Bikin Sallah: Gwamnan Kano ya yi wa mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa afuwa

Wannan shafi ne da zai rika kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran Sassan duniya a wannan rana ta babbar Sallah

Rahoto kai-tsaye

Barka da Sallah

Masu binmu a wannan shafi na BBCHausa barkanmu da wannan rana ta babbar sallah, ku kasance tare da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a wannan rana ta babbar sallah a Najeriya da Saudiyya da ma sauran sassan duniya.

Sunana Abdullahi Bello Diginza, kuma ni zan ja ragamar wannan shafi. Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin bayyana ra'ayoyinku.

Diginza
Bayanan hoto, Barkanmu da Sallah