum 60,000.
Shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Kenya na cikin wadanda suka halarci bikin rantsar da sabon shugaban.
Kalli yadda aka mika iko tsakanin tsohon shugaba Kenyatta da sabon shugaba Ruto.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.