Bikin Sallah: Gwamnan Kano ya yi wa mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa afuwa

Wannan shafi ne da zai rika kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran Sassan duniya a wannan rana ta babbar Sallah

Rahoto kai-tsaye

  1. Sai da safe

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma na Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  2. Shugaban Ukraine ya sallami wasu jakadun ƙasar

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sallami wasu jakadun kasar daga mukamansu, ciki har da jakadan kasar a Jamus.

    Mista Zelensky bai bayar da dalilin korar ba. A wasu lokuta, jakadan na Ukraine a Berlin, Andrii Melnyk, ya kan fito ya soki shugabannin siyasa na Jamus saboda yadda ake ganin sun gaza bai wa Ukraine goyon bayan soji yadda ya kamata.

    Wasu rahotannin na cewa wata kila a nada shi a matsayin mataimakin ministan harkokin waje, wasu kuma na ganin kamar haka da wuya kasancewa a baya-bayan nan ma'aikatar ta nesanta kanta daga wasu kalamai masu janyo ce-ce-ku-ce da yi wadanda suka shafi shugaban Ukraine a lokacin yakin duniya na biyu.

  3. Bikin Sallah: Gwamnan Kano ya yi wa mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa afuwa

    ..

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa fursunoni 90 afuwa ciki har da mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa.

    Gwamnan ya aiwatar da hakan ne sakamakon bikin Babbar Sallah.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan gyaran hali na Najeriya reshen Jihar Kano Musbahu Lawan K Nassarawa ya saka wa hannu, gwamnan ya biya wa mutum 77 diyyar kuɗin da ake binsu domin fita daga gidan gyaran halin haka kuma akwai mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa a baya da halayansu aka gamsu da su wanda hakan ya sa gwamnan ya yi musu afuwa.

    Haka kuma akwai fursunoni uku da aka yanke wa hukuncin kisa da gwamnan ya yi musu afuwa aka mayar da hukuncinsu ɗaurin rai da rai.

    Gwamna Ganduje ya kuma bai wa fursunonin shanu da raguna da shinkafa domin su ji daɗin Babbar Sallah.

  4. Shugaban Sri Lanka zai sauka daga mulki bayan masu zanga-zanga sun afka har ƙuryar ɗakinsa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban majalisar dokokin Sri Lanka ya bayyana cewa Shugaba Gotabaya Rajapaksa zai sauka daga mulki ranar Laraba 13 ga watan Yuli.

    Wannan ya biyo bayan gagarumar zanga-zanga da aka yi tsawon rana a yau da kuma zaman tattaunawa tsakanin shugaban majalisar da firaministan kasar da kuma shugabanin jam'iyya.

    Bukatar shugaban ya sauka daga mulki dai ita ce gaba-gaba da masu zanga-zangar ke nema tsawon watanni saboda gazawar hukumomi na magance hauhawarar farashi da karancin abinci da man fetur da kuma magani.

    A yau Asabar, masu zanga-zangar suka kwace iko da gidan shugaba Rajapaksa, inda daga bisani suka cinna wa gidan firaministan kasar, Ranil Wickramasinghe wuta.

  5. Buhari ya jinjina wa masu NYSC kan gyara rijiyoyin burtsatse a Daura

    Nigeria President

    Asalin hoton, Nigeria President

    Masu yi wa ƙasa hidima sun kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara a gidansa da ke Daura.

    Sun kai ziyarar ne a daidai lokacin da shugaban ya je mahaifarsa Daura domin hutun Babbar Sallah.

    A wani saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya gode wa masu yi wa ƙasa hidimar bisa ayyukan da suke yi wa ƙasar.

    Shugaban ya gode wa masu yi wa ƙasa hidimar bisa gyara rijiyoyin burtsatse da suka yi a Daura da kuma horas da matasa da kuma wayar da kan jama'a kan batun kula da kiwon lafiya

    Nigeria President

    Asalin hoton, Nigeria President

    Nigeria President

    Asalin hoton, Nigeria President

  6. Me yasa Sri Lanka ke cikin rikicin tattalin arziki?

    ,,.

    Asalin hoton, Getty Images

    Mamayar gidan shugaban kasan Sri Lanka a yau na zuwa ne bayan watanni da masu zanga-zanga suka dauka suna yi a fadin kasar saboda karewar kudaden waje da kasar ke fama da shi.

    Wanda hakan ya sa samun kayayyakin amfanin yau da kullum kamar su fetur da magani da abinci suka yi karanci.

    Hakan ne ya sanya gwamnatin Sri Lanka ta dakatar da sayar da man fetur ga mutanen kasar har zuwa ranar Lahadi, inda ake iya cewa ita ce kasa ta farko da ta yi hakan tun shekarun 1970.

    A makon da ya gabata, hukumomin ƙasar sun bayyana cewa man fetur ɗin ƙasa da mako ɗaya ne kawai ya rage a kasar wanda motocin bas da jiragen kasa da kuma motocin daukar marasa lafiya za su yi amfani da shi.

    An rufe makarantu a fadin kasar, inda aka umarci 'yan kasar da suka kai miliyan 22 yin aiki daga gida.

    Karancin abinci da kuma man fetur sun jawo hauhawarar farashi a kasar, inda yanzu hauhawarar farashin ya tashi zuwa kashi 30.

  7. Labarai da dumi-dumi, Masu zanga-zanga sun cinna wa gidan Firaiministan Sri Lanka wuta

    .

    Asalin hoton, NDTV

    Masu zanga-zanga a Sri Lanka sun cinna wa gidan Firaiminista Ranil Wickremesinghe wuta.

    A ƴan sa'o'in da suka gabata ne dai masu zanga-zangar suka afka gidan shugaban ƙasar da ke Colombo.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Rasha na amfani da makamai domin lalata mana hatsi – Ukraine

    UKraine

    Asalin hoton, KHERSON POLICE/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Ukraine na zargin Rasha da harba makamai kan tarin gonakinta

    'Yan Sanda a kudancin Ukraine sun ce sun shigar ga karar sojojin Rasha, bisa zargin lalata mata tarin hatsi da gangan a yankin Kherson na ƙasar.

    Ukraine ta bayyana cewa dakarun Rashan suna amfani da rokokin domin tayar da wuta a kan tarin gonakin alkama da sauran hatsinta a kowace rana.

    Sun kuma zargi sojojin Rasha da lalata wuraren da take ajiyar hatsin, da injinan aikin gona tare kuma tashar wutar lantarkinta.

    Ukraine dai na zargin Rasha da amfani da makamai wajen lalata kayan abinci.

  9. Falalar Babbar Sallah ga mabiya Addinin Musulunci

    Latsa lasifikar da ke sama domin sauraren wannan shirin

    A yayin da al'ummar Musulmi ke bikin Babbar Sallah ta bana, filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon ya mayar da hankali ne kan falalar da ke tattare da ranar da kuma muhimman abubuwa da ya kamata Musulmi su yi.

    Abokin aikinmu, Yusuf Tijjani ya tattauna da Imam Tukur Adam Al-Mannar, Limamin Babban Masallacin Juma'a na Al Mannar da ke Kaduna kuma ya fara bayani ne kan fai'doji da ke kunshe cikin ranar Babbar Sallah.

  10. Mahajjata sun kammala manyan rukunan Aikin Hajji

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kusan mutum miliyan daya ne dai ke gudanar da aikin hajjin bana

    A yau Asabar ne Mahajjata a Saudiyya ke kammala manyan rukunan Aikin Hajji Bayan da suka gudanar da Dawafi tare da Safa da Marwa, a daidai lokacin da sauran al'ummar musulman duniya ke shagulgulan bukukuwan Babbar Sallah.

    Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa tun da asubahin yau ne Alhazan suka fara fita daga Muzdalifa domin tafiya Mina wajen jifan shaidan, bayan da a jiya suka gudanar da tsayuwar Arfa.

    Kusan mutum miliyan daya ne dai ke gudanar da Aikin Hajjin bana

  11. Masu zanga-zanga sun kutsa har cikin ɗakin kwana na shugaban Sri Lanka

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dubban masu zanga-zanga a Sri lanka sun mamaye gidan shugaban kasar a Colombo, inda suke bukatar ya sauka daga shugabancin kasar.

    Dandazon masu zanga-zangar da ke daga tutoci sun yi dirar mikiya zuwa gidan shugaban kasar, tare da wuce shingen jami'an tsaro, kan yadda shugaban Gotabaya Rajapaksa ke tafiyar da al'amura a kasar d ake cikin matsin tattalin arziki na shekaru goma.

    Hotuna a kafofin sada zumunta sun nuna masu zanga-zangar sun kutsa har cikin ɗakin kwanan shugaban kasar inda suka rinƙa ɗaukar hotuna a kan gadonsa da zama kan kujeru.

    Da dama daga cikinsu kuma sun afka cikin wurin wanka na alfarma wato swimming pool inda suka yi ta wanka a ciki.

    An shafe watanni a ƙasar dai ana zanga-zanga inda za iya cewa kuɗaɗen waje sun ƙare a ƙasar wanda hakan ya sa ba a iya sawo kayayyakin amfanin yau da kullum kamar su fetur da magani da abinci.

    Makarantu ma sun shafe kusan makonni uku a rufe saboda wahalar man fetur.

  12. Akwai yiwuwar masu barbaɗa gishiri a abinci su mutu da wuri - Bincike

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon bincike ya nuna cewa mutanen da ke yawan barbaɗa gishiri a cikin abincinsu na fuskanatar barazanar mutuwa da wuri.

    Binciken, wanda aka wallafa a mujjalar European Heart da kuma ya kunshi mutane kusan rabin miliyan, ya gano cewa mutanen da ke kara gishiri a abincinsu, suna kara wa kansu kashi 28 na yiwuwar mutuwa da wuri.

    Har ila yau, binciken ya bayyana cewa maza da suka kai shekara 50, na rage wa kansu lokacin rayuwa a duniya ta hanyar kara gishiri a abincin.

    Farfesa Lu Qi, da ya jagoranci binciken a Amurka, ya ce ko da rage yawan shan gishiri ma, na iya haifar da fa'ida mai yawa ga lafiyar jikin mutum.

  13. Yadda ministan sadarwa na Najeriya Pantami ke gyara ragon layyarsa

    Ministan sadarwa da fasahar zamani na Najeriya Isa Ali Pantami yayin da yake gyara ragon layyarsa a yau Asabar.

    Professor Isa Ali Pantami

    Asalin hoton, Professor Isa Ali Pantami

    Professor Isa Ali Pantami

    Asalin hoton, Professor Isa Ali Pantami

    Professor Isa Ali Pantami

    Asalin hoton, Professor Isa Ali Pantami

  14. Shugaban Rwanda na neman wa'adin mulki na hudu

    Shugaban Rwanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Kagame dai na shugabantar kasar tun shekarar 2000

    Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya ce zai tsaya takara a zaben shugaban kasar da ke tafe a 2024.

    A wata tattaunawa da ya yi da gidan Talabijin na French TV channel, shugaban mai shekarar 64, ya ce yana duba yiyuwar kasance ''a kan karagar mulki nan da shekara 20 masu zuwa''

    A shekarar 2015 ne dai Kagame ya sauya kundin tsarin mulkin kasar abinda ya bashi damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2024

    A zaben shugaban kasar da ya gabata , alkaluman hukumar zabe sun nuna cewa ya lashe zaben da kashi 99 cikin dari na kuri'un da aka kada, sakamakon da masu sanya ido na kasashen wajen suka yi watsi da shi.

  15. Hotunan yadda Alhazai ke jifan shaidan

    Alhazan bana

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Daruruwan mahajjata suna cigaba da tururuwa zuwa jifan shaidan
    Alhazai
    Bayanan hoto, A jiya ne dai alhazan suka gudanar da tsayuwar Arfa
    Alhazai
    Bayanan hoto, Tun da sanyin safe ne suka fara fita
    Alhazan bana

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A jiya ne dai alhazan suka gudanar da tsayuwar Arfa
    Alhazai
    Bayanan hoto, kimanin mutum milyan guda ne dai ke gudanar da aikin hajjin bana
    Alhazan bana

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kowane Alhaji zai yi amfani da tsakuwa guda bakwai wajen wannan jifa
  16. Sarkin Saudiyya ya gaishe da alhazan bana

    Sarkin Salman

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Sarkin Salman ya jinjina wa kokarin da masautarsa ta yi wajen yaki da cutar Korona

    Babba mai kula da masallatai biyu mafiya daraja, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdul'aziz ya mika sakon gaisuwarsa zuwa ga al'umar kasar da ma mahajjatan da ke gudanar da aikin hajji da kuma sauran musulman duniya baki-daya.

    Jaridar Saudi Gazzet ta ruwaito cewa sarkin ya yi wa musulman duniya addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hakali.

    Ya kuma kara jinjina wa masarautarsa game da hobbasan da ta yi wajen yakar cutar Korona, wanda hakan ne a cewarsa ya sa aka samu karin mahajjata daga kasashen waje.

    A halin yanzu dai kimanin mahajjata miliyan daya ne ke gudanar da aikin hajji.

  17. Hotunan yadda aka gudanar da sallar idi a masallacin Shagari Kwatas da ke birnin Kano

    Mutane
    Bayanan hoto, A yau ne dai al'umar musulmi a fadin duniya ke gudanar da sallar idi
    Yara
    Bayanan hoto, yara ma ba a bar su a baya ba wajen zuwa sallar idin
    Mutane
    Bayanan hoto, Akan dai yi ziyarce-ziyarce domin gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki a ranar salla
    Mutane
    Bayanan hoto, Mutane na sauraron huduba bayan kammala sallar idi
    Mutane
    Bayanan hoto, An dai fuskanci tsadar ragunan layya a bana
    Mutane
    Bayanan hoto, Mutane kan gaisa da juna bayan kammala sallar idi, domin nuna murna da farin ciki
  18. Buhari ya nemi 'yan Najeriya su zama masu kishin kasa da rike addini

    Shugaba  Buhari

    Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

    Bayanan hoto, Shugaban ya kara da cewa ''mutane a yanzu basa soron Allah

    Shugaba Muhammadu Buhari ya kira ga 'yan Najeriya da su sanya bukatar kasa a farko sannan su rike addini wajen samun hadin-kai tsakanin 'yan kasar.

    A wata sanarwar sakon barka da sallah ga al'ummar musulmi a Najeriya da maitaimaka wa shugaban na musamman kan harkokin yada labaru, Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce 'in har da muna amfani da koyarwar addini, da mun sami mafita kan yawancin matsalolin da muke fuskanta a yanzu.''

    A cewar Shugaban ya kamata addini ya zamanto a matsayin abin a za a yi amfani da shi wajen yin abu mai kyau ga kasar nan.

    Ya kara da cewa satar kudin kasa da wasu jami'an gwamnati ke yi, wata manuniya ce ta yadda mutane ka barin koyarwar addini.

    Shugaban ya kara da cewa ''mutane a yanzu basa soron Allah, inda suke sanya abubuwa su zamanto masu wahala ga wasu''.

    Haka kuma ya ce ''shugabanni sukan watsar da shan rantsuwa da suka yi yayin shiga ofis ta hanyar karkatar da kudaden da aka tanada domin walwalar 'yan kasa zuwa aljihunansu.

    A kan matalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta, shugaban ya sha alwashin cewa ba zai gajiya ba har sai ya samar wa 'yan Najeriya mafita, inda yace yana sane da irin wahalhalun da suke ciki, kuma zai yi maganin hakan nan ba da jimawa ba.

    A karshe Shugaban ya taya musulman Najeriya da ma na duniya baki daya murnar bikin sallar layya.

  19. Yan sanda sun tarwatsa dubban masu zanga-zanga a Sri Lanka

    Mutane na zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka hallara a kusa da gidan gwamnatin shugaba Gotabaya Rajapaksa

    'Yan sanda a Colombo babban birnin Sri Lanka, sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa mutanen da suka taru don gudanar da babbar zanga zanga akan matsalar da tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

    Dubban mutane ne suka hallara a kusa da gidan gwamnatin shugaba Gotabaya Rajapaksa, a wani bangare na gudanar da zanga zangar da kungiyoyi da dama suka shirya a kasar.

    Dubban sojoji da 'yan sanda aka tura birnin don kare afkuwar wata tarzoma.

    A jiya Jumma'a ne aka janye dokar takaita zirga zirgar dare da aka sanya a kasar bayan sukar da kungiyoyin fararen hula da jam'iyyun adawa suka rinka yi akai.

    Sri Lanka dai na fuskantar karancin kudaden ajiya na kasashen waje da kuma fama da shigo da abinci da man fetir da kuma magunguna.

  20. Za a kai karar mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

    Ellon Musk

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ellon Musk ne mutumin da ya fi kowa arziki a duniya

    Shugaban kamfanin sadarwa na tiwita ya ce zai shigar da Elon Musk kara a kan kammala yarjejeniyar siyan kamfanin na Tiwita ta kudi har dala biliyan 44.

    A cikin wani sakon tiwita da ya wallafa, Bret Taylor, ya ce tiwita a nata bangaren a shirye take ta kammala cinikin kamar yadda aka tsara cikin yarjejeniyar da aka kulla da attajirin.

    Tun da farko Mr Musk ya ce zai janye daga yarjejeniyar. Lauyoyin Mr Musk na zargin kamfanin tiwita da kin basu wasu bayanai a kan wasu shafuka masu wallafa labarai barkatai.